Masu Hidimar Sabon Alkawari
1 Wato, har ila yau, yabon kanmu za mu fara yi kuma? Ko kuwa muna bukatar wasiƙun yabo ne zuwa gare ku, ko daga gare ku, kamar yadda waɗansu suke yi?
2 Ai, ku kanku ku ne wasiƙarmu ta yabo, wadda aka rubuta a zukatanku, domin kowa yă san ta, ya kuma karanta ta.
3 A fili yake, ku wasiƙa ce ta Almasihu, ta hannunmu, ba kuwa rubutun tawada ba ne, amma na Ruhun Allah Rayayye ne, ba kuwa a kan allunan dutse aka rubuta ta ba, sai dai a zuci.
4 Wannan ita ce irin amincewarmu ga Allah ta wurin Almasihu.
5 Ba domin mun isar wa kanmu ba ne, har da za mu ce mu ne muke gudanar da wani abu, a’a, iyawarmu daga Allah take,
6 domin shi ne ya iyar mana muka zama masu hidima na Sabon Alkawari, ba alkawarin rubutacciyar ka’ida ba, sai dai na Ruhu. Don kuwa rubutacciyar ka’ida, kisa take yi, Ruhu kuwa, rayarwa yake yi.
7 Aka zana hidimar Shari’ar Musa, wadda ƙarshenta mutuwa ce, a allunan duwatsu. An bayyana hidimar nan da babbar ɗaukaka, har Isra’ilawa suka kasa duban fuskar Musa saboda tsananin haskenta (ga ta kuwa mai shuɗewa ce).
8 Ina misalin fifikon hidimar Ruhu mafi ɗaukaka?
9 Gama idan hidimar da take jawo hukunci abar ɗaukakawa ce, to, lalle hidimar da take jawo samun adalcin Allah ta fi ta ɗaukaka nesa.
10 Hakika a wannan hali, abin da dā take da ɗaukaka ya rasa ɗaukaka sam, saboda mafificiyar ɗaukakar da ta jice ta.
11 Domin in aba mai shuɗewa an bayyana ta da ɗaukaka, ashe, abin da yake dawwamamme, lalle ne ya kasance da ɗaukakar da ta fi haka nesa.
12 Tun da yake muna da sa zuciya irin wannan, to, muna magana ne gabanmu gaɗi ƙwarai.
13 Ba kamar Musa muke ba, wanda ya rufe fuskarsa da mayafi, don kada Isr’ailawa su ga ƙarewar ɗaukakar nan mai shuɗewa.
14 Amma hankalinsu ya dushe, domin har ya zuwa yau, in ana karatun Tsohon Alkawari, mayafin nan har yanzu ba a yaye yake ba, domin ba ya yayuwa sai ta wurin Almasihu kaɗai.
15 Hakika har ya zuwa yau, duk lokacin da ake karatun littattafan Musa, sai mayafin nan yakan rufe zukatansu.
16 Amma da zarar mutum ya juyo ga Ubangiji, akan yaye masa mayafin.
17 To, Ubangiji fa shi ne Ruhu, a inda Ruhun Ubangiji yake kuma, a nan ‘yanci yake.
18 Mu dukanmu kuma, fuskokinmu ba lulluɓi, muna nuna ɗaukakar Ubangiji, kamar madubi, ana sauya mu mu ɗauki kamanninsa cikin ɗaukaka mai hauhawa. Ubangiji kuwa wanda yake ruhu, yana zartar da haka.