Ka’idodin Zama Keɓaɓɓe
1 Ubangiji kuma ya umarci Musa
2 ya faɗa wa Isra’ilawa, cewa idan mace ko namiji ya ɗau wa’adi na musamman na zama keɓaɓɓe domin ya keɓe kansa ga Ubangiji,
3 sai ya keɓe kansa daga ruwan inabin da yake sa maye da ruwan inabi mai tsami. Kada kuma ya sha ruwan inabi mai tsami da yake sa maye da kowane irin abin sha da aka yi da ‘ya’yan inabi mai tsami. Kada kuma ya ci ɗanyu ko busassun ‘ya’yan inabi.
4 A dukan kwanakin nan da ya keɓe kansa, kada ya ci kowane irin abu da aka yi da kurangar inabi, ko da ƙwayar inabi ko da ɓawonsa.
5 A dukan kwanakin wa’adinsa na keɓewa, kada aska ta taɓa kansa, sai kwanakin keɓewar kansa ga Ubangiji sun cika. Zai zama mai tsarki, zai kuma bar sumarsa ta yi tsawo.
6 A dukan kwanakin da ya keɓe kansa ga Ubangiji, kada ya kusaci gawa.
7 Ko ta mahaifinsa ce, ko ta mahaifiyarsa, ko ta ɗan’uwansa, ko ta ‘yar’uwarsa, ba zai ƙazantar da kansa ba, tun da yake ya keɓe kansa ga Allahnsa.
8 Shi tsattsarka ne ga Ubangiji dukan kwanakin da ya keɓe kansa.
9 Idan farat ɗaya wani mutum ya rasu kusa da shi, to, keɓewarsa ta ƙazantu, sai ya aske kansa a ranar tsarkakewarsa a kan rana ta bakwai.
10 A rana ta takwas kuwa zai kawo wa firist ‘yan kurciyoyi biyu, ko ‘yan tattabarai biyu a bakin ƙofar alfarwa ta sujada.
11 Sai firist ya miƙa ɗaya don hadayar zunubi, ɗaya kuma don hadayar ƙonawa, ya yi kafara dominsa, gama ya yi zunubi saboda gawa. A wannan rana zai sāke keɓe kansa.
12 Sai ya sāke keɓe kansa ga Ubangiji daidai da kwanakin da ya ɗauka a dā. Zai kawo ɗan rago bana ɗaya na yin hadaya don laifi. Kwanakin da ya yi a dā ba su cikin lissafi domin keɓewarsa ta dā ta ƙazantu.
13 Wannan ita ce ka’idar zama keɓaɓɓe a ranar da keɓewarsa ta cika. Za a kai shi ƙofar alfarwa ta sujada,
14 ya miƙa wa Ubangiji hadayarsa ta ɗan rago bana ɗaya mara lahani don yin hadaya ta ƙonawa, da ‘yar tunkiya bana ɗaya marar lahani ta yin hadaya don zunubi, da rago marar lahani don yin hadaya ta salama,
15 da kwandon abinci marar yisti da aka yi da lallausan gari kwaɓaɓɓe da mai, da ƙosai wanda aka yayyafa masa mai, da hadaya ta gari, da hadayu na sha.
16 Sai firist ɗin ya kai su gaban Ubangiji, ya miƙa hadaya don zunubi, da hadaya ta ƙonawa.
17 Ya kuma miƙa rago don hadaya ta salama ga Ubangiji tare da kwandon abinci, da ƙosai. Firist ɗin kuma zai miƙa hadaya ta gari, da hadaya ta sha.
18 Sai kuma keɓaɓɓen ya aske sumarsa a ƙofar alfarwa ta sujada, sa’an nan ya kwashe sumar, ya zuba cikin wutar da take ƙarƙashin hadaya ta salama.
19 Firist ɗin zai ɗauki dafaffiyar kafaɗar ragon, da malmala guda marar yisti daga cikin kwando, da ƙosai guda, ya sa su a tafin hannun keɓaɓɓen bayan da keɓaɓɓen ya riga ya aske sumarsa.
20 Firist ɗin zai haɗa su don yin hadayar kaɗawa a gaban Ubangiji. Za su zama rabo mai tsarki na firist tare da ƙirjin da aka kaɗa da cinyar da aka yi hadayar ɗagawa da ita. Bayan haka keɓaɓɓen ya iya shan ruwan inabi.
21 Wannan ita ce ka’ida a kan keɓaɓɓe wanda ya ɗau wa’adi. Hadayarsa ga Ubangiji za ta zama bisa ga keɓewarsa, banda kuma abin da ya iya bayarwa. Sai ya cika wa’adin da ya ɗauka bisa ga ka’idar keɓewarsa.
Albarkar da Firist zai Sa wa Jama’a
22 Ubangiji ya umarci Musa
23 ya faɗa wa Haruna da ‘ya’yansa maza, su sa wa Isra’ilawa albarka haka, su ce musu,
24 “Ubangiji ya sa muku albarka, ya kiyaye ku.
25 “Ubangiji ya sa fuskarsa ta haskaka ku, ya yi muku alheri.
26 “Ubangiji ya dube ku da idon rahama, ya ba ku salama.”
27 Idan suka sa wa jama’a wannan albarka sa’ad da suke addu’a ga Ubangiji domin Isra’ilawa, Ubangiji zai sa musu albarka.