Tsarkakewar Marasa Tsarki
1 Ubangiji ya yi magana da Musa da Haruna, ya ce,
2 “Wannan ita ce ka’ida wadda Ubangiji ya umarta. Ka faɗa wa Isra’ilawa su kawo maka jar karsana, marar lahani, wadda ba ta da wani aibi, wadda ba a taɓa aza mata karkiya ba.
3 Sai ka ba Ele’azara firist ita, sa’an nan a kai ta bayan sansani, a yanka ta gabansa.
4 Ele’azara, firist, kuwa zai ɗibi jininta da yatsansa, ya yayyafa sau bakwai a wajen alfarwar ta sujada.
5 Sai a ƙone karsanar a idonsa, za a ƙone fatarta, da naman, da jinin, tare da tarosonta.
6 Firist zai ɗauki itacen al’ul, da ɗaɗɗoya, da mulufi, ya jefa a wutar da take ƙone karsanar.
7 Sai firist ɗin ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, sa’an nan ya shiga zangon. Firist ɗin zai ƙazantu har zuwa maraice.
8 Shi kuma wanda ya ƙone karsanar, sai ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, shi ma zai ƙazantu har zuwa maraice.
9 Mutumin da yake da tsarki shi zai tara tokar karsanar, ya ajiye a wuri mai tsabta a bayan zangon. Za a adana tokar domin jama’ar Isra’ila, za a riƙa zubawa a ruwa don tsarkakewar zunubi.
10 Shi kuma wanda ya tara tokar karsanar, sai ya wanke tufafinsa zai ƙazantu har maraice. Wannan ka’ida ce ta har abada ga Isra’ilawa da baƙin da yake zama tare da su.”
Taɓa Gawa
11 “Duk wanda ya taɓa gawa zai ƙazantu har kwana bakwai.
12 A rana ta uku da ta bakwai zai tsarkake kansa da ruwa, zai kuwa tsarkaka, amma in a rana ta uku da ta bakwai bai tsarkake kansa ba, to, ba zai tsarkaka ba.
13 Duk wanda ya taɓa gawa, bai kuwa tsarkake kansa ba, ya ƙazantar da alfarwa ta sujada ta Ubangiji, ba za a lasafta shi cikin mutanen Allah ba, domin ba a yayyafa masa ruwan tsarkakewa ba.
14 “Wannan ita ce ka’ida a kan wanda ya rasu a alfarwa, duk wanda ya shiga alfarwar, da duk wanda yake cikin alfarwar zai ƙazantu har kwana bakwai.
15 Kowace buɗaɗɗiyarsa kuma wadda ba a rufe ba, za ta ƙazantu.
16 Wanda duk yake cikin saura ya taɓa wanda aka kashe da tokobi, ko gawa, ko ƙashin mutum, ko kabari zai ƙazantu har kwana bakwai.
17 “Don a tsarkake ƙazantar, sai a ɗiba daga cikin tokar hadaya don zunubi a cikinsa, sa’an nan a zuba ruwa mai gudu.
18 Tsarkakakken mutum zai ɗauki ɗaɗɗoya ya tsoma a ruwan, ya yayyafa wa alfarwar, da bisa kan dukan kayayyakin da suke ciki, da a kan mutanen da suke a wurin, da kan wanda ya taɓa ƙashin, ko ya taɓa wanda aka kashe, ko ya taɓa gawa, ko kabari.
19 A kan rana ta uku da ta bakwai kuma, wanda yake da tsarki zai yayyafa wa marar tsarkin ruwa, ya tsarkake shi. Sai mutumin ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, da maraice kuwa zai tsarkaka.
20 “Amma mutumin da ba shi da tsarki, bai kuwa tsarkake kansa ba, ba za a lasafta shi cikin jama’ar Allah ba, tun da yake ya ƙazantar da alfarwa ta sujada ta Ubangiji, gama ba a yayyafa masa ruwan da akan yayyafa wa marasa tsarki ba.
21 Wannan zai zama musu ka’ida har abada. Wanda ya yayyafa ruwan tsarkakewa, sai ya wanke tufafinsa, wanda kuma ya taɓa ruwan tsarkakewa zai zama marar tsarki har maraice.
22 Duk abin da mutumin da ba shi da tsarki ya taɓa zai ƙazantu, duk wanda kuma ya taɓa abin da marar tsarkin ya taɓa zai ƙazantu har maraice.”