Ruhun Allah da na Magabci
1 Ya ku ƙaunatattuna, ba kowane ruhu za ku gaskata ba, sai dai ku jarraba ku gani ko na Allah ne, don annabawan ƙarya da yawa sun fito duniya.
2 Ta haka za ku san Ruhun Allah, wato, duk ruhun da ya bayyana yarda, cewa Yesu Almasihu ya bayyana ne da jiki, shi ne na Allah.
3 Duk ruhun kuwa da bai bayyana yarda ga Yesu ba, ba na Allah ba ne, wannan shi ne ruhun magabcin nan na Almasihu wanda kuka ji zai zo, a yanzu ma har yana duniya.
4 Ya ku ‘ya’yana ƙanana, ku kam na Allah ne, kun kuma ci nasara a kan waɗannan, domin shi wanda yake zuciyarku ya fi wanda yake duniya ƙarfi.
5 Su kuwa na duniya ne, shi ya sa suke zance irin na duniya, duniya kuwa tana sauraronsu.
6 Mu kam na Allah ne. Duk wanda ya san Allah yakan saurare mu, wanda yake ba na Allah ba kuwa, ba ya sauraronmu. Ta haka muka san Ruhu na gaskiya da ruhu na ƙarya.
Allah Ƙauna Ne
7 Ya ku ƙaunatattuna, sai mu ƙaunaci juna, domin ƙauna ta Allah ce. Duk mai ƙauna kuwa haifaffen Allah ne, ya kuma san Allah.
8 Wanda ba ya ƙauna, bai san Allah ba sam, domin Allah shi ne ƙauna.
9 Ta haka aka bayyana ƙaunar Allah gare mu, da Allah ya aiko da Ɗansa makaɗaici a duniya, domin mu sami rai madawwami ta wurinsa.
10 Ta haka ƙauna take, wato, ba mu ne muka ƙaunaci Allah ba, sai dai shi ne ya ƙaunace mu, ya aiko Ɗansa, hadayar sulhu saboda a gafarta zunubanmu.
11 Ya ku ƙaunatattuna, tun da yake Allah ya ƙaunace mu haka, ai, mu ma ya kamata mu ƙaunaci juna.
12 Ba mutumin da ya taɓa ganin Allah daɗai, amma kuwa in muna ƙaunar juna sai Allah ya dawwama cikinmu, ƙaunar nan tasa kuma tă cika a cikinmu.
13 Ta haka muka sani muna a zaune a cikinsa, shi kuma a cikinmu, saboda Ruhunsa da ya ba mu.
14 Mun duba, muna kuma ba da shaida, cewa Uba ya aiko Ɗan ya zama Mai Ceton duniya.
15 Kowa ya bayyana yarda, cewa Yesu Ɗan Allah ne, sai Allah yă dawwama a cikinsa, shi kuma a cikin Allah.
16 Mun sani, mun kuma gaskata ƙaunar da Allah yake yi mana. Allah shi ne ƙauna wanda yake a dawwame cikin kauna kuwa, ya dawwama a cikin Allah ke nan, Allah kuma a cikinsa.
17 Ta haka ne ƙauna ta cika a gare mu, har mu kasance da amincewa a ranar shari’a, domin kamar yadda yake, haka mu ma muke a duniyar nan.
18 Ba tsoro ga ƙauna, amma cikakkiyar ƙauna takan yaye tsoro. Tsoro kansa ma azaba ne, mai jin tsoro kuwa ba shi da cikakkiyar ƙauna,
19 Muna ƙauna, domin shi ne ya fara ƙaunarmu.
20 Kowa ya ce yana ƙaunar Allah, alhali kuwa yana ƙin dan’uwansa, to, maƙaryaci ne. Don wanda ba ya ƙaunar ɗan’uwansa da yake gani, ba dama ya ƙaunaci Allah wanda bai taɓa gani ba.
21 Wannan kuma shi ne umarnin da muka samu daga gare shi, cewa mai ƙaunar Allah, sai ya ƙaunaci ɗan’uwansa kuma.