Gaisuwa
1 Daga Bulus, manzon Almasihu Yesu da yardar Allah, don sanar da alkawarin nan na rai wanda yake ga Almasihu Yesu,
2 zuwa ga Timoti ƙaunataccen ɗana.
Alheri, da jinƙai, da salama na Allah Uba, da na Almasihu Yesu Ubangijinmu su tabbata a gare ka.
Kada Ka Ji Kunya
3 Ina gode wa Allah, wanda nake bauta wa da lamiri mai tsabta, kamar yadda kakannina suka yi, duk sa’ad da nake tunawa da kai a cikin addu’ata ba fāsawa.
4 Sa’ad da nake tunawa da hawayenka, nakan yi began ganinka dare da rana, domin in yi farin ciki matuƙa.
5 Ina tunawa da sahihiyar bangaskiyarka, wadda da farko take tare da kakarka Loyis, da mahaifiyarka Afiniki, a yanzu kuma na tabbata tana tare da kai.
6 Saboda haka, ina so in faɗakar da kai, ka lura baiwar nan ta Allah, wadda take tare da kai ta wurin ɗora maka hannuwana.
7 Ai, Allah ba halin tsoro ya ba mu ba, hali mai ƙarfi ne, mai ƙauna, da kuma kamunkai.
8 Saboda haka, kada ka ji kunyar ba da shaidar Ubangijinmu, da kuma tawa, ni da nake ɗan sarƙa saboda shi, sai dai mu jure wa shan wuya tare, saboda bishara, bisa ga ikon Allah,
9 wanda ya cece mu, ya kuma kira mu da kira mai tsarki, ba don wani aikin lada da muka yi ba, sai dai domin nufinsa, da kuma alherinsa, da aka yi mana baiwa tun fil’azal, a cikin Almasihu Yesu,
10 wadda a yanzu aka bayyana ta bayyanar Mai Cetonmu Almasihu Yesu, wanda ya shafe mutuwa, ya kuma bayyana rai da rashin mutuwa, ta wurin bishara.
11 A wannan bishara an sa ni mai wa’azi, da kuma manzonta, da mai koyarwarta kuma.
12 Saboda haka, ne nake shan wuya haka. Duk da haka, ban kunyata ba, domin na san wanda na gaskata da shi, na kuma tabbata yana da iko ya kiyaye abin da na danƙa masa, har ya zuwa waccan rana.
13 Ka yi koyi da sahihiyar maganar da ka ji daga gare ni, da bangaskiya da ƙauna da take ga Almasihu Yesu.
14 Kyakkyawan abin nan da aka ba ka amana, ka kiyaye shi ta wurin Ruhu Mai Tsarki, wanda yake zaune a zuciyarmu.
15 Ka dai sani duk waɗanda suke ƙasar Asiya sun juya mini baya, a cikinsu kuwa har da Fijalas da kuma Harmajanas.
16 Ubangiji yă yi wa iyalin Onisifaras jinƙai, don sau da yawa yake sanyaya mini zuciya, bai kuwa ji kunyar ɗaurina da aka yi ba.
17 Har ma da ya zo Roma, sai ya neme ni ido a rufe, ya kuwa same ni.
18 Ubangiji ya yi masa jinƙai a waccan rana. Ka dai sani sarai yadda ya yi ɗawainiya mai yawa a Afisa.