Hanzarin Bulus a gaban Agaribas
1 Daga nan, sai Agaribas ya ce wa Bulus, “An ba ka izinin yin magana.”
Sa’an nan fa Bulus ya ɗaga hannu, ya fara kawo hanzarinsa ya ce,
2 “Lalle na yi arziki, ya sarki Agaribas, da yake a gabanka ne zan kawo hanzarina yau a game da duk ƙarata da Yahudawa suka yi,
3 musamman da yake gwani ne kai ga sanin al’adun Yahudawa da maganganunsu. saboda haka, ina roƙonka ka saurare ni da haƙuri.
4 “Irin zaman da na yi tun daga ƙuruciyata, wato tun da farko, a cikin jama’armu da kuma a Urushalima har ya zuwa yau, sananne ne ga dukan Yahudawa.
5 Sun sani tun ainihi, in dai za su yarda su yi shaida, cewa lalle ni Bafarisiye ne bisa ga ɗariƙar nan da ta fi tsanani cikin addinin nan namu.
6 Ai, saboda na sa zuciya ga cikar alkawarin nan ne da Allah ya yi wa kakanninmu nake nan a tsaye a yi mini shari’a.
7 Alkwarin nan kuwa, shi ne wanda kabilanmu goma sha biyu suke himmantuwa ga bauta wa Allah dare da rana, suna sa zuciya su ga cikarsa. Saboda sa zuciyar nan kuma fa Yahudawa suke ƙarata, ya sarki!
8 Yaya cewa Allah yana ta da matattu sa’an nan, ya ƙi gaskatuwa a gare ku?
9 “To, ni kaina ma a dā na ga kamar wajibi ne in yi abubuwa da yawa, na gāba da sunan Yesu Banazare.
10 Na kuwa yi haka a Urushalima, har na sami izini daga manyan firstoci, na kulle tsarkaka da yawa a kurkuku. Har ma a lokacin da ake kashe su ina goyon bayan yin haka.
11 Na kuma sha gwada musu azaba a dukan majami’u, ina ƙoƙarin sa su yin saɓo. Don kuma tsananin fushi da su, sai da na fafare su har waɗansu garuruwa na ƙetaren iyaka, ina tsananta musu.”
Labarin Juyowar Bulus
12 “Cikin halin haka ne, ina tafiya Dimashƙu da izinin manyan firistoci da kuma saƙonsu,
13 da rana a tsaka a hanya, ya sarki, na ga wani haske ya bayyano daga sama, fiye da hasken rana, duk ya haskaka kewaye da ni da abokan tafiyata.
14 Da duk muka fāɗi, sai na ji wata murya tana ce mini da yahudanci, ‘Shawulu, Shawulu, don me kake tsananta mini? Da wuya a gare ka ka yi ta shuri bisa a kan tsini.’
15 Ni kuwa sai na ce, ‘Wane ne kai, ya Ubangiji?’ Sai Ubangiji ya ce, ‘Ni ne Yesu wanda kake tsananta wa.
16 Amma tashi ka miƙe tsaye, gama na bayyana a gare ka ne da wannan maƙasudi, wato in sa ka mai hidima, mashaidi kuma na abubuwan da ka gani a game da ni, da kuma abubuwa waɗanda zan bayyana maka a nan gaba.
17 Zan tsirar da kai daga jama’ar nan da kuma al’ummai, waɗanda zan aike ka a gare su,
18 domin ka buɗe musu ido, su juyo daga duhu zuwa haske, daga kuma mulkin Shaiɗan zuwa wurin Allah, domin su sami gafarar zunubai, da kuma gādo tare da dukan tsarkaka saboda sun gaskata da ni.’ ”
Shaidar Bulus a Gaban Yahudawa da Al’ummai
19 “Saboda haka, ya sarki Agaribas, ban ƙi biyayya ga wahayin nan da ya zo mini daga Sama ba.
20 Da fari, na yi wa mutanen Dimashƙu wa’azi, sa’an nan na yi a Urushalima da dukan kewayen ƙasar Yahudiya, sa’an nan kuma na yi wa al’ummai, cewa su tuba su juyo ga Allah, su kuma yi aikin da zai nuna tubarsu.
21 Saboda wannan dalili ne Yahudawa suka kama ni a Haikali, har suna neman kashe ni.
22 Da na sami taimakon Allah kuwa, ga ni a nan har yanzu, ina shaida wa babba da yaro, ba na faɗar kome sai abin da annabawa da Musa suka ce zai auku,
23 cewa dai lalle ne Almasihu yă sha wuya, shi ne kuma zai fara tashi daga matattu, ya sanar da jama’ar nan da al’ummai haske.”
Bulus Yana Fata Agaribas Ya Gaskata
24 Bulus na cikin kawo hanzarinsa, sai Festas ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Bulus, kai dai ruɗaɗɗe ne, yawan karatunka yana juya maka kai.”
25 Amma Bulus ya ce, “Ya mafifici Festas, ai, ban ruɗe ba, gaskiya nake faɗa, cikin natsuwa kuwa.
26 Ai, al’amarin nan sananne ne ga sarki, ina kuma masa magana gabagaɗi ne, gama na tabbata ba abin da ya kuɓuce wa hankalinsa cikin al’amarin nan, don wannan abu ba a ɓoye aka yi shi ba.
27 Ya sarki Agaribas, ka gaskata annabawa? Na dai sani ka gaskata.”
28 Sai Agaribas ya ce wa Bulus, “Wato a ɗan wannan taƙaitaccen lokaci kake nufin mai da ni Kirista?”
29 Bulus kuwa ya ce, “Ko a ɗan wannan, ko a mai yawa, ina fata ga Allah, ba kai kaɗai ba, har ma duk waɗanda suke saurarona a yau, su zama kamar yadda nake, sai dai banda sarƙar nan.”
30 Sai sarki ya tashi, haka kuma mai mulki da Barniki, da waɗanda suke a zaune tare da su.
31 Bayan sun keɓe waje ɗaya, suka yi shawara, suka ce, “Ai, mutumin nan bai yi wani abin da ya isa kisa ko ɗauri ba.”
32 Agaribas kuma ya ce wa Festas, “Ba don dai mutumin nan ya riga ya nemi ɗaukaka ƙararsa a gaban Kaisar ba, da sai a sake shi.”