Sandan Haruna
1 Ubangiji ya yi magana da Musa ya ce,
2 “Ka faɗa wa Isra’ilawa su ba ka sanduna, sanda guda daga kowane shugaban gidan kakanninsu, sanduna goma sha biyu ke nan. Ka rubuta sunan kowane mutum a sandansa.
3 Ka rubuta sunan Haruna a kan sandan Lawi, gama akwai sanda guda domin kowane gidan kakanninsu.
4 Sai ka ajiye su a alfarwa ta sujada a gaban akwatin alkawari, inda nakan sadu da kai.
5 Mutumin da sandansa ya yi toho, shi ne na zaɓa, da haka zan sa gunagunin da Isra’ilawa suke yi a kaina ya ƙare.”
6 Musa kuwa ya yi magana da Isra’ilawa. Sai dukan shugabanninsu suka ba shi sanda ɗaya ɗaya, sanda ɗaya daga kowane shugaba bisa ga gidajen kakanninsu, sanduna goma sha biyu ke nan. Sandan Haruna yana cikin sandunan.
7 Sai Musa ya ajiye sandunan a gaban Ubangiji cikin alfarwa ta sujada.
8 Kashegari Musa ya shiga alfarwar, sai ga shi, sandan Haruna na gidan Lawiyawa ya huda, ya yi toho, ya yi furanni, ya kuma yi ‘ya’yan almon nunannu, wato wani irin itace ne mai kama da na yazawa.
9 Musa kuwa ya fito wa Isra’ilawa da dukan sandunan da aka ajiye a gaban Ubangiji. Suka duba, kowanne ya ɗauki sandansa.
10 Ubangiji ya ce wa Musa, “Mayar da sandan Haruna a akwatin alkawari, alama ce ga masu tawaye ta cewa za su mutu idan ba su daina gunaguninsu ba.”
11 Haka kuwa Musa ya yi yadda Ubangiji ya umarce shi.
12 Isra’ilawa suka ce wa Musa, “Ba shakka, mun hallaka. Mun lalace, dukanmu mun lalace.
13 Duk wanda ya kusaci alfarwa ta sujada ta Ubangiji, zai mutu. Ashe, dukanmu za mu mutu ke nan!”