Fushin Ubangiji da Yahuza bai Huce Ba
1 Sai Ubangiji ya ce mini, “Ko da a ce Musa da Sama’ila za su tsaya a gabana, duk da haka zuciyata ba za ta komo wurin mutanen nan ba. Ka kore su daga gabana su yi tafiyarsu!
2 Sa’ad da suka tambaye ka, ‘Ina za mu tafi?’ Sai ka faɗa musu cewa, Ubangiji ya ce,
‘Waɗanda suke na annoba, su tafi ga
annoba!
Waɗanda suke na takobi, su tafi ga
takobi!
Waɗanda suke na yunwa, su tafi ga
yunwa!
Waɗanda suke na bauta, su tafi ga
bauta!’
3 Zan sa musu masu hallakarwa huɗu,” in ji Ubangiji, “da takobi don kisa, da karnuka don yayyagawa, da tsuntsayen sararin sama, da dabbobin duniya don su cinye, su hallakar.
4 Zan kuma sa su zama abin banƙyama ga dukan mulkokin duniya saboda abin da Manassa ɗan Hezekiya, Sarkin Yahuza ya aikata a Urushalima.
5 “Wa zai ji tausayinki, ya
Urushalima?
Wa zai yi baƙin ciki dominki?
Wa kuma zai ratso wurinki don ya
tambayi lafiyarki?
6 Ni Ubangiji na ce, kun ƙi ni, kuna ta
komawa da baya,
Don haka na nuna ikona gāba da ku,
na hallaka ku,
Na gaji da jin tausayinku!
7 Na sheƙe su da abin sheƙewa a
ƙofofin garuruwan ƙasar.
Na sa ‘ya’yansu su mutu, na hallaka
mutanena,
Ba su daina yin mugayen ayyukansu
ba.
8 Na yawaita gwauraye, wato mata da
mazansu suka mutu,
Fiye da yashin teku.
Na kawo wa uwayen samari mai
hallakarwa da tsakar rana.
Na sa azaba da razana su auka musu
farat ɗaya.
9 Ita wadda ta haifi ‘ya’ya bakwai ta
yi yaushi ta suma,
Ranarta ta faɗi tun lokaci bai yi ba,
An kunyatar da ita, an wulakantar
da ita.
Waɗanda suka ragu daga cikinsu
Zan bashe su ga takobi gaban abokan
gābansu.
Ni Ubangiji na faɗa.”
10 Kaitona, ya mahaifiyata, da kika haife ni, mai jayayya mai gardama da kowa cikin dukan ƙasar! Ban ba da rance ba, ba kuma wanda ya ba ni rance, duk da haka dukansu suna zagina.
11 Ubangiji ya ce mini, “Zan keɓe ka domin alheri, hakika zan sa abokan gaba su yi roƙo gare ka a lokacin bala’i da kuma lokacin damuwa.
12 Wa zai iya karya ƙarfe ko tagulla daga arewa?”
13 Ubangiji ya ce mini, “Zan ba da wadatarku da dukiyarku ganima kyauta, saboda dukan zunubanku a dukan ƙasar.
14 Zan sa ku bauta wa abokan gābanku a ƙasar da ba ku sani ba, gama fushina ya kama kamar wuta, zai yi ta ci har abada.”
15 Sa’an nan Irmiya ya ce, “Ya
Ubangiji, ka sani.
Kai ne, ka ziyarce ni,
Ka kuma sāka wa waɗanda suke
tsananta mini.
Ka sani saboda kai nake shan zargi.
16 Maganarka da na samu na ci.
Maganarka kuwa ta zama abar
murna a gare ni,
Ta faranta mini zuciya.
Gama ana kirana da sunanka,
Ya Ubangiji Allah Mai Runduna.
17 Ban zauna cikin ƙungiyar masu
annashuwa ba.
Ban kuwa yi murna ba,
Na zauna ni kaɗai saboda kana tare
da ni,
Gama ka sa na cika da haushi.
18 Me ya sa azabata ta ƙi ƙarewa,
Raunukana kuma ba su warkuwa,
Sun kuwa ƙi warkewa?
Za ka yaudare ni kamar rafi,
Ko kamar ruwa mai ƙafewa?”
19 “Domin haka ga abin da ni, Ubangiji
na ce,
Idan ka komo sa’an nan zan kawo
ka.
Za ka tsaya a gabana.
Idan ka hurta abin da yake gaskiya
ba na ƙarya ba,
Za ka zama kakakina.
Za su komo gare ka,
Amma kai ba za ka koma wurinsu
ba.
20 Zan maishe ka garun tagulla saboda
waɗannan mutane,
Za su yi yaƙi da kai, amma ba za
su yi nasara a kanka ba,
Gama ina tare da kai don in cece ka,
in kuɓutar da kai.
21 Zan kuɓutar da kai daga hannun
mugaye,
Zan ɓamɓare ka daga hannun
marasa tausayi.”