Darajar Sabon Haikalin
1 A rana ta ashirin da ɗaya ga watan bakwai sai Ubangiji ya yi magana da annabi Haggai ya ce,
2 “Ka yi magana da Zarubabel ɗan Sheyaltiyel, mai mulkin Yahuza, da Yoshuwa ɗan Yehozadak, babban firist, da dukan sauran mutane, ka ce,
3 ‘Wa ya ragu a cikinku da ya ga wannan Haikali da darajarsa ta dā? Ƙaƙa kuke ganinsa yanzu? A ganinku ba a bakin kome yake ba?
4 Duk da haka yanzu sai ku yi ƙarfin hali, kai Zarubabel, da kai Yoshuwa ɗan Yehozadak, babban firist, da dukanku mutanen ƙasar, ku kama aikin, gama ina tare da ku. Ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.
5 Na yi muku alkawari a sa’ad da kuka fito daga Masar, cewa Ruhuna zai zauna tare da ku, haka yake yanzu, kada ku ji tsoro!’
6 “Ni Ubangiji Mai Runduna, ina cewa ba da jimawa ba, zan girgiza sammai, da duniya, da teku, da sandararriya ƙasa.
7 Zan kuma girgiza al’umman duniya duka don dukiyar al’umman duniya ta samu. Zan kuwa cika Haikalin nan da daraja.
8 Azurfa tawa ce, zinariya kuma tawa ce. Ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.
9 Darajar Haikalin nan ta nan gaba za ta fi ta dā. A wannan wuri zan ba da salama. Ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.”
An Tsauta wa Mutane saboda Rashin Amincinsu
10 A rana ta ashirin da huɗu ga watan tara a shekara ta biyu ta sarautar Dariyus, Ubangiji kuma ya yi magana da annabi Haggai ya ce,
11 “Ka tambayi firistoci a kan wannan doka.
12 ‘Idan mutum yana riƙe da nama tsattsarka a rigarsa, idan rigar ta taɓa gurasa, ko dafaffen abinci, ko ruwan inabi, ko mai, ko kowane irin abinci, wannan zai sa abin ya tsarkaka?’ ”
Sai firistocin suka amsa suka ce, “A’a.”
13 Sai kuma Haggai ya ce, “Idan wanda ya ƙazantu ta wurin taɓa gawa, ya taɓa ɗaya daga cikin waɗannan abubuwa, wannan zai sa abin ya ƙazantu?”
Sai firistoci suka ce, “Wannan zai sa abin ya ƙazantu!”
14 Sai Haggai ya ce, “Ubangiji ya ce, ‘Haka yake da wannan jama’a da wannan al’umma da take gabana da kowane irin aikinsu. Abin da suke miƙawa kuma marar tsarki ne.
15 “ ‘Ina roƙonku, ku tuna a ran nan tun kafin a ɗora dutse a kan dutse na gina Haikalin Ubangiji, yaya kuke?
16 A lokacin, idan wani ya tafi wurin tsibin da zai auna mudu ashirin, sai ya iske mudu goma kawai. Idan kuma wani ya tafi wurin matse ruwan inabi don ya ɗebo mudu hamsin, sai ya tarar da mudu ashirin kawai.
17 Na aukar muku da burtuntuna, da fumfuna, da ƙanƙara a kan amfanin gonakinku, duk da haka ba ku komo wurina ba, ni Ubangiji na faɗa.
18 Yanzu ku tuna a ran nan, wato rana ta ashirin da huɗu ga watan tara, tun daga ranar da aka aza harsashin ginin Haikalin Ubangiji.
19 Ba sauran iri a rumbu. Kurangar inabi kuma, da itacen ɓaure, da rumman, da itacen zaitun ba su ba da amfani ba tukuna. Amma daga wannan rana zuwa gaba zan sa muku albarka.’ ”
Ubangiji Ya Yi wa Zarubabel Alkawari
20 Ubangiji kuma ya yi magana da Haggai a rana ta ashirin da huɗu ga watan, ya ce,
21 “Ka faɗa wa Zarubabel, mai mulkin Yahuza cewa, ‘Ina cikin shirin girgiza sammai da duniya.
22 Zan kuma hamɓare gadon sarautan daula, in kuma karya ƙarfin daular al’umman. Zan kuma hallaka karusai da mahayansu. Sojojin dawakai kuma za su kashe junansu da takuba.
23 A wannan rana, ni Ubangiji Mai Runduna, zan ɗauke ka, kai Zarubabel, bawana ɗan Sheyaltiyel, in maishe ka kamar zobe mai hatimi, gama na zaɓe ka, ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.’ ”