1 Na ƙudura a raina ba zan sāke zuwa wurinku in sa ku baƙin ciki ba.
2 To, in na sa ku baƙin ciki, wa zai faranta mini rai, in ba wanda na sa baƙin cikin ba?
3 Na rubuto muku haka ne, don kada in na zo, waɗanda ya kamata su faranta mini rai, ya zamana sun sa ni baƙin ciki. Domin na amince da ku duka, cewa farin cikina naku ne ku duka.
4 Na rubuto muku ne ina a cikin wahala da baƙin ciki gaya, har da hawaye mai yawa, ba don in sa ku baƙin ciki ba, sai dai domin ku san irin tsananin ƙaunar da nake yi muku.
Gafarta wa Mai Laifi
5 Amma in wani ya jawo baƙin ciki, ba ni kaɗai ya jawo wa ba, amma ga wani fanni, sai in ce dukanku ne ya jawo wa, ba tsanantawa nake yi ba.
6 Irin mutumin nan, horon nan da galibin jama’a suka yi masa, ai, ya isa haka.
7 Gara dai ku yafe masa, ku kuma ƙarfafa masa zuciya, don kada gāyar baƙin ciki ya sha kansa.
8 Saboda haka, ina roƙonku ku tabbatar masa da ƙaunarku.
9 Na rubuto muku wannan takanas, domin in jarraba ku, in ga ko kuna yin biyayya ta kowace hanya.
10 Wanda kuka yafe wa kome, ni ma na yafe masa. Abin da na yafe kuwa, in dai har ma akwai abin yafewa, saboda ku ne na yafe masa, albarkacin Almasihu,
11 don kada Shaiɗan ya ribace mu, gama mu ba jahilan makidodinsa ba ne.
Alhinin Bulus a Taruwasa
12 To, sa’ad da na zo Taruwasa in yi bisharar Almasihu, ko da yake an buɗe mini hanya a cikin Ubangiji,
13 duk da haka dai hankalina bai kwanta ba, domin ban tarar da ɗan’uwana Titus a can ba, saboda haka, sai na yi bankwana da su, na zarce na tafi Makidoniya.
Nasara a Cikin Almasihu
14 Amma godiya ta tabbata ga Allah, shi da kullum yake yi mana jagaba mu ci nasara, albarkacin Almasihu, ta wurinmu kuma yake baza ƙanshin nan, na sanin Almasihu a ko’ina.
15 Don kuwa, a gun Allah mu ne ƙanshin Almasihu a cikin waɗanda ake ceto, da waɗanda suke a hanyar hallaka.
16 Ga na ƙarshe ɗin, ƙanshin nan warin mutuwa ne, mai kaiwa ga hallaka, ga na farkon kuwa, ƙanshin rai ne mai kaiwa ga rai. To, wa zai iya ɗaukar nauyin waɗannan abubuwa?
17 Domin mu ba kamar mutane da yawa muke ba, masu yi wa Maganar Allah algus, mu kaifi ɗaya ne, kamar yadda Allah ya umarce mu, haka muke magana a gaban Allah, muna na Almasihu.