L. KID 18

Ayyukan Lawiyawa da Firistoci

1 Sai Ubangiji ya ce wa Haruna, “Kai da ‘ya’yanka, da gidan mahaifinka za ku ɗauki hakkin abin da ya shafi alfarwa ta sujada. Kai da ‘ya’yanka kuma za ku ɗauki hakkin aikinku wanda ya shafi firistoci.

2 Ka kawo ‘yan’uwanka tare da kai, wato kabilar Lawi, kakanka, don su yi muku aiki sa’ad da kai da ‘ya’yanka kuke gaban alfarwa ta sujada.

3 Za su taimake ku, su kuma yi dukan ayyukan alfarwa. Amma fa, ba za su kusaci kayayyakin Wuri Mai Tsarki, ko bagade ba, don kada su, har da ku, ku mutu.

4 Za su haɗa kai da ku su lura da alfarwa ta sujada da dukan aikace-aikace na cikin alfarwar. Kada wani dabam ya kusace ku.

5 Ku lura da ayyukan Wuri Mai Tsarki da na bagade don kada hasala ta sāke fāɗa wa Isra’ilawa.

6 Ga shi, ni na ɗauki ‘yan’uwanku, Lawiyawa, daga cikin mutanen Isra’ila. Kyauta suke a gare ku, waɗanda aka bayar ga Ubangiji don su lura da alfarwa ta sujada.

7 Da kai, da ‘ya’yanka za ku yi aikin firist da duk abin da ya shafi bagade da aiki na bayan labule. Ku ne za ku yi wannan aiki. Na ba ku aikin firist ya zama naku. Duk wani dabam wanda ya zo kuwa, za a kashe shi.”

Rabon Firistoci

8 Ubangiji ya kuma ce wa Haruna, “Na ba ka aikin lura da hadayuna na ɗagawa, wato sadakokin Isra’ilawa, na ba ka su su zama rabonka da na ‘ya’yanka har abada.

9 Abin da ya ragu daga cikin hadaya mafi tsarki da ake miƙa mini zai zama rabonka da na ‘ya’yanka, wato daga kowace hadaya, da hadaya ta gari, da hadaya don zunubi, da hadaya don laifi.

10 A wuri mai tsarki za ku ci shi, kowane namiji ya iya ci. Abu mai tsarki ne a gare ka.

11 “Har yanzu kuma duk sadakokin da Isra’ilawa suke bayarwa don hadaya ta ɗagawa da ta kaɗawa, na ba ka, kai da ‘ya’yanka mata da maza, a kowane lokaci. Duk wanda yake da tsarki a gidanka zai iya ci.

12 “Duk mai mafi kyau, da ruwan inabi mafi kyau duka, da hatsi mafi kyau duka na nunan fari, waɗanda suke bayarwa ga Ubangiji, na ba ku.

13 Nunan fari na dukan amfanin gonarsu wanda suke kawowa ga Ubangiji, zai zama naka. Duk wanda yake da tsarki a gidanka zai iya cinsa.

14 “Iyakar abin da aka keɓe wa Ubangiji a Isra’ila zai zama naka.

15 “Dukan haihuwar fari, ko ta mutum ko ta dabba da sukan bayar ga Ubangiji zai zama naka. Amma ka fanshi kowace haihuwar fari ta mutum, ko ta dabbar da take haram.

16 Sai ka fanshe su suna ‘yan wata ɗaya a bakin shekel biyar biyar, bisa ga ma’aunin kuɗin da ake aiki da shi.

17 Haihuwar fari ta saniya, ko ta tunkiya, ko ta akuya, ba za ka fanshe su ba, gama su halal ne. Sai kayayyafa jininsu a kan bagade, kitsensu kuma ka ƙone a kan bagaden ƙona hadayu, zai zama turare mai ƙanshi, mai daɗi ga Ubangiji.

18 Naman kuwa zai zama naka, duk da ƙirji na kaɗawa da cinyar dama da aka miƙa su hadaya ta kaɗawa.

19 “Duk hadayu na ɗagawa na tsarkakakkun abubuwan da Isra’ilawa suka miƙa wa Ubangiji, na ba ka, da kai da ‘ya’yanka mata da maza a kowane lokaci. Wannan alkawarin gishiri ne na Ubangiji dominka da zuriyarka.”

20 Ubangiji kuma ya ce wa Haruna, “Ba za ka gāji kome a ƙasar Isra’ilawa ba, ba ka da wani rabo a cikinta. Ni ne rabonka da gādonka a cikin Isra’ilawa.”

Rabon Lawiyawa

21 Ubangiji ya ce, “Na ba Lawiyawa kowace zaka ta Isra’ilawa gādo saboda aikinsu da suke ya a alfarwa ta sujada.

22 Nan gaba kada Isra’ilawa su zo kusa da alfarwa ta sujada don kada su yi zunubi, su mutu.

23 Gama Lawiyawa ne kaɗai za su yi aikin alfarwa ta sujada, wannan alhakinsu ne. Wajibi ne kuma ga zuriyarsu a kowane lokaci. Lawiyawa ba su da gādo tare da Isra’ilawa.

24 Gama ni Ubangiji na ba su zaka da Isra’ilawa suke kawo mini ta hadaya ta ɗagawa ta zama gādonsu. Saboda haka ne, na ce ba su da gādo tare da Isra’ilawa.”

Zaka

25 Ubangiji ya ce wa Musa,

26 “Har yanzu ka faɗa wa Lawiyawa, cewa sa’ad da suka karɓi zaka daga Isra’ilawa wadda na ba su gādo, sai su fitar da zaka daga cikin zakar, su miƙa wa Ubangiji hadaya ta ɗagawa.

27 Za a lasafta hadayarku ta ɗagawa kamar hatsinku ne da kuka sussuka a masussuka, da kuma kamar cikakken amfanin ruwan inabin da kuka samu a wurin matsewar inabinku.

28 Haka za ku miƙa hadaya ta ɗagawa ga Ubangiji daga cikin dukan zakar da kuke karɓa daga wurin Isra’ilawa. Daga ciki za ku ba da hadaya ta ɗagawa ga Ubangiji ta hannun Haruna, firist.

29 Daga dukan kyautar da ake kawo muku, za ku ba Ubangiji hadaya ta ɗagawa daga mafi kyau da kuke samu.

30 Domin haka kuwa sai ka ce musu, ‘Sa’ad da kuka ɗaga mafi kyau daga cikinta duka, sai ragowar ta zama ta Lawiyawa kamar abin da ya fito daga masussuka, da wurin matsewar inabinsu.

31 Za ku iya cinta ko’ina da kuka ga dama, ku da iyalan gidajenku, gama ladanku ke nan saboda aikin da kuke yi a alfarwa ta sujada.

32 Ba kuwa za ta zama muku sanadin zunubi ba, in dai har kuka ɗaga mafi kyau duka. Ba za ku ɓata tsarkakakkun abubuwa na Isra’ilawa ba, don kada ku mutu.’ ”