Gaisuwa
1 Daga Bulus, manzon Almasihu Yesu da yardar Allah, da kuma ɗan’uwanmu Timoti, zuwa ga ikkilisiyar Allah da take a Koranti, tare da dukan tsarkaka na duk ƙasar Akaya.
2 Alheri da salama na Allah Ubanmu, da na Ubangiji Yesu Almasihu su tabbata a gare ku.
Godiyar Bulus Bayan Shan Wuya
3 Godiya ta tabbata a gare shi, shi wanda yake Allah, da Uba na Ubangijinmu Yesu Almasihu, Uba mai yawan jinƙai, Allah na dukan ta’aziyya,
4 shi da yake yi mana ta’aziyya a dukan wahalarmu, domin mu kuma mu iya ta’azantar da masu shan kowace irin wahala, da ta’aziyyar nan da mu ma muka samu a gun Allah.
5 Domin kuwa kamar yadda muke shan wuya ƙwarai, irin wadda Almasihu ya sha, haka kuma ake yi mana ta’aziyya ƙwarai, ta wurin Almasihu.
6 Ko ana wahalshe mu ma, ai, saboda ta’azantuwarku ce, da kuma lafiyarku. Ko ana ta’azantar da mu, ai, saboda ta’azantuwarku ce, wadda take sa ku, ku jure wa irin wuyan nan, da muke sha.
7 Sa zuciyarmu a kanku ƙaƙƙarfa ce, domin mun sani, kamar yadda kuka yi tarayya da mu a cikin shan wuya, haka kuma, za ku yi tarayya a cikin ta’aziyyar.
8 ‘Yan’uwa, ba ma so ku jahilta da wahalar da muka sha a ƙasar Asiya, domin kuwa mun ji jiki ƙwarai da gaske, har abin ya fi ƙarfinmu, har ma muka fid da tsammanin rayuwa.
9 Har ma muka ji kamar hukuncin kisa aka yi mana, wannan kuwa don kada mu dogara ga kanmu ne, sai dai ga Allah, mai ta da matattu.
10 Shi ne ya kuɓutar da mu daga muguwar mutuwa a fili, zai kuwa kuɓutar da mu, ga shi kuma muke dogara yă kuɓutar da mu har ila yau.
11 Ku ma sai ku taimake mu da addu’a, domin mutane da yawa su gode wa Allah, ta dalilinmu, saboda albarkar da aka yi mana, ta amsa addu’o’i masu yawa.
Bulus Ya Dakatar da Ziyararsa
12 Fariyarmu ke nan, lamirinmu yana ba da shaida, cewa mun yi zaman tsarki a duniya da zuciya ɗaya, tsakani da Allah, tun ba ma a gare ku ba, ba bisa ga wayo irin na ɗan adam ba, sai dai bisa ga alherin Allah.
13 Domin wasiƙarmu zuwa gare ku, ba ta ƙunshi wani abu dabam ba, sai dai ainihin abin da kuka karanta kuka kuma fahimta, ina kuwa fata ku fahimta sosai da sosai,
14 kamar yadda kuka riga kuka ɗan fahimce mu, cewa kwa iya yin fāriya da mu, kamar yadda mu ma za mu iya yi da ku, a ranar Ubangijinmu Yesu.
15 Saboda na amince da haka, shi ya sa na so zuwa wurinku da fari, domin ku sami albarka riɓi biyu.
16 Wato niyyata in bi a kanku in za ni Makidoniya, in kuma komo wurinku daga Makidoniya, sa’an nan ku yi mini rakiya in zan tafi Yahudiya.
17 Ashe, a lokacin da na yi niyyar yin haka, wato na nuna rashin tsai da zuciya ke nan? Ko kuwa shiririta nake yi kawai irin ta halin mutuntaka, in ce, “I” in koma in ce, “A’a”?
18 Yadda ba shakka Allah yake mai alkawari, haka ma maganar da muka yi muku, ba shiririta a ciki.
19 Domin kuwa, Ɗan Allah, Yesu Almasihu, wanda ni, da Sila, da Timoti muka yi muku wa’azi, ai, ba shiririta a game da shi, har kullum a kan gaskiya yake.
20 Domin dukan alkawaran Allah cikarsu a gare shi take, ta wurinsa ne kuma muke faɗar “Amin”, domin a ɗaukaka Allah.
21 Domin kuwa, Allah shi ne mai tabbatar da mu da ku gaba ɗaya ga Almasihu, shi ne wanda ya shafe mu kuma.
22 Ya buga mana hatiminsa cewa mu nasa ne, ya kuma yi mana baiwa da Ruhunsa a zukatanmu, domin tabbatar da abin da zai yi a nan gaba.
23 Labudda, Allah shi ne mashaidina a kan cewa, musamman don sawwaƙe muku ne, na fāsa zuwa Koranti.
24 Ba cewa muna nuna muku iko a kan bangaskiyarku ba ne, a’a, sai dai muna aiki tare ne, domin ku yi farin ciki, domin a game da bangaskiyarmu kam, kuna tsaye kankan.