Ruwa daga cikin Dutse
1 Sai dukan taron jama’ar Isra’ilawa suka zo jejin Zin a watan fari, suka sauka a Kadesh. A nan ne Maryamu ta rasu, a nan kuma aka binne ta.
2 Da jama’a suka rasa ruwa, sai suka taru suka tayar wa Musa da Haruna.
3 Suka ce wa Musa, “Da ma mun mutu kamar yadda ‘yan’uwanmu suka mutu a gaban Ubangiji.
4 Don me ka fito da taron jama’ar Ubangiji zuwa cikin wannan jeji don mu mutu a nan, mu da dabbobinmu?
5 Don me kuma ka sa muka fito daga masar, ka kawo mu a wannan mugun wuri inda babu hatsi, ko ɓaure, ko inabi, ko rumman, ko ruwan da za a sha ma?”
6 Sai Musa da Haruna suka bar taron jama’a, suka tafi ƙofar alfarwa ta sujada, suka fāɗi rubda ciki. Ɗaukakar Ubangiji kuwa ta bayyana a gare su.
7 Ubangiji ya ce wa Musa,
8 “Ka ɗauki sandanka, kai da Haruna, ɗan’uwanka, ku tara jama’a, ku yi magana da dutsen a gabansu ya ba da ruwan da yake cikinsa. Za ka sa ruwa ya ɓuɓɓugo musu daga dutsen. Ta haka za ka ba taron jama’a da garkunansu ruwan sha.”
9 Musa kuwa ya ɗauki sanda daga gaban Ubangiji kamar yadda ya umarce shi.
10 Sai Musa da Haruna suka sa jama’a su taru a gaban dutsen, sa’an nan Musa ya ce musu, “Ku kasa kunne, ku ‘yan tawaye, za mu fito muku da ruwa daga cikin dutsen nan?”
11 Musa kuwa ya ɗaga hannu, ya bugi dutsen sau biyu da sandansa, sai ruwa mai yawa ya yi ta kwararowa. Taron jama’a tare da garkunansu suka sha.
12 Ubangiji kuwa ya ce wa Musa da Haruna, “Tun da yake ba ku gaskata ni ba, ba ku kuwa ɗaukaka ni a idon Isra’ilawa ba, to, ba za ku kai taron jama’ar nan a ƙasar da na ba su ba.”
13 Wannan ya faru ne a Meriba inda mutanen Isra’ila suka yi wa Ubangiji gunaguni, inda shi kuma ya nuna musu shi mai tsarki ne.
Sarkin Edom ya Hana Isra’ilawa Wucewa
14 Sai Musa ya aika manzanni daga Kadesh zuwa wurin Sarkin Edom, su ce masa, “In ji ɗan’uwanka, Isra’ila, ka dai san dukan wahalar da ta same mu,
15 yadda kakanninmu suka gangara zuwa Masar, suka zauna a can da daɗewa, da yadda Masarawa suka wahalshe mu, mu da kakanninmu.
16 Sa’ad da muka yi kuka ga Ubangiji, Ubangiji kuwa ya ji kukanmu, ya aiko mala’ikansa, ya fisshe mu daga Masar. Ga mu nan a Kadesh, garin da yake kan iyakar ƙasarka.
17 Ka yarda mana mu ratsa ƙasarka, ba za mu bi ta cikin gona, ko gonar inabi ba, ba kuwa za mu sha ruwan rijiyarka ba. Mu dai za mu bi gwadaben sarki, ba za mu kauce dama ko hagu ba, har mu wuce ƙasarka.”
18 Amma Edomawa suka ce masa, “Ba za ku ratsa ta ƙasarmu ba! Idan kuwa kun ce za ku gwada, za mu fita mu ci ku da yaƙi.”
19 Amma mutanen Isra’ila suka amsa musu suka ce, “Ai, za mu bi gwadabe ne kawai, idan kuwa mu da dabbobinmu mun sha ruwanku, sai mu biya, mu dai, a yardar mana mu wuce kawai.”
20 Amma Edomawa suka sāke cewa, “Ba mu yarda ba.” Sai suka fito da runduna mai yawa su yi yaƙi da su.
21 Da haka Edomawa suka hana Isra’ilawa ratsa ƙasarsu. Sai Isra’ilawa suka kauce musu.
Haruna ya Rasu
22-23 Sai taron jama’ar Isra’ila suka kama tafiya daga Kadesh, suka je Dutsen Hor, a kan iyakar ƙasar Edom. Ubangiji kuwa ya ce wa Musa da Haruna a can,
24 “Haruna ba zai shiga ƙasar da na alkawarta zan ba Isra’ila ba, zai mutu, gama ku biyun nan kuka tayar wa umarnina a Meriba.
25 Ka kawo Haruna da ɗansa, Ele’azara, bisa Dutsen Hor.
26 Ka tuɓe wa Haruna rigunansa na firist, ka sa wa ɗansa, Ele’azara. Haruna zai mutu can.”
27 Musa kuwa ya yi yadda Ubangiji ya umarta. Suka hau bisa Dutsen Hor a idon dukan taron jama’a.
28 Sai Musa ya tuɓe wa Haruna rigunansa na firist ya sa wa Ele’azara ɗan Haruna. Haruna kuwa ya rasu a kan dutsen. Sa’an nan Musa da Ele’azara suka sauko daga kan dutsen.
29 Sa’ad da dukan jama’a suka ga Haruna ya rasu, sai duka suka yi makoki dominsa har kwana talatin.