AFI 5

Ku Yi Zaman Haske

1 Saboda haka sai ku zama masu koyi da Allah, in ku ƙaunatattun ‘ya’yansa ne.

2 Ku yi zaman ƙauna kamar yadda Almasihu ya ƙaunace mu, ya kuma ba da kansa dominmu, sadaka mai ƙanshi, hadaya kuma ga Allah.

3 Kada ma a ko ambaci fasikanci, da kowane irin aikin lalata ko kwaɗayi a tsakaninku, domin kuwa bai dace da tsarkaka ba.

4 Haka ma alfasha, da zancen banza da wauta, don bai kamata ba, sai dai a maimakon haka ku riƙa gode wa Allah.

5 Kun dai tabbata, ba wani fasiki, ko mai aikin lalata, ko mai kwaɗayi (wanda shi da mai bautar gumaka duk ɗaya ne), da yake da gādo a mulkin Almasihu da na Allah.

6 Kada wani ya hilace ku da maganar wofi, gama sabili da waɗannan zunubai ne fushin Allah yake aukawa a kan kangararru.

7 Saboda haka, kada ku yi cuɗanya da su,

8 domin dā ku duhu ne, amma a yanzu ku haske ne a cikin Ubangiji. Ku yi zaman mutanen haske,

9 domin haske shi ne yake haifar duk abin da yake nagari, na adalci, da na gaskiya.

10 Ku dai tabbata abin zai gamshi Ubangiji.

11 Ku yi nesa da ayyukan duhu na banza da wofi, sai dai ku tona su.

12 Gama abin kunya ne a ma faɗi abubuwan da suke yi a asirce.

13 Duk abin da aka kawo a gaban haske a san ainihinsa, gama duk abin da aka san ainihinsa ya haskaka.

14 Saboda haka aka ce,

“Farka, ya kai mai barci, ka tashi daga matattu.

Almasihu kuwa zai haskaka ka.”

15 Saboda haka, sai ku mai da hankali ƙwarai ga zamanku, kada ku zama kamar marasa hikima, sai dai masu hikima.

16 Ku yi matuƙar amfani da lokaci don kwanaki mugaye ne.

17 Don haka kada ku zama marasa azanci, sai dai ku fahimci abin da yake nufin Ubangiji.

18 Kada kuma ku bugu da giya, hanyar masha’a ke nan. Sai dai ku cika da Ruhu,

19 kuna zance da junanku da kalmomin zabura, da waƙoƙin yabo, da waƙoƙi na ruhu, kuna raira waƙoƙi da zabura ga Ubangiji da yabo a zukatanku.

20 Kullum ku riƙa gode wa Allah Uba da sunan Ubangijinmu Yesu Almasihu a kan ko mene ne.

Maza da Mata

21 Ku bi juna saboda ganin girman Almasihu.

22 Ku matan aure, ku yi biyayya ga mazanku, Ubangiji ke nan kuke yi wa.

23 Don miji shi ne shugaban matarsa, kamar yadda Almasihu yake shugaban Ikkilisiya, wato, jikinsa, shi kansa kuma shi ne Mai Ceton jikin.

24 Kamar yadda Ikkilisiya take bin Almasihu, haka kuma mata su bi mazansu ta kowane hali.

25 Ku maza, ku ƙaunaci matanku kamar yadda Almasihu ya ƙaunaci ikkilisiya, har ya ba da kansa dominta,

26 domin ya miƙa ta ga Allah, tsarkakakkiya bayan da ya wanke ta da ruwa ta wurin Kalma,

27 domin shi kansa yă ba kansa Ikkilisiya da ɗaukakarta, ba tare da tabo ko tamoji ba, ko wani irin abu haka, tă dai zamo tsattsarka marar aibu.

28 Ta haka ya wajaba maza su ƙaunaci matansu, jikinsu ke nan suke yi wa. Ai, wanda ya ƙaunaci matarsa, ya ƙaunaci kansa ke nan.

29 Domin ba wanda ya taɓa ƙin jikinsa, sai dai ya rene shi, ya yi tattalinsa, kamar yadda Almasihu yake yi wa Ikkilisiya,

30 domin mu gaɓoɓin jikinsa ne.

31 “Saboda haka ne, mutum sai ya bar mahaifinsa da mahaifiyarsa, ya manne wa matarsa, su biyu su zama jiki guda.”

32 Wannan asiri muhimmi ne, ni kuwa ina nufin Almasihu ne da ikkilisiya.

33 Duk da haka dai, sai kowane ɗayanku ya ƙaunaci matarsa kamar kansa, ita matar kuwa ta yi wa mijinta ladabi.