1 To, a Ikkilisiyar da take Antakiya akwai waɗansu annabawa, da masu koyarwa, wato Barnaba, da Saminu wanda ake kira Baƙi, da Lukiyas Bakurane, da Manayan wanda aka goya tare da sarki Hirudus, da kuma Shawulu.
2 Sa’ad da suke yi wa Ubangiji ibada, suna kuma yin azumi, Ruhu Mai Tsarki ya ce, “Sai ku keɓe mini Barnaba da Shawulu domin aikin da na kira su a kai.”
3 Bayan kuma sun yi azumi, sun kuma yi addu’a, sai suka ɗora musu hannu, suka sallame su.
Manzanni Sun Yi Wa’azi a Kubrus
4 Su kuwa, da Ruhu Mai Tsarki ya aike su, suka tafi Salukiya, daga can kuma suka shiga jirgin ruwa sai tsibirin Kubrus.
5 Da suka kai Salamis, suka sanar da Maganar Allah a majami’un Yahudawa, ga kuma Yahaya na taimakonsu.
6 Bayan sun zazzaga tsibirin duka har Bafusa, suka iske wani mai sihiri, annabin ƙarya, Bayahude, mai suna Bar-yashu’a,
7 Wanda yake tare da muƙaddas Sarjiyas Bulus, mutum mai basira. Sai muƙaddashin ya kira Barnaba da Shawulu ya nemi jin Maganar Allah.
8 Amma Alimas mai sihirin nan, (don wannan ita ce ma’anar sunansa), ya mūsa musu, yana neman bauɗar da muƙaddashin nan daga bangaskiya.
9 Shawulu kuwa, wanda kuma ake kira Bulus, cike da Ruhu Mai Tsarki, ya zuba masa ido,
10 ya ce, “Kai babban maha’inci, munafiƙi, ɗan Iblis, magabcin adalci duka, ba za ka daina karkata miƙaƙƙun hanyoyin Ubangiji ba?
11 To, ga shi, hannun Ubangiji na kanka, za ka makance, ba za ka ga rana ba har wani lokaci.” A nan take kuwa sai wani hazo da duhu suka rufe shi, ya yi ta neman wanda zai yi masa jagora.
12 Da muƙaddashin ya ga abin da ya faru, sai ya ba da gaskiya, yana mamaki da koyarwar Ubangiji.
Bulus da Barnaba a Antakiya ta Bisidiya
13 Sai Bulus da abokan tafiyarsa suka tashi daga Bafusa a jirgin ruwa, suka isa Bariyata ta ƙasar Bamfiliya. Yahaya kuwa ya bar su, ya koma Urushalima.
14 Amma suka wuce gaba daga Bariyata, suka tafi Antakiya ta ƙasar Bisidiya. Ran Asabar kuma sai suka shiga majami’a suka zauna.
15 Bayan an yi karatun Attaura da littattafan annabawa, shugabannin majami’ar suka aika musu, suka ce, “’Yan’uwa, in kuna da wata maganar gargaɗi da za ku yi wa jama’a, ai, sai ku yi.”
16 Sai Bulus ya miƙe, ya ɗaga hannu a yi shiru, ya ce,
“Ya ku ‘yan’uwa Isra’ilawa, da sauran masu tsoron Allah, ku saurara!
17 Allahn jama’ar nan Isra’ila ya zaɓi kakanninmu, ya ɗaukaka jama’ar sa’ad da suke baƙunci a ƙasar Masar, da maɗaukakin iko kuma ya fito da su daga cikinta.
18 Wajen shekara arba’in yake haƙuri da su cikin jeji.
19 Ya kuma hallaka al’umma bakwai a ƙasar Kan’ana, sai ya raba musu ƙasar tasu gādo, suka zauna har shekara arbaminya da hamsin.
20 Bayan haka kuma ya naɗa musu mahukunta har ya zuwa zamanin Annabi Sama’ila.
21 Sa’an nan suka roƙa a naɗa musu sarki, sai Allah ya ba su Saul ɗan Kish, mutumin kabilar Biliyaminu, har shekara arba’in.
22 Bayan da ya kawar da shi sai ya gabatar da Dawuda ya zama sarkinsu, ya kuma shaide shi da cewa, ‘Na sami Dawuda ɗan Yesse, mutum ne da nake ƙauna ƙwarai, wanda kuma zai aikata dukan nufina.’
23 Daga zuriyar mutumin nan ne Allah ya kawo wa Isra’ila Mai Ceto, Yesu kamar yadda ya yi alkawari.
24 Kafin ya bayyana a fili kuwa, Yahaya ya yi wa duk jama’ar Isra’ila wa’azi su tuba a kuma yi musu baftisma.
25 Yayin da Yahaya ya kusa gama nasa zamani, sai ya ce, ‘Wa kuke tsammani nake? Ba fa ni ne shi ɗin nan ba. Amma ga shi akwai wani mai zuwa a bayana, wanda ko takalmansa ma ban isa in balle ba.’
26 “Ya ku ‘yan’uwa, zuriyar Ibrahim, da kuma sauran masu tsoron Allah a cikinku, mu fa aka aiko wa kalmar ceton nan.
27 Ga shi, mazaunan Urushalima da shugabanninsu ba su gane shi ba, sa’an nan kuma ba su fahimci maganar annabawa da ake karantawa kowace Asabar ba, har suka cika maganar nan ta annabawa, yayin da suka hukunta shi.
28 Ko da yake ba su same shi da wani laifin kisa ba, duk da haka suka roƙi Bilatus a kashe shi.
29 Da suka cikasa dukkan abin da aka rubuta game da shi, suka sauko da shi daga kan gungumen, suka sa shi a kabari.
30 Amma Allah ya tashe shi daga matattu.
31 Kwanaki da yawa kuwa yana bayyana ga waɗanda suka zo tare da shi Urushalima daga Galili, waɗanda a yanzu su ne shaidunsa ga jama’a.
32 Mu ma mun kawo muku albishir, cewa, alkawarin nan da Allah ya yi wa kakanninmu,
33 ya cika mana shi, mu zuriyarsu, da ya ta da Yesu daga matattu, yadda yake a rubuce a cikin Zabura ta biyu cewa,
‘Kai Ɗana ne,
Ni Ubanka ne yau.’
34 Game da ta da shi daga matattu da Allah ya yi, a kan cewa ba zai sāke komawa cikin halin ruɓa ba kuwa, ga abin da ya ce,
‘Zan yi muku tsattsarkar albarkar nan da na tabbatar wa Dawuda.’
35 Domin a wata Zabura ma ya ce,
‘Ba za ka yarda Mai Tsarkinka ya ruɓa ba.’
36 Dawuda kam, bayan da ya bauta wa mutanen zamaninsa bisa ga nufin Allah, ya yi barci, aka binne shi tare da kakanninsa, ya kuwa ruɓe.
37 Amma shi wannan da Allah ya tashe shi, bai ruɓa ba.
38 Saboda haka, ‘yan’uwa, sai ku sani albarkacin mutumin nan ne ake sanar da ku gafarar zunubanku.
39 Ta gare shi kuma, duk masu ba da gaskiya suka kuɓuta daga dukan abubuwan da ba dama Shari’ar Musa ta kuɓutar da ku.
40 Saboda haka sai ku mai da hankali, kada abin nan da littattafan annabawa suke faɗa ya aukar muku, wato
41 ‘Ga shi, ku masu rainako,
Za ku ruɗe don mamaki, ku shuɗe!
Domin zan yi wani aiki a zamaninku,
Aikin da ba yadda za a yi ku gaskata,
Ko da wani ya gaya muku.’ ”
42 Suna fita majami’a ke nan, sai mutane suka roƙe su su ƙara yi musu wannan magana a ran Asabar mai zuwa.
43 Da jama’a suka watse, Yahudawa da yawa, da kuma waɗanda suka shiga Yahudanci, masu ibada, suka bi Bulus da Barnaba. Su kuma suka yi musu magana, suna yi musu gargaɗi su zauna a cikin alherin Allah.
44 Da Asabar ta kewayo, kusan duk birnin, suka hallara su ji Maganar Allah.
45 Amma da Yahudawa suka ga taro masu yawa, suka yi kishi gaya, suka yi ta musun abubuwan da Bulus ya faɗa, suna zaginsa.
46 Sai Bulus da Barnaba suka yi magana gabagaɗi, suka ce, “Ku, ya wajaba a fara yi wa Maganar Allah, amma da yake kun ture ta, kun nuna ba ku cancanci samun rai madawwami ba, to, za mu juya ga al’ummai.
47 Domin haka ubangiji ya umarce mu, ya ce,
‘Na sa ka haske ga al’ummai,
Don ka zama sanadin ceto, har ya zuwa iyakar duniya.’ ”
48 Da al’ummai suka ji haka, suka yi farin ciki, suka ɗaukaka Maganar Ubangiji, ɗaukacin kuma waɗanda aka ƙaddara wa samun rai madawwami suka ba da gaskiya.
49 Maganar Ubangiji kuwa, sai ta yi ta yaɗuwa a duk ƙasar.
50 Amma Yahudawa suka zuga waɗansu mata masu ibada, masu daraja, da kuma waɗansu manyan gari, suka haddasa tsanani ga Bulus da Barnaba, suka kore su daga ƙasarsu.
51 Su kuwa suka karkaɗe ƙurar ƙafafunsu don shaida a kansu, suka tafi Ikoniya.
52 Amma kuwa masu bi suna farin ciki matuƙa, suna kuma a cike da Ruhu Mai Tsarki.