Isra’ilawa sun yi Sujada ga Ba’al-feyor
1 Sa’ad da Isra’ilawa suka yi zango a Shittim, maza suka fara yin lalata da matan Mowabawa.
2 Waɗannan mata sukan gayyaci mutanen zuwa wajen shagalin tsafinsu. Isra’ilawa kuwa sukan ci abinci, su kuma yi sujada ga gumaka.
3 Ta haka Isra’ilawa suka shiga bautar gumakan Ba’al na Feyor. Sai Ubangiji ya husata da Isra’ilawa.
4 Ya ce wa Musa, “Ɗauki sugabannin jama’a, ka rataye su a rana a gabana don in huce daga fushin da nake yi da Isra’ilawa.”
5 Musa kuwa ya ce wa alƙalan Isra’ilawa, “Kowa ya kashe mutanensa da suka shiga bautar gumakan Ba’al-feyor.”
6 Sai ga wani Ba’isra’ile ya taho da wata mace, Bamadayaniya, ya kai ta alfarwarsa ƙiriƙiri a gaban Musa da dukan taron jama’ar Isra’ila a sa’ad da suke kuka a ƙofar alfarwa ta sujada.
7 Finehas ɗan Ele’azara, wato jikan Haruna, firist, ya gani, sai ya tashi daga cikin taron, ya ɗauki mashi.
8 Ya bi Ba’isra’ilen, har zuwa ƙuryar alfarwar, ya soke dukansu biyu, Ba’isra’ilen da macen, har ya sha zarar macen. Da haka aka tsai da annoba daga Isra’ilawa.
9 Duk da haka annobar ta kashe mutane dubu ashirin da dubu huɗu (24,000).
10 Sai Ubangiji ya ce wa Musa,
11 “Finehas ɗan Ele’azara, wato jikan Haruna, firist, ya kawar da fushina daga Isra’ilawa saboda ya yi kishi irin nawa a gabansu, don haka ban shafe Isra’ilawa saboda kishina ba.
12 Domin haka ina yi masa alkawarin da ba zai ƙare ba.
13 Alkawarin zai zama nasa da na zuriyarsa, wato alkawarin zama firist din din din, domin ya yi kishi saboda Allahnsa. Ya kuwa yi kafara domin Isra’ilawa.”
14 Sunan Ba’isra’ilen da aka kashe tare da Bamadayaniyar, Zimri ɗan Salu, shi ne shugaban gidan Saminawa.
15 Sunan Bamadayaniya kuwa, Kozbi, ‘yar Zur. Shi ne shugaban mutanen gidan ubansa a Madayana.
16 Ubangiji kuma ya umarci Musa, ya ce,
17 “Ku fāɗa wa Madayanawa ku hallaka su.
18 Gama sun dame ku da makircinsu da suka yaudare ku a kan al’amarin Feyor da na Kozbi ‘yar’uwarsu, ‘yar shugaban Madayana, wadda aka kashe a ranar da aka yi annoba a Feyor.”