Gaisuwa
1 Daga Bulus, da Sila, da Timoti, zuwa ga Ikkilisiyar Tasalonikawa, wadda take ta Allah ubanmu da Ubangiji Yesu Almasihu.
2 Alheri da salama na Allah Uba, da na Ubangiji Yesu Almasihu su tabbata a gare ku.
Bayyanar Almasihu don Yin Hukunci
3 Lalle ne a kullum mu gode wa Allah saboda ku, ‘yan’uwa, haka kuwa ya kyautu, da yake bangaskiyarku haɓaka take yi ƙwarai da gaske, har ma ƙaunar kowane ɗayanku ga juna ƙaruwa take yi.
4 Saboda haka, mu kanmu ma taƙama muke yi da ku a cikin ikilisiyoyin Allah, saboda jimirinku, da bangaskiyarku a cikin yawan tsananin da kuke sha, da ƙuncin da kuke a ciki.
5 Wannan kuwa ita ce tabbatar hukunci mai adalci na Allah, domin a lasafta ku a cikin waɗanda suka cancanci zama a Mulkin Allah, wanda kuke shan wuya dominsa,
6 domin kuwa Allah ya ga adalci ne, yă yi sakamokon ƙunci ga waɗanda suke ƙuntata muku,
7 yă kuma ba ku hutu har da mu ma, ku da ake ƙuntata wa ɗin, a ranar bayyanar Ubangiji Yesu daga Sama tare da manyan mala’ikunsa, a cikin wuta mai ruruwa,
8 yana ta sāka wa waɗanda suke ƙi sanin Allah, da kuma waɗanda suka ƙi bin bisharar Ubangijinmu Yesu.
9 Za su sha hukuncin madawwamiyar hallaka, suna a ware da zatin Ubangiji, da kuma, maɗaukakin ikonsa,
10 wato, a lokacin da ya dawo, tsarkakansa su ɗaukaka shi, duk masu ba da gaskiya kuma su yi al’ajabinsa a ranar nan, don kun gaskata shaidar da muka yi muku.
11 Da wannan maƙasudi, a kullum muke yi muku addu’a, Allahnmu yă sa ku cancanci kiransa, ya biya muku duk muradinku na yin nagarta, da aikin bangaskiya ta wurin ƙarfin ikonsa,
12 don a ɗaukaka sunan Ubangijinmu Yesu a cikinku, ku kuma a cikinsa, bisa ga alherin Allahnmu, da na Ubangiji Yesu Almasihu.