Fatawar Irmiya da Amsar Ubangiji
1 Ya Ubangiji, kai adali ne sa’ad da na kawo ƙara a gare ka.
Duk da haka zan bayyana ƙarata a
gabanka,
Me ya sa mugaye suke arziki cikin
harkarsu?
Me ya sa dukan maciya amana suke
zaman lafiya,
Suna kuwa ci gaba?
2 Kai ka dasa su, sun kuwa yi saiwa,
Suna girma, suna kuma ba da
‘ya’ya,
Sunanka na a cikin bakinsu, amma
kana nesa da zuciyarsu.
3 Amma kai, ya Ubangiji, kana sane da
ni, kana ganina,
Kai kanka kake gwada tunanina.
Ka jawo su kamar tumaki zuwa
mayanka,
Ka ware su domin ranar yanka.
4 Sai yaushe ƙasar za ta daina
makoki,
Ciyawar kowace saura kuma ta daina
yin yaushi?
Saboda muguntar mazaunan ƙasar
ne dabbobi da tsuntsaye suka
ƙare,
Domin mutanen suna cewa, “Ba zai
ga ƙarshenmu ba.”
5 Ubangiji ya ce,
“Idan kai da mutane kun yi tseren
ƙafa sun gajiyar da kai,
Yaya za ka iya gāsa da dawakai?
Idan ka fāɗi a lafiyayyiyar ƙasa,
Ƙaƙa za ka yi a kurmin Urdun?
6 Gama har da ‘yan’uwanka da gidan
mahaifinka,
Sun ci amanarka,
Suna binka da kuka,
Kada ka gaskata su,
Ko da yake suna faɗa maka
maganganu masu daɗi.”
7 Ubangiji ya ce,
“Na bar jama’ata.
Na rabu da gādona,
Na ba da wanda raina yake ƙauna a
hannun maƙiyansa.
8 Abin gādona ya zama mini kamar
zaki a cikin kurmi,
Ya ta da murya gāba da ni,
Domin haka na ƙi shi.
9 Ashe, abin gadon nan nawa ya zama
dabbare-dabbaren tsuntsun nan ne
mai cin nama?
Tsuntsaye masu cin nama sun kewaye
shi?
Tafi, ka tattaro namomin jeji,
Ka kawo su su ci.
10 Makiyaya da yawa sun lalatar da
gonar inabina.
Sun tattake nawa rabo,
Sun mai da nawa kyakkyawan rabo
kufai da hamada.
11 Sun maishe shi kufai, ba kowa,
Yana makoki a gare ni,
Ƙasar duka an maishe ta kufai,
Amma ba wanda zuciyarsa ta damu a
kan wannan.
12 A kan dukan tsaunukan nan na
hamada
Masu hallakarwa sun zo,
Gama takobin Ubangiji yana ta kisa
Daga wannan iyakar ƙasa zuwa
waccan,
Ba mahalukin da yake da salama.
13 Sun shuka alkama, sun girbe
ƙayayuwa,
Sun gajiyar da kansu, amma ba su
amfana da kome ba.
Za su sha kunya saboda abin da suke
girbe,
Saboda zafin fushin Ubangiji.”
14 Ga abin da Ubangiji ya faɗa a kan mugayen maƙwabtan Isra’ila waɗanda suka taɓa gādon da ya ba jama’arsa Isra’ila su gada. “Saboda haka zan tumɓuke su daga cikin ƙasarsu. Zan kuma tumɓuke mutanen Yahuza daga cikinsu.
15 Bayan na tumɓuke su kuma, zan sāke yi musu jinƙai, in komar da su, kowanne zuwa gādonsa.
16 Zai zama kuwa, idan za su himmantu su koyi al’amuran jama’ata, su yi rantsuwa da sunana, su ce, ‘Da zatin Ubangiji,’ kamar yadda suka koya wa jama’ata yin rantsuwa da Ba’al, sa’an nan za a gina su a tsakiyar jama’ata.
17 Amma idan wata al’umma za ta ƙi kasa kunne, to, sai in tumɓuke ta ɗungum, in hallaka ta, in ji Ubangiji.”