1 Ku kasa kunne ga wannan, ya ku
matan Samariya,
Ku da kuka yi ƙiba kamar
turkakkun shanu,
Ku da kuke wulakanta kasassu,
Kuna yi wa matalauta danniya,
Kukan umarci mazajenku,
Ku ce, “Kawo mini abin sha!”
2 Da yake Ubangiji Mai Tsarki ne
Ya riga ya yi alkawari,
Ya ce, “Hakika kwanaki za su zo
Da za a jawo ku da ƙugiyoyi,
Kowannenku zai zama kamar kifi a
ƙugiya.
3 Za a kwashe ku, a fitar da ku
Ta inda garu ya tsage na mafi kusa
duka, a jefar.”
Isra’ila Sun Kāsa Koyo
4 Ubangiji ya ce,
“Jama’ar Isra’ila,
Ku tafi Betel, tsattsarkan wuri,
Ku yi ta zunubi!
Ku tafi Gilgal ku ƙara zunubi!
Ku yi ta kawo dabbobi sadaka
kowace safiya.
A kowace rana ta uku
Ku yi ta ba da zaka.
5 Ku miƙa abincinku hadaya ta
godiya.
Ku yi ta yin fariya da hadayarku ta
yardar rai!
Gama irin abin da kuke jin daɗin yi
ke nan.”
6 Ubangiji ya ce,
“Ai, ni ne, na sa a yi yunwa a
biranenku.
Shi ya sa ba ku da abinci.
Duk da haka ba ku juyo gare ni ba.
7 Na hana wa shuke-shukenku ruwa
A lokacin da suka fi bukata.
Na sa a yi ruwa a wani birni,
A wani birni kuwa na hana,
Wata gonar ta sami ruwan sama,
Amma wadda ba ta samu ba ta
bushe.
8 Ƙishirwa ta sa jama’a su tafke har
birane biyu ko uku
Suka tafi neman ruwa a birnin da
suke maƙwabtaka da shi,
A nan ma ba su sami isasshen ruwan
sha ba,
Duk da haka ba ku komo wurina
ba.
9 “Na sa darɓa, da domana
Su lalatar da amfanin gonakinku.
Fāra kuma ta cinye lambunanku
Da gonakin inabinku, da itatuwan
ɓaurenku,
Da na zaitun ɗinku.
Duk da haka ba ku komo wurina ba.
10 “Na aukar muku da annoba irin
wadda na aukar wa Masar.
Na karkashe samarinku a wurin
yaƙi,
Na kwashe dawakanku.
Na cika hancinku da ɗoyin
sansaninku.
Duk da haka ba ku komo wurina ba.
11 “Na hallakar da waɗansunku
Kamar yadda na hallakar da Saduma
da Gwamrata.
Kamar sanda kuke, wanda aka fizge
daga wuta.
Duk da haka ba ku komo wurina
ba.
12 Saboda haka, jama’ar Isra’ila,
Ga abin da zan yi muku,
Zan kuwa yi shi duk,
Sai ku yi shirin zuwa gaban
Ubangiji.”
13 Allah ne ya yi duwatsu
Ya kuma halicci iska.
Ya sanar da nufinsa ga mutum,
Ya juya rana ta zama dare.
Yana sarautar duniya duka.
Sunansa kuwa Ubangiji Maɗaukaki!