Annabawan Ƙarya da Malaman Ƙarya
1 Amma fa annabawan ƙarya sun bayyana a cikin jama’a, kamar yadda za a sami malaman ƙarya a cikinku, waɗanda za su saɗaɗo da maɓarnacciyar fanɗarewa, har ma su ƙi Mamallakin da ya fanso su, suna jawo wa kansu hallaka farat ɗaya.
2 Da yawa kuwa za su bi fajircinsu, har za a kushe hanyar gaskiya saboda su.
3 Mahaɗantan malaman nan na ƙarya za su ribace ku da tsararrun labarunsu. An riga an yanke hukuncinsu tun dā, wanda zai hallaka su a shirye yake sosai.
4 Da yake Allah bai rangwanta wa mala’iku ba sa’ad da suka yi zunubi, sai ya jefa su a Gidan Wuta, ya tura su a cikin ramummuka masu zurfi, masu baƙin duhu, a tsare su har ya zuwa ranar hukunci,
5 tun da yake bai rangwanta wa mutanen tun can dā dā kuma ba, amma ya kiyaye Nuhu mai wa’azin adalci, da waɗansu mutum bakwai, sa’ad da ya aiko da Ruwan Tsufana zuwa a cikin duniyar nan ta marasa bin Allah,
6 da yake kuma ya mai da biranen Saduma da Gwamrata toka, ya yi musu hukuncin hallaka, ya mai da su abin ishara ga marasa bin Allah,
7 da yake kuma ya ceci Lutu adali, wanda fajircin kangararru ya baƙanta masa rai ƙwarai
8 (don kuwa abin da adalin nan ya yi, ya kuma gani, sa’ad da yake a cikinsu, sai kowace rana yakan ji ciwon aikinsu na kangara a zuciyarsa mai adalci),
9 ashe kuwa, Ubangiji ya san yadda zai kuɓutar da masu tsoronsa daga gwaje-gwaje, ya kuma tsare marasa adalci a kan jiran hukunci, har ya zuwa ranar shari’a,
10 tun ba waɗanda suka dulmuya a cikin muguwar sha’awa mai ƙazantarwa ba, suke kuma raina mulki.
Masu tsaurin ido ne su, masu taurin kai kuma, ba sa jin tsoron zagin masu ɗaukaka.
11 Amma kuwa mala’iku, ko da yake sun fi su ƙarfi da iko, duk da haka, ba su ɗora musu laifi da zage-zage a gaban Ubangiji.
12 Amma waɗannan mutane, kamar daddobi marasa hankali suke, masu bin abin da jikinsu ya ba su kawai, waɗanda aka haifa, don a kama a kashe, har suna kushen abubuwan da ba su fahinta ba, lalle kuwa za su hallaka a sanadin ɓacin nan nasu,
13 suna shan sakamakon muguntarsu. Sun ɗauka a kan jin daɗi ne a yi annashuwa da rana kata. Sun baƙanta, sun zama abin kunya. Sun dulmuya ga ciye-ciye da shaye-shaye, suna ta nishaɗi a cikinku.
14 Jarabar zina take a gare su, ba sa ƙoshi da yin zunubi. Suna yaudarar marasa kintsuwa. Sun ƙware da ƙwaɗayi. La’anannun iri!
15 Sun yar da miƙaƙƙiyar hanya, sun bauɗe, sun bi hanyar Bal’amu ɗan Beyor, wanda ya cika son samu ta hanyar mugunta.
16 Amma an tsawata masa a kan laifinsa, har dabba marar baki ma ta yi magana kamar mutum, ta kwaɓi haukan annabin nan.
17 Mutanen nan kamar mabubbugen ruwa wadanda suka kafe, ƙasashi ne da iska take kaɗawa. Su ne aka tanada wa matsanancin duhu.
18 Ta surutai barkatai marasa kan gado na ruba, da halinsu na fasikanci sukan shammaci waɗanda da ƙyar suke kuɓucewa daga masu zaman saɓo,
19 suna yi musu alkawarin ‘yanci, ga shi kuwa, su da kansu bayin zamba ne. Don mutum bawa ne na duk abin da ya rinjaye shi.
20 In kuwa bayan da suka tsere wa ƙazantar duniyar albarkacin sanin Ubangijinmu, Mai Cetonmu Yesu Almasihu, suka kuma sāke sarƙafewa a ciki, har aka rinjaye su, ƙarshen zamansu ya fi na fari lalacewa ke nan.
21 Da ba su taɓa sanin hanyar adalci tun da fari ba, da ya fiye musu, bayan sun san ta, sa’an nan su juya ga barin umarnin nan mai tsarki.
22 Ai kuwa, karin maganar nan na gaskiya ya dace da su cewa, “Kare ya cinye amansa,” da kuma, “Gursunar da aka yi wa wanka ta kome ga birgima cikin laka.”