Gudunmawa ga Tsarkaka
1 To, a yanzu kuma ga zancen ba da gudunmawa ga tsarkaka, kamar yadda na umarci ikilisiyoyin Galatiya, haka ku ma za ku yi.
2 A kowace ranar farko ta mako, kowannenku ya riƙa tanada wani abu, yana ajiyewa gwargwadon samunsa, kada sai na zo tukuna, a tara gudunmawa.
3 Sa’ad da na iso, sai in aiki waɗanda kuka amince da su da wasiƙa, su kai taimakonku Urushalima.
4 In ya kyautu ni ma in tafi, to, sai su raka ni.
Shirye-shiryen Tafiya
5 Zan zo gare ku bayan na zazzaga ƙasar Makidoniya, don kuwa ta Makidoniya zan bi.
6 Watakila zan jima a wurinku, ko ma in ci damina, don ku yi mini rakiya duk in da za ni.
7 Ba sona ne in gan ku a yanzu in wuce kawai ba, a’a, ina sa zuciya ma in yi kwanaki a wurinku, in Ubangiji ya yarda.
8 Amma zan dakata a Afisa har ranar Fentikos.
9 Don kuwa, an buɗe mini wata hanya mai fāɗi ta yin aiki mai amfani, akwai kuma magabta da yawa.
10 In Timoti ya zo, ku tabbata ya sami sakewa a cikinku, domin aikin Ubangiji yake yi kamar yadda nake yi.
11 Kada fa kowa yă raina shi. Ku raka shi lafiya, ya komo a gare ni, domin ina duban hanyarsa tare da ‘yan’uwa.
12 Ga zancen ɗan’uwanmu Afolos kuwa, na roƙe shi ƙwarai, don yă zo wurinku, tare da saurar ‘yan’uwa, amma ko kusa bai yi nufin zuwa a yanzu ba. Zai zo dai sa’ad da ya ga ya dace.
Gargaɗi da Gaisuwa
13 Ku zauna a faɗake, ku dāge ga bangaskiyarku, ku yi ƙwazo, ku yi ƙarfi.
14 Duk abin da za ku yi, ku yi shi da ƙauna.
15 To, ‘yan’uwa, kun sani fa jama’ar gidan Istifanas su ne nunan fari a ƙasar Akaya, sun kuwa ba da kansu ga yi wa tsarkaka hidima.
16 Ina roƙonku ku yi wa irin waɗannan mutane biyayya, har ma ga duk waɗanda suke abokan aikinmu da wahalarmu.
17 Na yi farin ciki da zuwan Istifanas, da Fartunatas, da Akaikas, domin sun ɗebe mini kewarku.
18 Sun dai wartsakar da ni da kuma ku. Sai ku kula da irin waɗannan mutane.
19 Ikilisiyoyin ƙasar Asiya suna gaishe ku. Akila da Bilkisu, tare da ikkilisiyar da take taruwa a gidansu, suna gaishe ku da kyau da kyau saboda Ubangiji.
20 Dukan ‘yan’uwa suna gaishe ku. Ku gaggai da juna da tsattsarkar sumba.
21 Ni Bulus, ni nake rubuta gaisuwar nan da hannuna.
22 Duk wanda ba ya ƙaunar Ubangiji yă zama la’ananne. Ubangijinmu fa yana zuwa!
23 Alherin Ubangijinmu Yesu yă tabbata a gare ku.
24 Ina gaishe ku duka, gaisuwar ƙauna, albarkar Almasihu Yesu.