Arziki a Cikin Kasake
1 Saboda haka, da yake muna da wannan hidima bisa ga jinƙan Allah, ba za mu karai ba.
2 Ba ruwanmu da ɓoye-ɓoye na munafunci, ko makirci, ko yi wa Maganar Allah algus, amma ta wurin bayyana gaskiya a fili, sai kowane mutum ya shaidi gaskiyarmu a lamirinsa a gaban Allah.
3 Ko da bishararmu a rufe take, ai, ga waɗanda suke hanyar hallaka kaɗai take a rufe.
4 Su ne marasa ba da gaskiya, waɗanda sarkin zamanin nan ya makantar da hankalinsu, don kada hasken bisharar ɗaukakar Almasihu, shi da yake surar Allah, ya haskaka su.
5 Domin ba wa’azin kanmu muke yi ba, sai dai na Yesu Almasihu a kan shi ne Ubangiji, mu kuwa bayinku ne saboda Yesu.
6 Domin shi Allah wanda ya ce, “Haske yă ɓullo daga duhu ya haskaka,” shi ne ya haskaka zukatanmu domin a haskaka mutane su san ɗaukakarsa a fuskar Yesu Almasihu.
7 Wannan wadata da muke da ita kuwa, a cikin kasake take, wato, jikunanmu, don a nuna mafificin ikon nan na Allah ne, ba namu ba.
8 Ana wahalshe mu ta kowace hanya, duk da haka, ba a ci ɗunguminmu ba. Ana ruɗa mu, duk da haka ba mu karai ba.
9 Ana tsananta mana, duk da haka ba mu zama yasassu ba. Ana ta fyaɗa mu a ƙasa, duk da haka ba a hallaka mu ba.
10 Kullum muna a cikin hatsarin kisa, irin kisan da aka yi wa Yesu, domin a bayyana rayuwar Yesu ta gare mu.
11 Wato, muddin muna a raye, kullum zaman mutuwa muke yi saboda Yesu, domin a bayyana ran Yesu ta wurin jikin nan namu mai mutuwa.
12 Ta haka mutuwa take aikatawa a cikinmu, ku kuwa rai a cikinku.
13 Tun da yake muna da ruhun bangaskiya iri ɗaya da na wanda ya rubuta wannan, “Na gaskata, saboda haka na yi magana,” to, mu ma mun gaskata, saboda haka kuma muke magana.
14 Mun sani shi wannan da ya ta da Ubangiji Yesu daga matattu, mu ma zai tashe mu albarkacin Yesu, yă kuma kawo mu a gabansa tare da ku.
15 Duk wannan fa don amfaninku ne, domin alherin Allah ya yaɗu ga mutane masu yawa, ta haka ya zama sanadin yawaita godiya ga Allah, domin a ɗaukaka Allah.
Rayuwa ta Wurin Bangaskiya
16 Saboda haka ba mu karai ba, ko da yake jikinmu na mutuntaka yana ta lalacewa, duk da haka, ruhunmu a kowace rana sabunta shi ake yi.
17 Don wannan ‘yar wahalar tamu, mai saurin wucewa ita take tanadar mana madawwamiyar ɗaukaka mai yawa, fiye da kwatanci.
18 Domin ba abubuwan da ido yake gani muke dubawa ba, sai dai marasa ganuwa, gama abubuwan da ake gani, masu saurin wucewa ne, marasa ganuwa kuwa, madawwama ne.