1 Duk ɗaukacin masu igiyar bauta a wuyansu, su ɗauki iyayengijinsu a kan sun cancanci a girmama su matuƙa, don kada a ɓata sunan Allah da kuma koyarwar nan.
2 Waɗanda suke da iyayengiji masu ba da gaskiya, kada su raina su, domin su ‘yan’uwa ne a gare su. Sai ma su ƙara bauta musu, tun da yake waɗanda suke moron aikin nan nasu masu ba da gaskiya ne, ƙaunatattu kuma a gare su.
Bin Allah da Wadar Zuci
Ka koyar da waɗannan abubuwa, ka kuma yi gargaɗinsu.
3 Duk wanda yake wata koyarwa dabam, bai kuwa yarda da sahihiyar maganar Ubangijinmu Yesu Almasihu, da kuma koyarwar da ta dace da bautar Allah ba,
4 girmankai ya ciccika shi ke nan, bai san kome ba, yana da muguwar jarabar gardama da jayayya a kan maganganu kawai, waɗanda suke jawo hassada, da husuma, da yanke, da mugayen zace-zace,
5 da kuma yawan tankiya a cikin mutane masu ɓataccen hankali, waɗanda har gaskiya ta ƙaurace musu, suna tsammani bin Allah hanya ce ta samu.
6 Bin Allah a game da wadar zuci kuwa riba ce mai yawa.
7 Don ba mu zo duniya da kome ba, ba kuwa za mu iya fita da kome ba.
8 To, in muna da abinci da sutura, ai, sai mu dangana da su.
9 Masu ɗokin yin arziki kuwa, sukan zarme da jaraba, su fāɗa a cikin tarko, suna mugayen sha’awace-sha’awace iri iri na wauta da cutarwa, irin waɗanda suke dulmuyar da mutane, su kai ga lalacewa da hallaka.
10 Ai, son kuɗi shi ne tushen kowane irin mugun abu. Don tsananin jarabar kuɗi kuwa waɗansu mutane, har sun bauɗe wa bangaskiya, sun jawo wa kansu baƙin ciki iri iri masu sukar rai.
Famar Gaske saboda Bangaskiya
11 Amma, ya kai, bawan Allah, ka guje wa waɗannan abubuwa, ka dimanci aikin adalci, da bin Allah, da bangaskiya, da ƙauna, da jimiri, da kuma tawali’u.
12 Ka yi fama, famar gaske saboda bangaskiya, ka riƙi rai madawwamin nan, wanda aka kira ka saboda shi, sa’ad da ka bayyana yarda, kyakkyawar bayyana yarda, a gaban shaidu masu yawa.
13 Na gama ka da Allah mai raya kome, na kuma gama ka da Almasihu Yesu, wanda ya yi shaida, kyakkyawar shaidar nan, a gaban Buntus Bilatus,
14 ka bi umarninsa, ba tare da wani aibi ko zargi ba, har ya zuwa bayyanar Ubangijinmu Yesu Almasihu,
15 wannan kuwa makaɗaicin mamallaki, abin yabo, Sarkin sarakuna. Ubangijin iyayengiji zai bayyana shi a lokacinsa.
16 Shi ne kaɗai marar mutuwa, yake kuma zaune a cikin hasken da ba ya kusatuwa. Shi kuwa ba mutumin da ya taɓa ganinsa, ko kuwa zai iya ganinsa. Girma da madawwamin mulki su tabbata a gare shi. Amin, amin.
17 Masu dukiyar duniyar nan kuwa ka gargaɗe su kada su nuna alfarma, kada kuwa su dogara da dukiya marar tabbata, sai dai ga Allah, wanda yake ba mu kome a yalwace don mu ji daɗinsa.
18 Sai dai su yi nagarta da bijinta a wajen aiki nagari, su kasance masu hannu sake, suna alheri.
19 Ta haka suke kafa wa kansu kyakkyawan tushe don nan gaba, domin su riƙi rai wanda yake na hakika.
20 Ya Timoti, ka kiyaye abin da aka ba ka amana. Ka yi nesa da masu maganganun sāɓo na banza da wofi, da yawan musu da ake ƙarya, ake ce da shi ilimi.
21 Waɗansu kuwa, a garin taƙama, da haka har sun kauce wa bangaskiya.
Alheri yă tabbata a gare ku.