L. FIR 18

An Haramta yin Lalata

1 Ubangiji kuma ya ce wa Musa

2 ya faɗa wa mutanen Isra’ila cewa, “Ni ne Ubangiji Allahnku.

3 Kada ku yi kamar yadda suke yi a ƙasar Kan’ana inda nake kai ku. Kada ku kiyaye dokokinsu.

4 Amma ku bi ka’idodina, ku yi tafiya a cikinsu, gama ni ne Ubangiji Allahnku.

5 Domin haka sai ku kiyaye dokokina da ka’idodina waɗanda ta wurin kiyaye su mutum zai rayu. Ni ne Ubangiji.”

6 Ubangiji ya ba da waɗannan ka’idodi kuma. Kada kowane mutum ya kusaci ‘yar’uwarsa don ya kwana da ita. Ya ce, “Ni ne Ubangiji.”

7 Kada ya ƙasƙantar da mahaifinsa, wato, kada ya kwana da mahaifiyarsa, kada ya ƙasƙantar da mahaifiyarsa.

8 Kada ya kwana da matar mahaifinsa, gama ita matar mahaifinsa ce.

9 Kada ya kwana da ‘yar’uwarsa, ‘yar mahaifinsa, ko ‘yar mahaifiyarsa, ko a gida ɗaya aka haife ta da shi, ko a wani gida dabam.

10 Kada ya kwana da jikanyarsa gama zai zama ƙasƙanci a gare shi.

11 Kada ya kwana da ‘yar matar mahaifinsa, wadda mahaifinsa ya haifa, tun da yake ita ‘yar’uwarsa ce.

12 Kada ya kwana da bābarsa gama ‘yar’uwar mahaifinsa ce.

13 Kada ya kwana da innarsa, gama ita ‘yar’uwar mahaifiyarsa ce.

14 Kada ya kwana da matar ɗan’uwan mahaifinsa, gama ita ma bābarsa ce.

15 Kada ya kwana da matar ɗansa, gama ita surukarsa ce.

16 Kada ya kwana da matar ɗan’uwansa, gama ita matar ɗan’uwansa ce.

17 In ya kwana da mace, kada kuma ya kwana da ‘yarta, ko jikanyarta, wannan duk haramun ne, gama su danginsa ne na kusa.

18 Muddin matarsa tana da rai, ba zai auro ƙanwarta ta zama kishiyarta ba.

19 Kada ya kwana da mace a lokacin hailarta, gama ba ta da tsarki.

20 Kada ya kwana da matar maƙwabcinsa don kada ya ƙazantar da kansa.

21 Kada ya ba da ɗaya daga cikin ‘ya’yansa don a miƙa wa Molek, gama yin haka zai ƙasƙantar da sunan Allah. Shi Ubangiji ne.

22 Kada ya yi luɗu, gama Allah yana ƙin wannan.

23 Kada wani ko wata su kwana da dabba don kada su wofintar da kansu.

24 Kada su ƙazantar da kansu da irin waɗannan abubuwa, gama da irin waɗannan abubuwa ne al’umman da Ubangiji yake kora a gabansu suka ƙazantar da kansu.

25 Har ƙasar ma ta ƙazantu, don haka Ubangiji ya hukunta muguntarta, ƙasar kuwa ta amayar da mazaunanta.

26 Amma su sai su kiyaye dokokin Ubangiji da ka’idodinsa. Kada su aikata ko ɗaya daga cikin waɗannan abubuwa na banƙyama, ko haifaffe na gida, ko baƙon da yake baƙunta a cikinsu.

27 Gama mazaunan ƙasar da suka riga su, sun aikata dukan abubuwa masu banƙyaman nan, don haka ƙasar ta ƙazantu.

28 Kada kuma ƙasar ta amayar da su idan sun ƙazantar da ita, kamar yadda ta amayar da al’ummar da ta riga su zama a cikinta.

29 Duk wanda ya aikata abu ɗaya daga cikin waɗannan abubuwa masu banƙyaman nan za a raba shi da jama’a.

30 Ubangiji kuma ya ce, “Don haka sai ku kiyaye umarnina, kada ku kiyaye dokoki na banƙyama waɗanda aka kiyaye kafin ku zo, kada ku ƙazantu da su. Ni ne Ubangiji Allahnku.”