Kabilai a Gabashin Urdun
1 Kabilan Ra’ubainu da Gad suna da dabbobi da yawa ƙwarai. Da suka ga ƙasar Yazar da ta Gileyad wuri ne mai kyau domin shanu,
2 sai suka je wurin Musa da Ele’azara firist, da shugabannin taron jama’ar,
3 suka ce, “Atarot, da Dibon, da Yazar, da Bet-nimra, da Heshbon, da Eleyale, da Simba, da Nebo, da Ba’al-meyon,
4 ƙasar da Ubangiji ya ci da yaƙi a gaban taron jama’a, ƙasa ce mai kyau don dabbobi. Ga shi kuwa, barorinka suna da dabbobi da yawa.
5 Idan mun sami tagomashi a gare ka, ka ba mu wannan ƙasa ta zama mallakarmu, kada ka kai mu a wancan hayin Urdun.”
6 Amma Musa ya amsa musu ya ce, “Wato sai ‘yan’uwanku su yi ta yaƙi,ku kuwa ku yi zamanku a nan, ko?
7 Don me za ku karya zuciyar jama’ar Isra’ila daga hayewa zuwa ƙasar da Ubangiji ya ba su?
8 Haka iyayenku suka yi sa’ad da na aike su daga Kadesh-barneya don su dubo ƙasar.
9 Gama sa’ad da suka tafi Kwarin Eshkol suka ga ƙasar, suka karya zuciyar jama’a daga shigar ƙasar da Ubangiji ya ba su.
10 Saboda haka Ubangiji ya husata a ranan nan, har ya yi wa’adi ya ce,
11 ‘Hakika ba wani daga cikin mutanen da suka fito daga Masar, tun daga mai shekara ashirin zuwa gaba da zai ga ƙasar da na rantse zan ba Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, domin ba su bi ni sosai ba.
12 Sai dai Kalibu, ɗan Yefunne Bakenizze, da Joshuwa ɗan Nun, domin su ne kaɗai suka bi ni sosai.’
13 Saboda Ubangiji ya husata da isra’ilawa, shi ya sa suka yi ta yawo a jeji har shekara arba’in, wato sai da tsaran nan wadda ta aikata mugunta a gaban Ubangiji ta ƙare.
14 Ga shi, ku kuma da kuke ‘ya’yan mugayen mutanen nan, ku da kuke a matsayin iyayenku, kuna so ku ƙara sa Ubangiji ya husata da Isra’ilawa.
15 Gama idan kun ƙi binsa, zai sāke yashe ku a jeji. Ku ne kuwa za ku zama sanadin hallakar mutanen nan duka.”
16 Sai suka zo kusa da shi, suka ce, “Za mu gina garu na dutse don mu kāre dabbobinmu, da birane don ‘ya’yanmu a nan.
17 ‘Ya’yanmu za su zauna a biranen don gudun mazaunan ƙasar, amma mu za mu ɗauki makamai mu tafi tare da sauran Isra’ilawa, har mu kai su wuraren zamansu.
18 Ba kuwa za mu koma gidajenmu ba, sai lokacin da kowane Ba’isra’ile ya sami gādonsa.
19 Gama ba za mu ci gādo tare da su a wancan hayin Urdun ba, domin mun sami gādonmu a wannan hayi na gabashin Urdun.”
20 Sai Musa ya ce musu, “Idan za ku yi haka, wato ku ɗauki makamai, ku tafi yaƙi a gaban Ubangiji,
21 kowane sojanku ya haye Urdun a gaban Ubangiji, har lokacin da Ubangiji ya kori abokan gābansa daga gabansa,
22 har kuma lokacin da aka ci ƙasar a gaban Ubangiji kafin ku koma, to, za ku kuɓuta daga alhakinku a gaban Ubangiji da jama’ar Isra’ila. Wannan ƙasa kuwa za ta zama mallakarku a gaban Ubangiji.
23 Idan kuwa ba ku yi haka ba, kun yi wa Ubangiji laifi, ku tabbata fa alhakin zunubinku zai kama ku.
24 To, sai ku gina wa ‘ya’yanku birane, ku gina wa garkunanku garu, amma ku aikata abin da kuka faɗa da bakinku.”
25 Sai Gadawa da Ra’ubainawa suka amsa wa Musa, suka ce, “Barorinka za su yi kamar yadda ka umarta.
26 ‘Ya’yanmu, da matanmu, da tumakinmu, da shanunmu za su zauna a birane a nan Gileyad.
27 Amma kowane soja a cikinmu zai haye a gaban Ubangiji zuwa yaƙi kamar yadda shugabanmu ya faɗa.”
28 Sai Musa ya yi wa Ele’azara firist, da Joshuwa ɗan Nun, da shugabannin gidajen kakannin kabilan mutanen Isra’ila kashedi a kansu,
29 ya ce, “Idan kowane soja na Gadawa da Ra’ubainawa zai haye Urdun tare da ku don yaƙi har an ci ƙasar dominku, to, sai ku ba su ƙasar Gileyad ta zama mallakarsu.
30 Amma idan ba su haye tare da ku da shirin yaƙi ba, to, sai ku ba su gādo tare da ku a cikin ƙasar Kan’aniyawa.”
31 Gadawa da Ra’ubainawa kuwa suka ce, “Kamar yadda Ubangiji ya ce wa barorinka, haka za mu yi.
32 Za mu haye da shirin yaƙi a gaban Ubangiji zuwa cikin ƙasar Kan’aniyawa, amma za mu sami gādonmu a wannan hayin Urdun.”
33 Sa’an nan Musa ya ba Gadawa, da Ra’ubainawa, da rabin mutanen Manassa, ɗan Yusufu, mulkin Sihon, Sarkin Amoriyawa, da mulkin Og, Sarkin Bashan, wato ƙasar da biranenta da karkaransu.
34 Sai Gadawa suka gina Dibon, da Atarot, da Arower,
35 da Atarot-shofan, da Yazar, da Yogbeha,
36 da Bet-nimra, da Bet-aram su zama birane masu garu da shinge don dabbobi.
37 Ra’ubainawa kuwa suka gina Heshbon da Eleyale, da Kiriyatayim,
38 da Nebo, da Ba’al-meyon, da Sibma.
39 Mutanen Makir, ɗan Manassa, suka tafi Gileyad, suka ci ta da yaƙi, suka kori Amoriyawan da suke cikinta.
40 Sai Musa ya ba mutanen Makir, ɗan Manassa, Gileyad, suka zauna ciki.
41 Yayir, ɗan Manassa, ya tafi ya ci ƙauyukansu da yaƙi, suka ba su suna Hawot-yayir.
42 Noba kuma ya tafi ya ci Kenat da ƙauyukanta da yaƙi, ya ba ta suna Noba bisa ga sunansa.