Juyowar Shawulu
1 Shawulu kuwa yana kan tsananta kashedi da gāba da masu bin Ubangiji, cewa zai kashe su, sai ya je wurin babban firist,
2 ya roƙe shi ya yi masa wasiƙu zuwa majami’un Dimashƙu, don in ya sami masu bin wannan hanya, mata ko maza, yă zo da su birnin Urushalima a ɗaure.
3 Yana tafiya ke nan, ya yi kusa da Dimashƙu, ba zato sai ga wani haske daga sama ya haskaka kewaye da shi.
4 Sai ya fāɗi, ya kuma ji wata murya tana ce masa, “Shawulu, Shawulu, don me kake tsananta mini?”
5 Shi kuma ya ce, “Wane ne kai, ya Ubangiji?” Sai ya ce, “Ni ne Yesu wanda kake tsananta wa.
6 Amma ka tashi ka shiga gari, can za a faɗa maka abin da za ka yi.”
7 Abokan tafiyarsa kuwa suka rasa bakin magana, suna jin muryar, amma ba su ga kowa ba.
8 Sai Shawulu ya tashi, amma da ya buɗe ido ya kasa gani. Sai aka yi masa jagora, aka kai shi Dimashƙu.
9 Kwanansa uku ba ya gani, ba ya kuma ci, ba ya sha.
10 To, akwai wani mai bi a Dimashƙu, mai suna Hananiya. Ubangiji ya yi masa magana cikin wahayi ya ce, “Hananiya.” Shi kuwa ya ce, “Na’am, ya Ubangiji.”
11 Sai Ubangiji ya ce masa, “Tashi ka tafi titin nan da ake kira Miƙaƙƙiye, ka tambaya a gidan Yahuza, ko akwai wani mutumin Tarsus, mai suna Shawulu, ga shi nan, yana addu’a,
12 har ma a cikin wahayi ya ga wani mutum, mai suna Hananiya, ya shigo ya ɗora masa hannu, don ya sāke samun ganin gari.”
13 Amma Hananiya ya amsa ya ce, “Ya Ubangiji, na sha jin labarin mutumin nan gun mutane da yawa, kan yawan muguntar da ya yi wa tsarkakanka a Urushalima.
14 Ga shi kuma manyan firistoci sun ba shi izini ya ɗaure duk mai yin addu’a da sunan har a nan ma.”
15 Amma Ubangiji ya ce masa, “Kai dai, je ka, domin shi ma’aikacina ne zaɓaɓɓe, domin yă sanar da sunana ga al’ummai, da sarakuna, da kuma Isra’ilawa.
16 Domin zan sanar da shi yawan wuyar da lalle zai sha saboda sunana.”
17 Sai Hananiya ya tafi, ya shiga gidan. Da ya ɗora masa hannu, ya ce, “Ya ɗan’uwana Shawulu, Ubangiji ne ya aiko ni, wato Yesu, wanda ya bayyana a gare ka a kan hanyar da ka biyo, domin ka sāke gani, a kuma cika ka da Ruhu Mai Tsarki.”
18 Nan take sai wani abu kamar ɓawo ya faɗo daga idanunsa, sai ya sāke gani. Sa’an nan ya tashi, aka yi masa baftisma.
19 Sai ya ci abinci, ƙarfinsa kuma ya komo.
Shawulu Ya Yi Wa’azi a Dimashƙu
Shawulu kuwa ya yi ‘yan kwanaki tare da masu bi da suke Dimashƙu.
20 Nan da nan ya fara wa’azin Yesu a majami’unsu, cewa shi ne Ɗan Allah.
21 Duk waɗanda suka ji shi, suka yi ta al’ajabi, suka ce, “Ashe, ba wannan ne ya watsa masu yin addu’a da sunan nan a Urushalima ba? Ya zo nan ne ma da niyyar ya kai su gaban manyan firistoci a ɗaure.”
22 Sai Shawulu ya ƙara ƙarfafa, yana ta dama hankalin Yahudawan da suke zaune a Dimashƙu, yana tabbatarwa, cewa Yesu shi ne Almasihu.
Shawulu Ya Kuɓuce wa Yahudawa
23 Bayan an ɗan daɗe Yahudawa suka ƙulla shawara su kashe shi.
24 Amma Shawulu ya sami labarin makircinsu. Dare da rana suna fako a ƙofofin gari don su kashe shi,
25 amma da daddare almajiransa suka tafi da shi, suka zura shi ta wata taga a jikin garu cikin babban kwando.
Shawulu a Urushalima
26 Da ya zo Urushalima ya yi ƙoƙarin shiga cikin masu bi, amma duk suka ji tsoronsa, don ba su gaskata shi mai bi ba ne.
27 Amma Barnaba ya kama hannunsa ya kai shi wurin manzannin, ya gaya musu yadda Shawulu ya ga Ubangiji a hanya, da yadda Ubangiji ya yi masa magana, da kuma yadda ya yi wa’azi gabagaɗi da sunan Yesu a Dimashƙu.
28 Daga nan ya yi ta cuɗanya da su a Urushalima,
29 yana wa’azi gabagaɗi da sunan Ubangiji. Ya kuma riƙa magana da Yahudawa masu jin Helenanci, yana muhawwara da su, amma suka yi ta neman kashe shi.
30 Da ‘yan’uwa suka fahimci haka, suka kawo shi Kaisariya, suka aika da shi Tarsus.
31 Sa’an nan ne Ikkilisiyar duk ƙasar Yahudiya, da ta Galili, da ta Samariya ta sami lafiya, ta ingantu sosai, suna tafiyar da al’amuransu da tsoron Ubangiji, Ruhu Mai Tsarki na taimakonsu, har suka yawaita.
An Warkar da Iniyasu
32 To, da Bitrus ya zazzaga lardi duka, sai kuma ya je wurin tsarkakan nan da suke zaune a Lidda.
33 Nan ya tarar da wani mutum, mai suna Iniyasu, wanda yake kwance a kan gado shekara takwas, yana shanyayye.
34 Sai Bitrus ya ce masa, “Iniyasu, Yesu Almasihu ya warkar da kai. Tashi ka kintsa gadonka.” A nan tāke ya tashi.
35 Duk mutanen Lidda da na ƙasar Sarona kuwa suka gan shi, suka juyo ga Ubangiji.
Bitrus Ya Ta Da Tabita daga Matattu
36 A Yafa kuwa akwai wata mai bi, mai suna Tabita, wato Dokas ke nan. Matar nan kuwa lazimar aiki nagari ce, da kuma gudunmawa.
37 A lokacin nan ta yi rashin lafiya, ta mutu. Da suka yi mata wanka, suka shimfiɗe ta a kan bene.
38 Da yake Lidda kusa da yafa take, da masu bi suka ji Bitrus na can, suka aiki mutum biyu wurinsa, su roƙe shi ya zo wurinsu ba da jinkiri ba.
39 Sai Bitrus ya tashi ya tafi tare da su. Da ya iso suka kai shi benen. Dukan mata waɗanda mazansu suka mutu suka tsaya kusa da shi, suna kuka, suna nunnuna riguna da tufafi da Dokas ta yi musu tun suna tare.
40 Amma Bitrus ya fitar da su duka waje, ya durƙusa, ya yi addu’a. Ya juya wajen gawar, ya ce, “Tabita, tashi.” Ta buɗe ido, da ta ga Bitrus, ta tashi zaune.
41 Ya kuwa miƙa mata hannu ya tashe ta. Sai ya kira tsarkaka da matan waɗanda mazansu suka mutu ya miƙa musu ita rayayyiya.
42 Labari ya bazu a dukan Yafa, mutane da yawa kuwa suka gaskata da Ubangiji.
43 To, ya zauna kwanaki da yawa a Yafa a gidan wani majemi mai suna Saminu.