Bulus da Barnaba a Ikoniya
1 To, a Ikoniya suka shiga majami’ar Yahudawa tare, suka yi wa’azi, har mutane masu yawa, Yahudawa da al’ummai, suka ba da gaskiya.
2 Amma Yahudawa da suka ƙi bi, suka zuga al’ummai, suka ɓata tsakaninsu da ‘yan’uwa.
3 Sai Bulus da Barnaba suka daɗe a nan ƙwarai, suna wa’azi gabagaɗi bisa ga ikon Ubangiji, shi da ya shaida maganar alherinsa ta yarjin mu’ujizai da abubuwan al’ajabi ta hannunsu.
4 Amma mutanen birni suka rarrabu, waɗansu suka koma bayan Yahudawa, waɗansu kuma bayan manzannin.
5 Sa’ad da al’ummai da Yahudawa tare da shugabanninsu suka tasar wa manzannin, su wulakanta su, su jejjefe su da duwatsu,
6 suka sami labari, suka gudu zuwa biranen Likoniya wato Listira da Darba, da kuma kewayensu.
7 Nan suka yi ta yin bisharar.
An Jejjefi Bulus a Listira
8 To, a Listira akwai wani mutum a zaune, wanda ƙafafunsa ba su da ƙarfi, gurgu ne tun da aka haife shi, bai ma taɓa tafiya ba.
9 Yana sauraron wa’azin Bulus, sai Bulus ya zuba masa ido, da ya ga bangaskiyarsa ta isa a warkar da shi,
10 ya ɗaga murya ya ce, “Tashi, ka tsaya cir.” Sai wuf ya zabura, har ya yi tafiya.
11 Da taron suka ga abin da Bulus ya yi, suka ɗaga murya gaba ɗaya suna cewa da Likoniyanci, “Lalle, alloli sun sauko mana da siffar mutane!”
12 Sai suka ce Barnaba shi ne Zafsa, Bulus kuwa don shi ne shugaban magana, wai shi ne Hamisa.
13 Sai sarkin tsafin Zafsa, wanda ɗakin gunkinsa yake ƙofar gari, ya kawo bajimai da tutocin furanni ƙofar gari, yana son yin hadaya tare da jama’a.
14 Amma da manzannin nan, Barnaba da Bulus, suka ji haka, suka kyakketa tufafinsu, suka ruga cikin taron, suna ɗaga murya suna cewa,
15 “Don me kuke haka? Ai, mu ma ‘yan adam ne kamarku, mun dai kawo muku bishara ne, domin ku juya wa abubuwan banzan nan baya, ku juyo ga Allah Rayayye, wanda ya halicci sama, da ƙasa, teku, da kuma dukkan abin da yake a cikinsu.
16 Shi ne a zamanin dā, ya bar dukan al’ummai su yi yadda suka ga dama.
17 Duk da haka kuwa bai taɓa barin kansa, ba shaida ba, domin yana yin alheri, shi da yake yi muku ruwan sama, da damuna mai albarka, yana ƙosar da ku da abinci, yana kuma faranta muku rai.”
18 Duk da waɗannan maganganu da ƙyar suka hana jama’ar nan yin hadaya saboda su.
19 Amma waɗansu Yahudawa suka zo daga Antakiya da Ikoniya, da suka rarrashi taron, suka jejjefe Bulus suka ja shi bayan gari, suna zato ya mutu.
20 Amma da masu bi suka taru a kansa, sai ya tashi ya koma garin. Kashegari kuma ya tafi Darba tare da Barnaba.
21 Bayan sun yi bishara a wannan gari, sun kuma sami masu bi da yawa, suka koma Listira da Ikoniya, da kuma Antakiya,
22 suna ƙarfafa masu bi, suna yi musu gargaɗi su tsaya ga bangaskiya, suna cewa, sai da shan wuya mai yawa za mu shiga Mulkin Allah.
23 Bayan kuma sun zaɓar musu dattawa a kowace Ikkilisiya, game da addu’a da azumi, suka danƙa su ga Ubangiji, wanda dā ma suka gaskata da shi.
Komawa Antakiya ta Suriya
24 Da suka zazzaga ƙasar Bisidiya, suka isa ƙasar Bamfiliya.
25 Da kuma suka faɗi Maganar a Bariyata, suka tafi Ataliya.
26 Daga nan kuma suka shiga jirgin ruwa sai Antakiya, inda tun dā aka yi musu addu’a alherin Allah ya kiyaye su cikin aikin nan da yanzu suka gama.
27 Da suka iso, suka tara jama’ar Ikkilisiya suka ba da labarin dukan abin da Allah ya aikata ta wurinsu, da kuma yadda ya buɗe wa al’ummai ƙofar bangaskiya.
28 Sun kuwa jima a can tare da masu bi.