Wajibi ga Juna
1 Kada ka tsauta wa dattijo, sai dai ka roƙe shi kamar mahaifinka. Samari kuma ka ɗauke su kamar ‘yan’uwanka,
2 tsofaffi mata kuma kamar uwayenka, ‘yan mata kuwa kamar ‘yan’uwanka, da matuƙar tsarkaka.
3 Ka girmama gwauraye mata, waɗanda ba sa da mataimaka.
4 In wata gwauruwa tana da ‘ya’ya ko jikoki, sai su koya, ya wajaba su fara nuna wa danginsu bautar Allah da suke yi, su kuma sāka wa iyayensu da alheri. Wannan abin karɓa ne a gun Allah.
5 Gwauruwa marar mataimaki kuwa, mai zaman kaɗaici, ta dogara ga Allah ke nan, tana nacewa ga roƙon Allah, tana addu’a dare da rana.
6 Amma wadda take zaman annashuwa kuwa, kamar matacciya take, ko da tana a raye.
7 Ka umarce su a game da waɗannan abubuwa, don su kasance marasa abin zargi.
8 Duk wanda bai kula da danginsa ba, tun ba ma iyalinsa ba, ya mūsa wa bangaskiya ke nan, ya kuma fi marar ba da gaskiya mugunta.
9 Kada a lasafta gwauruwa a cikin gwauraye, sai dai ta kai shekara sittin, ba ta yi aure fiye da ɗaya ba,
10 wadda ake yabo a kan kyawawan ayyukanta, wadda kuma ta goyi ‘ya’ya sosai, ta yi wa baƙi karamci, ta wanke ƙafafun tsarkaka, ta taimaki ƙuntatattu, ta kuma nace wa yin kowane irin aiki nagari.
11 Amma kada ka lasafta gwauraye masu ƙuruciya waɗanda mazansu suka mutu, a cikin gwaurayen, don in zuciyarsu ta kasa daurewa a game da wa’adin da suka yi da Almasihu, sai su so yin aure,
12 hukunci yā kama su ke nan, tun da yake sun ta da wa’adinsu na farko.
13 Banda haka kuma sukan koyi zaman banza, suna zirga-zirga gida gida. Ba ma kawai masu zaman banza za su zama ba, har ma sai su zama matsegunta, masu shishigi, suna faɗar abin da bai kamata ba.
14 Saboda haka, ina so gwauraye masu ƙuruciya waɗanda mazansu suka mutu su yi aure, su haifu, su tafiyar da al’amuran gida, kada su ba magabci hanyar zarginmu.
15 Gama waɗansu ma har sun bauɗe, sun bi Shaiɗan.
16 Duk mace mai bi, da take da dangi gwauraye mata, sai ta taimake su, kada a nauwaita wa ikkilisiya, don ikkilisiyar ta samu ta taimaki gwauraye marasa mataimaka.
17 Dattawan ikkilisiya da suke a riƙe da al’amura sosai, a girmama su ninkin ba ninkin, tun ba ma waɗanda suke fama da yin wa’azi da koyarwa ba.
18 Domin Nassi ya ce, “Kada ka sa wa takarkari takunkumi sa’ad da yake sussuka.” Ya kuma ce, “Ma’aikaci ya cancanci ladarsa.”
19 Kada ka yarda in an kawo ƙarar wani dattijon ikkilisiya, sai dai da shaidu biyu ko uku.
20 Masu yin zunubi kuwa, sai ka tsawata musu a gaban dukkan jama’a, don saura su tsorata.
21 Na gama ka da Allah, da Almasihu Yesu, da kuma zaɓaɓɓun mala’iku, ka kiyaye waɗannan abubuwa ƙwarai da gaske, kada ka yi kome da tāra.
22 Kada ka yi garajen ɗora wa kowa hannu, kada kuwa zunuban waɗansu su shafe ka. Ka tsare kanka a tsarkake.
23 A nan gaba ba ruwa kaɗai za ka sha ba, sai dai ka sha ruwan inabi kaɗan saboda cikinka, da kuma yawan laulayinka.
24 Zunuban waɗansu mutane a fili suke, tun ba a kai gaban shari’a ba. Zunuban waɗansu kuwa, sai daga baya suke bayyana.
25 Haka kuma, kyawawan ayyukan waɗansu a fili suke, waɗanda ba haka suke ba, ba za su tabbata a ɓoye ba.