1 Da Bal’amu ya gane Ubangiji yana jin daɗin sa wa Isra’ilawa albarka bai tafi neman shawara kamar dā ba, sai ya fuskanci jeji,
2 ya ta da idanunsa ya ga Isra’ilawa sun yi zango kabila kabila. Sai Ruhun Allah kuwa ya sauko masa.
3 Sai ya yi annabcinsa, ya ce.
“Faɗar Bal’amu ɗan Beyor,
Faɗar mutumin da idonsa take a buɗe.
4 Faɗar wanda yake jin faɗar Allah,
Shi wanda yake ganin wahayin Maɗaukaki,
Yana durƙushe, amma idanunsa a buɗe suke.
5 Alfarwan Isra’ilawa suna da kyan gani!
6 Kamar dogon jerin itatuwan dabino,
Kamar gonaki a gefen kogi,
Kamar itatuwan aloyes da Ubangiji ya dasa,
Kamar kuma itatuwan al’ul a gefen ruwaye.
7 Sojojin Isra’ilawa za su sa al’ummai rawar jiki;
Za su yi mulkin jama’a mai yawa
Sarkinsu zai fi Agag girma,
Za a ɗaukaka mulkinsa.
8 Allah ne ya fisshe su daga Masar,
Kamar kutunkun ɓauna yake a gare su,
Yakubu zai cinye maƙiyansa,
Zai kakkarya ƙasusuwansu, ya mummurɗe kibansu.
9 Al’ummar tana kama da ƙaƙƙarfan zaki
Sa’ad da yake barci, ba wanda zai yi ƙarfin hali ya tashe shi.
Duk wanda ya sa muku albarka zai sami albarka,
Duk wanda ya sa muku la’ana zai sami la’ana.”
Annabcin Bal’amu
10 Sai Balak ya husata da Bal’amu, ya tafa hannunsa ya ce wa Bal’amu, “Na kirawo ka don ka la’anta maƙiyana, amma ga shi, har sau uku kana sa musu albarka.
11 Yanzu sai ka tafi abinka. Hakika,na ce zan ɗaukaka ka, amma ga shi, Ubangiji ya hana maka ɗaukakar.”
12 Sai Bal’amu ya ce wa Balak, “Ashe, ban faɗa wa manzanninka waɗanda ka aiko gare ni ba?
13 Na ce, ‘Ko da Balak zai ba ni gidansa cike da azurfa da zinariya, ba zan iya in zarce maganar Ubangiji ba, in aikata nagarta ko mugunta bisa ga nufin kaina.’ Abin da Ubangiji ya faɗa shi ne zan faɗa.”
14 Bal’amu ya ce wa Balak, “Yanzu fa, zan koma wurin mutanena. Ka zo in sanar maka da abinda mutanen nan za su yi wa mutanenka nan gaba.”
15 Sai ya hurta jawabinsa, ya ce,
“Faɗar Bal’amu ɗan Beyor,
Faɗar mutumin da idonsa take buɗe,
16 Faɗar wanda yake jin faɗar Allah,
Wanda ya san hikimar Maɗaukaki,
Wanda yake ganin wahayin Mai Iko Dukka,
Yana durƙurshe, amma idanunsa a buɗe suke.
17 Ina ganinsa, amma ba yanzu ba,
Ina hangensa, amma ba kusa ba.
Tauraro zai fito daga cikin Yakubu,
Kandiri zai fito daga cikin Isra’ila,
Zai ragargaje goshin Mowabawa,
Zai kakkarya ‘ya’yan Shitu duka.
18 Za a mallaki Edom,
Hakka kuma za a mallaki Seyir abokiyar gābanta,
Isra’ila za ta gwada ƙarfi.
19 Yakubu zai yi mulki,
Zai hallaka waɗanda suka ragu cikin birni.”
20 Sai ya dubi Amalek, ya hurta jawabinsa, ya ce,
“Amalek na fari ne cikin al’ummai,
amm ƙarshensa hallaka ne.”
21 Sai kuma ya dubi Keniyawa, ya hurta jawabinsa, ya ce,
“Wurin zamanku mai ƙarƙo ne,
Gidajenku kuma suna cikin duwatsu.
22 Duk da haka za a lalatar da Keniyawa.
Har yaushe za ku zama bayin Assuriyawa?”
23 Sai kuma ya hurta jawabinsa, ya ce,
“Kaito, wa zai rayu sa’ad da Allah ya yi wannan?
24 Jiragen ruwa kuwa za su zo daga Kittim,
Za su wahalar da Assuriya da Eber,
Su kuma da kansu za su lalace.”
25 Sai Bal’amu ya tashi ya koma garinsu, Balak kuma ya yi tafiyarsa.