1 Shawulu kuwa yana goyon bayan kisan Istifanas.
Shawulu Ya Yi wa Ikkilisiya Ɓarna Ƙwarai
A ran nan kuwa wani babban tsanani ya auko wa Ikkilisiyar da take Urushalima. Duk aka warwatsa su a lardin Yahudiya da na Samariya, sai dai manzannin kawai.
2 Sai waɗansu mutane masu bautar Allah suka binne Istifanas, suka yi masa kuka ƙwarai.
3 Amma Shawulu ya yi ta yi wa Ikkilisiya ɓarna ƙwarai da gaske, yana shiga gida gida, yana jan mata da maza, yana jefa su a kurkuku.
An Yi Wa’azin Bishara a Samariya
4 To, waɗanda aka warwatsar nan kuwa, suka yi ta zazzagawa suna yin bishara.
5 Filibus ya tafi birnin Samariya, yana ta yi musu wa’azin Almasihu.
6 Da taron suka ji, suka kuma ga mu’ujizan da Filibus yake yi, da nufi ɗaya suka mai da hankali ga abin da ya faɗa.
7 Domin da yawa masu baƙaƙen aljannu suka rabu da su, aljannun kuwa na ta ihu. Shanyayyu da guragu da yawa kuma an warkar da su.
8 Saboda haka aka yi ta farin ciki a garin ƙwarai da gaske.
9 Akwai wani mutum kuwa, mai suna Saminu, wanda dā yake sihiri a birnin, har yana ba Samariyawa mamaki, yana cewa shi wani muhimmi ne.
10 Duk jama’a kuwa suka mai da hankali a gare shi, babba da yaro, suna cewa, “Mutumin nan, ai, ikon nan ne na Allah, da ake kira mai girma.”
11 Sai suka mai da hankali gare shi, don ya daɗe yana ta ba su al’ajabi da sihirinsa.
12 Amma da suka gaskata bisharar da Filibus ya yi a kan Mulkin Allah, da kuma sunan Yesu Almasihu, duka aka yi musu baftisma mata da maza.
13 Har Saminu da kansa ma ya ba da gaskiya, bayan an yi masa baftisma kuma ya manne wa Filibus. Ganin kuma ana yin mu’ujizai da manyan al’ajibai, ya yi mamaki ƙwarai.
14 To, da manzannin da suke Urushalima suka ji Samariyawa sun yi na’am da Maganar Allah, suka aika musu da Bitrus da Yahaya.
15 Su kuwa da suka iso, suka yi musu addu’a don su sami Ruhu Mai Tsarki,
16 domin bai sauko wa ko wannensu ba tukuna, sai dai kawai an yi musu baftisma ne da sunan Ubangiji Yesu.
17 Sai suka ɗora musu hannu, suka kuwa sami Ruhu Mai Tsarki.
18 To, da Saminu ya ga, ashe, ta ɗora hannun manzanni ne ake ba da Ruhun, sai ya miƙa musu kuɗi,
19 ya ce, “Ni ma ku ba ni wannan iko, don kowa na ɗora wa hannu, yă sami Ruhu Mai Tsarki.”
20 Amma Bitrus ya ce masa, “Ku hallaka, kai da kuɗinka, don ka zaci da kuɗi ne za ka sami baiwar Allah!
21 Ba ruwanka da wannan al’amari sam, don zuciyarka ba ɗaya take ba a gaban Allah.
22 Saboda haka sai ka tuba da wannan mugun aiki naka, ka roƙi Ubangiji ko a gafarta maka abin da ka riya a zuciyarka.
23 Domin na ga kai tushen ɗaci ne, kana kulle a cikin mugunta.”
24 Sai saminu ya amsa ya ce, “Ku roƙar mini Ubangiji kada ko ɗaya daga cikin abin da kuka faɗa ya aukar mini.”
25 To, bayan manzannin sun tabbatar da Maganar Ubangiji, sun faɗe ta, suka koma Urushalima, suna yin bishara a ƙauyukan Samariyawa da yawa.
Filibus da Mutumin Habasha
26 Sai wani mala’ikan Ubangiji ya ce wa Filibus, “Tashi, ka yi kudu, ka bi hanyar da ta fito daga Urushalima zuwa Gaza,” wato hanyar hamada.
27 Sai ya tashi ya tafi. Ga wani mutumin Habasha, wani bābā, mai babban matsayi a mulkin Kandakatu, sarauniyar Habasha, shi ne kuwa ma’ajinta, ya zo Urushalima ne yin sujada,
28 yana komawa gida a zaune a cikin keken dokinsa, yana karatun littafin Annabi Ishaya.
29 Sai Ruhu ya ce wa Filibus, “Matsa ka yi kusa da keken dokin nan.”
30 Sai Filibus ya yi gudu zuwa wurinsa, ya ji shi yana karatun littafin Annabi Ishaya. Ya ce, “Kana kuwa fahimtar abin da kake karantawa?”
31 Sai ya ce, “Ina fa? Sai ko wani ya fassara mini.” Sai ya roƙi Filibus ya hau su zauna tare.
32 Wannan kuwa shi ne nassin da yake karantawa, “An ja shi kamar tunkiya zuwa mayanka. Kamar yadda ɗan rago yake shiru a hannun mai sausayarsa, Haka, ko bakinsa bai buɗe ba.
33 An yi masa ƙasƙanci har an hana masa gaskiya tasa. Wa yake iya ba da labarin zamaninsa? Domin an katse ransa daga duniya.”
34 Sai bābān ya ce wa Filibus, “Shin kam, annabin nan, maganar wa yake yi? Tasa ko ta wani?”
35 Sai Filibus ya buɗe baki ya fara da wannan Nassi, yana yi masa bisharar Yesu.
36 Suna cikin tafiya, suka iso wani ruwa, sai bābān ya ce, “Ka ga ruwa! Me zai hana a yi mini baftisma?”
37 Filibus ya ce, “In dai ka ba da gaskiya da zuciya ɗaya, ai, sai a yi maka.” Bābān ya amsa ya ce, “Na gaskata Yesu Almasihu ɗan Allah ne.”
38 Sai ya yi umarni a tsai da keken dokin. Sai dukansu biyu suka gangara cikin ruwan, Filibus da bābān, ya yi masa baftisma.
39 Da suka fito daga ruwan, Ruhun Ubangiji ya fauce Filibus, bābān kuma bai ƙara ganinsa ba. Sai ya yi ta tafiya tasa yana farin ciki.
40 Amma aka ga Filibus a Azotus. Sai ya zaga dukan garuruwa, yana yin bishara, har ya isa Kaisariya.