Gādon Matan Aure
1 Sai shugabannin gidajen iyalan ‘ya’yan Gileyad, ɗan Makir, jikan Manassa, ɗan Yusufu, suka zo suka yi magana da Musa da sauran shugabanni.
2 Suka ce, “Ubangiji ya umarce ka ka raba wa Isra’ilawa gādon ƙasar ta hanyar jefa kuri’a. Ubangiji kuwa ya umarce ka ka ba ‘ya’ya mata na Zelofehad, ɗan’uwanmu, gādo.
3 Amma idan suka auri waɗansu daga waɗansu kabilan jama’ar Isra’ila, wato za a ɗebe gādonsu daga gādon kakanninmu a ƙara wa gādon kabilan mutanen da suka aura, wato ka ga an ɗebe daga cikin namu gādo ke nan.
4 Sa’ad da shekara ta hamsin ta murnar Isra’ilawa ta kewayo, za a haɗa gādonsu da na kabilan mutanen da suka aura, da haka za a ɗebe gādonsu daga gādon kabilar kakanninmu.”
5 Musa kuwa ya umarci Isra’ilawa bisa ga faɗar Ubangiji ya ce, “Abin da mutanen kabilar ‘ya’yan Yusufu suka faɗa daidai ne.
6 Abin da Ubangiji ya umarta a kan ‘ya’ya mata na Zelofehad ke nan, ‘A bar su su auri wanda suka ga dama, amma sai a cikin iyalin kabilar kakansu.
7 Ba za a sāke gādon Isra’ilawa daga wata kabila zuwa wata ba, gama kowane mutum na cikin jama’ar Isra’ila zai riƙe gādonsa na kabilar kakanninsa.
8 Kowace ‘ya mace wadda ta ci gādo a wata kabilar Isra’ila, sai ta yi aure a cikin kabilar kakanta domin kowane Ba’isra’ile ya ci gādon kakanninsa.
9 Ta yin haka ba za a sāke gādo daga wata kabila zuwa wata ba, gama kowace kabilar Isra’ila za ta riƙe gādonta.’ ”
10 Sai ‘ya’yan Zelofehad mata, wato Mala, da Tirza, da Hogla, da Milka, da Nowa suka yi kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.
11 Suka auri ‘ya’yan ‘yan’uwan mahaifinsu.
12 Sun yi aure a cikin iyalan ‘ya’yan Manassa, ɗan Yusufu. Gādonsu kuwa bai ɓalle daga cikin kabilar iyalin kakansu ba.
13 Waɗannan su ne umarnai da ka’idodi waɗanda Ubangiji ya ba jama’ar Isra’ila ta wurin Musa a filayen Mowab kusa da Urdun daura da Yariko.