Dokoki a kan Tsarki da Yin Adalci
1 Ubangiji ya ce wa Musa
2 ya faɗa wa dukan taron jama’ar Isra’ila cewa, “Ku zama tsarkakakku, gama ni Ubangiji Allahnku mai tsarki ne.
3 Sai ko wannenku ya girmama mahaifiyarsa da mahaifinsa, ya kuma kiyaye lokatan sujada. Ni ne Ubangiji Allahnku.
4 “Kada ku juya ku bi gumaka, ko kuma ku yi wa kanku gumaka na zubi. Ni ne Ubangiji Allahnku.
5 “Sa’ad da za ku miƙa hadaya ta salama ga Ubangiji, ku miƙa ta domin a karɓe ku.
6 A cinye ta a ranar da kuka miƙa ta ko kuwa kashegari. Abin da ya ragu har kwana na uku, sai a ƙone da wuta,
7 gama ta zama abar ƙyama, idan aka ci ta a rana ta uku, ba za ta zama abar karɓa ba.
8 Wanda ya ci ta a rana ta uku ɗin, zai zama da laifi, domin ya tozartar da abu mai tsarki na Ubangiji, sai a raba wannan mutum da jama’a.
9 “Sa’ad da kuke girbin amfanin ƙasarku, kada ku girbe gefen gonakinku, kada kuma ku yi kala bayan da kuka gama girbi.
10 Kada ku girbe kalar gonar inabinku, kada kuma ku tattara ‘ya’yan inabinku da suka kakkaɓe, sai ku bar wa matalauta, da baƙo. Ni ne Ubangiji Allahnku.
11 “Kada ku yi sata, ko ku cuci wani, ko ku yi ƙarya.
12 Kada ku yi alkawari da sunana idan dai ba ku da niyyar cika shi, wannan zai jawo wa sunana ƙasƙanci. Ni ne Ubangiji Allahnku.
13 “Kada ku zalunci kowa ko ku yi masa ƙwace. Kada kuma ku bar lokacin biyan hakkin ma’aikaci ya kai har gobe.
14 Kada ku zagi kurma, kada kuma ku sa wa makaho abin tuntuɓe, amma ku ji tsoron Ubangiji Allahnku. Ni ne Ubangiji.
15 “Ku yi gaskiya da adalci cikin shari’a, kada ku ma ku yi wa matalauci son zuciya, ko ku goyi bayan mawadaci.
16 Kada ku yi ta yaɗa ƙarya game da wani. Sa’ad da wani yake cikin shari’ar kuɓutar da ransa, ku yi magana muddin dai shaidarku za ta taimake shi. Ni ne Ubangiji.
17 “Kada wani ya riƙe ɗan’uwansa da ƙiyayya a zuciyarsa, amma ya daidaita rashin jituwa da shi, don kada ya yi zunubi saboda shi.
18 Kada ya ɗaukar wa kansa fansa a kan wani ko ya yi ta ƙinsa, amma ya ƙaunaci sauran mutane kamar yadda yake ƙaunar kansa. Ni ne Ubangiji.
19 “Sai ku kiyaye dokokina. Kada ku bar dabbobinku su yi barbara da waɗansu iri dabam. Kada ku shuka iri biyu a gonakinku. Kada ku sa tufar da aka yi da ƙyalle iri biyu.
20 “Idan mutum ya kwana da mace wadda take baiwa, wadda kuma wani yake tashinta, tun ba a fanshe ta ba, ko kuwa ba a ‘yanta ta ba, sai a bincike, amma ba za a kashe su ba, domin ita ba ‘yantacciya ba ce.
21 Amma ya kawo rago na yin hadaya don laifinsa ga Ubangiji a ƙofar alfarwa ta sujada.
22 Sai firist ya yi kafara da ragon hadaya don laifi saboda laifin mutumin a gaban Ubangiji. Za a kuwa gafarta masa zunubin da ya yi.
23 “Sa’ad da kuka shiga ƙasar, kuka dasa itatuwa iri iri masu ba da ‘ya’ya na ci, ‘ya’yan itatuwan za su zama ƙazantattu a gare ku har shekara uku. A cikin shekarun nan uku ba za ku ci su ba.
24 A shekara ta huɗu ‘ya’yan itatuwan za su tsarkaka. Hadaya ce ta yabo ga Ubangiji.
25 Amma a shekara ta biyar, sai ku ci ‘ya’yan itatuwan domin su ba ku amfani a yalwace. Ni ne Ubangiji Allahnku.
26 “Kada ku ci kowane abu da jininsa, kada kuma ku yi duba, ko sihiri.
27 Kada ku yi wa goshinku da gemunku kwakkwafe saboda matattu,
28 ko ku tsattsaga jikinku, ko kuwa ku yi wa kanku jarfa. Ni ne Ubangiji.
29 “Kada ku ƙasƙantar da ‘ya’yanku mata ta wurin sa su su zama karuwan masujadai, idan kuka yi haka, za ku juya ga gumaka, ƙasar za ta cika da lalata.
30 Sai ku kiyaye lokatan sujada, ku kuma darajanta alfarwata mai tsarki. Ni ne Ubangiji.
31 “Kada ku tafi wurin masu mabiya, kada kuma ku nemi shawarar bokaye, domin kada su sa ku ku ƙazantu. Ni ne Ubangiji Allahnku.
32 “Ku girmama tsofaffi ku darajanta su, gama kuna tsorona. Ni ne Ubangiji.
33 “Idan baƙo ya baƙunce ku a ƙasarku, kada ku cuce shi.
34 Amma ku ɗauke shi tankar ɗan ƙasa, ku ƙaunace shi kamar kanku, gama dā ku ma baƙi ne a ƙasar Masar. Ni ne Ubangiji Allahnku.
35 “Kada ku cuci wani wajen yin amfani da kowane irin ma’auni na ƙarya, wato, awon tsawo, ko na nauyi, ko na ruwa.
36 Sai ma’auninku na awon nauyi, da mudun awo, da mudun awon abin da yake ruwa ruwa, su zama na gaskiya. Ni ne Ubangiji Allahnku wanda ya fisshe ku daga ƙasar Masar.
37 Sai ku kiyaye, ku aikata dokokina da umarnaina duka. Ni ne Ubangiji.”