An Kai Ƙarar Bulus
1 Bayan kwana biyar sai babban firist, Hananiya, ya zo tare da waɗansu shugabanni, da kuma wani lauya, mai suna Tartulus, suka yi ƙarar Bulus a gaban mai mulki.
2 Da aka kirawo Tartulus, ya shiga kai ƙarar Bulus, ya ce, “Ya mafifici Filikus, tun da yake ta gare ka ne muke zaman lafiya ƙwarai, ta tsinkayarka ne kuma ake kyautata zaman jama’armu,
3 kullum muna yarda da haka ƙwarai a ko’ina, tare da godiya ba iyaka.
4 Amma don kada in gajiyad da kai, ina roƙonka a cikin nasiharka, ka saurari ɗan taƙaitaccen jawabinmu.
5 Mun tarar da mutumin nan fitinanne ne, yana ta da hargitsi tsakanin Yahudawa ko’ina a duniya, shi kuma ne turun ɗariƙar Nazarawa.
6 Har ma yana nema ya tozarta Haikali, amma muka kama shi. [Niyyarmu ce mu hukunta shi bisa ga shari’armu.
7 Amma shugaba Lisiyas ya zo ya ƙwace shi daga hannunmu ƙarfi da yaji,
8 ya yi umarni masu ƙararsa su zo a gabanka.] In kuwa ka tuhume shi da kanka, za ka iya tabbatarwa daga bakinsa duk ƙarar da muke tāsarwa.”
9 Yahudawa ma suka goyi bayan haka, suna tabbatarwa haka abin yake.
Hanzarin Bulus a gaban Filikus
10 Da mai mulki ya alamta wa Bulus ya yi magana, sai ya amsa ya ce, “Tun da na sani ka yi shekaru da yawa kana yi wa jama’ar nan shari’a, da farin ciki zan kawo hanzarina.
11 Ai, ka iya tabbatarwa, bai fi kwana goma sha biyu ba tun da na tafi Urushalima yin sujada.
12 Ba su kuwa taɓa samuna ina muhawwara da kowa ba, ko kuwa ta da husuma har mutane su taru a Haikali, ko a majami’u, ko kuwa a cikin birni.
13 Ba kuma za su iya tabbatar maka abin da yanzu suke ƙarata a kai ba.
14 Amma na yarda cewa, bisa ga hanyar nan da suke kira ‘Ɗariƙa’ nake bauta wa Allahn kakanninmu, nake kuma gaskata duk abin da yake a rubuce a cikin Attaura da kuma littattafan annabawa.
15 Ina sa zuciya ga Allah, yadda su waɗannan ma suke sawa, wato za a ta da matattu, masu adalci da marasa adalci duka.
16 Saboda haka, a kullum nake himma in kasance da lamiri marar abin zargi a wurin Allah da wurin mutane.
17 To, bayan ‘yan shekaru sai na je domin in kai gudunmawa ga jama’armu, in kuma yi sadaka.
18 Ina cikin yin haka sai suka same ni a tsarkake a Haikali, ba kuwa da wani taro ba, balle hargowa. Amma akwai waɗansu Yahudawa daga ƙasar Asiya–
19 su ne kuwa ya kamata su zo nan a gabanka su yi ƙarata, in suna da wata magana a game da ni.
20 Ko kuwa waɗannan mutane kansu su faɗi laifina da suka samu, sa’ad da na tsaya a gaban majalisa,
21 sai ko maganar nan ɗaya tak, da na ɗaga murya na faɗa, sa’ad da nake a tsaye a cikinsu, cewa, ‘Game da maganar tashin matattu ake yi mini shari’a a gabanku yau.’ ”
An Tsare Bulus
22 Filikus kuwa da yake yana da sahihin ilimi a game da wannan hanya ya dakatar da su, ya ce, “In shugaba Lisiyas ya iso, zan yanke muku shari’a.”
23 Ya kuma ba jarumi umarni ya tsare Bulus, amma ya sassauta masa, kada kuwa ya hana mutanensa zuwa wurinsa su kula da shi.
24 Bayan ‘yan kwanaki Filikus ya zo tare da matarsa, Durusila, wata Bayahudiya. Sai ya aika a zo da Bulus, ya kuwa saurare shi a kan maganar gaskatawa da Almasihu Yesu.
25 Bulus yana ba da bayani a kan adalci, da kamunkai, da kuma hukuncin nan mai zuwa, Filikus ya kaɗu, ya kāda baki ya ce, “Yanzu kam, sai ka koma. In na sami zarafi nā kira ka.”
26 Don yana sa rai Bulus zai ba shi kuɗi, shi ya sa ya yi ta kiransa a kai a kai, yana zance da shi.
27 Amma bayan shekara biyu sai Borkiyas Festas ya gāji Filikus. Filikus kuwa don neman farin jini a wurin Yahudawa, ya bar Bulus a ɗaure.