Zaɓen Mutum Bakwai Masu Hidima
1 To, a kwanakin nan da yawan masu bi suke Ƙaruwa, sai Yahudawa masu jin Helenanci suka yi wa Ibraniyawa gunaguni domin bā a kula da matayensu waɗanda mazansu suka mutu, a wajen rabon gudunmawa a kowace rana.
2 Sai goma sha biyun nan suka kirawo duk jama’ar masu bi, suka ce, “Ai, bai kyautu ba mu mu bar wa’azin Maganar Allah, mu shagala a kan sha’anin abinci.
3 Saboda haka, ‘yan’uwa, sai ku zaɓi mutum bakwai daga cikinku, waɗanda ake yabawa, cike da Ruhu da kuma hikima, waɗanda za mu danƙa wa wannan aiki.
4 Mu kuwa sai mu nace da yin addu’a da kuma koyar da Maganar.”
5 Abin da suka faɗa kuwa ya ƙayatar da jama’a duka. Sai suka zaɓi Istifanas, mutumin da yake cike da bangaskiya da Ruhu Mai Tsarki, da Filibus, da Burokoras, da Nikanar, da Timan, da Barminas, da Nikolas mutumin Antakiya wanda dā ya shiga Yahudanci.
6 Waɗannan ne aka gabatar a gaban manzannin. Bayan sun yi addu’a kuma, suka ɗora musu hannu.
7 Maganar Allah kuwa sai ƙara haɓaka take yi, yawan masu bi kuma a birnin Urushalima sai ta ƙaruwa yake yi ƙwarai da gaske, firistoci masu yawan gaske kuma suka yi na’am da bangaskiyar nan.
An Kama Istifanas
8 To, Istifanas, cike da alheri da iko, ya yi ta yin manyan al’ajabai da mu’ujizai a cikin jama’a.
9 Sa’an nan waɗansu na majami’ar da ake kira majami’ar Libartinawa, wato Kuraniyawa da Iskandariyawa, da kuma waɗansu daga ƙasar Kilikiya da ta Asiya, suka tasar wa Istifanas da muhawwara.
10 Amma ko kaɗan ba dama su yi masa mūsu, domin ya yi magana da hikima, Ruhu na iza shi.
11 Sai suka zuga mutane a asirce, su kuwa suka ce, “Mun ji shi yana zagin Musa, yana saɓon Allah.”
12 Ta haka suka ta da hankalin jama’a, da shugabanni, da malaman Attaura, su kuma suka aukar masa, suka kama shi, suka kawo shi a gaban majalisa.
13 Sai suka gabatar da masu shaidar zur, suka ce, “Mutumin nan ba ya rabuwa da kushe tsattsarkan wurin nan, da kuma Attaura,
14 don mun ji shi yana cewa wai wannan Yesu Banazare zai rushe wurin nan, yă kuma sauya al’adun da Musa ya bar mana.”
15 Da duk waɗanda suke zaune a majalisar suka zura masa ido, suka ga fuska tasa kamar fuskar mala’ika take.