AMOS 1

Horon Allah a kan Maƙwabtan Isra’ila

1 Ga zantuttukan Amos, ɗaya daga cikin makiyayan ƙauyen Tekowa. Allah ya bayyana wa Amos wannan saƙo, tun shekara biyu kafin girgizar duniya, a lokacin da Azariya yake sarautar Yahuza, Yerobowam ɗan Yehowash kuwa yake sarautar Isra’ila.

2 Amos ya ce,

“Ubangiji zai yi ruri daga Sihiyona,

Muryarsa za ta yi tsawa daga

Urushalima.

Da jin wannan, sai wuraren kiwo za

su bushe,

Ƙwanƙolin Dutsen Karmel, da yake

kore zai yi yaushi.”

Suriya

3 Ubangiji ya ce,

“Mutanen Dimashƙu sun ci gaba da

yin zunubi.

Hakika, zan hukunta su,

Don sun zalunci mutanen Gileyad da

zalunci mai tsanani.

4 Don haka zan aukar da wuta a kan

fādar Sarkin Suriya.

Za ta ƙone kagarar Ben-hadad,

sarki.

5 Zan ragargaje ƙyamaren ƙofofin

birnin Dimashƙu,

In kawar da masu sarautar Bet-eden

da na kwarin Awen.

Za a kwashe mutanen Suriya ganima

zuwa ƙasar Kir.”

Filistiya

6 Ubangiji ya ce,

“Mutanen Gaza sun ci gaba da yin

zunubi.

Hakika, zan hukunta su,

Don sun kwashe al’umma duka, sun

sayar wa mutanen Edom.

7 Saboda haka zan aukar da wuta a

kan garun Gaza ta ƙone kagarar

birnin.

8 Zan kawar da masu sarautar biranen

Ashdod da Ashkelon,

Zan karɓe sandan mulkin Ekron.

Sauran Filistiyawa da suka ragu

kuma,

Za su mutu duka.”

Taya

9 Ubangiji ya ce,

“Mutanen Taya sun ci gaba da yin

zunubi.

Hakika, zan hukunta su,

Don sun kwashe mutanen sun kai

ƙasar Edom.

Suka karya yarjejeniyar abuta wadda

suka yi.

10 Saboda haka zan aukar da wuta a

kan garun Taya,

Ta ƙone kagarar birnin.”

Edom

11 Ubangiji ya ce,

“Mutanen Edom sun ci gaba da yin

zunubi.

Hakika, zan hukunta su,

Don sun farauci ‘yan’uwansu,

Isra’ilawa,

Suka ƙi su nuna musu jinƙai.

Ba su yarda su huce daga fushinsu

ba.

12 Saboda haka zan aukar da wuta a

kan Teman,

Ta ƙone kagarar Bozara.”

Ammon

13 Ubangiji ya ce,

“Mutanen Ammon sun ci gaba da yin

zunubi.

Hakika, zan hukunta su,

Don haɗamarsu ta ƙasa,

Suka tsaga mata masu ciki a

Gileyad.

14 Saboda haka zan aukar da wuta a

kan garun Rabba,

Ta ƙone kagarar birnin.

Za a yi kururuwa a ranar yaƙi,

Faɗan kuwa zai yi rugugi kamar

hadiri.

15 Sarkinsu da manyan mutanensu za a

kai su wata ƙasa dabam.”