IRM 16

Umarnin Ubangiji zuwa ga Irmiya

1 Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce,

2 “Ba za ka yi aure ka haifi ‘ya’ya mata da maza a wannan wuri ba.

3 Ga abin da ni Ubangiji na faɗa a kan ‘ya’ya mata da maza da aka haifa a wannan wuri, da kuma a kan iyayensu mata da maza da suka haife su a wannan ƙasa,

4 za su mutu da muguwar cuta. Ba za a yi makoki dominsu ba, ba kuwa za a binne su ba. Za su zama juji. Takobi da yunwa za su kashe su, gawawwakinsu za su zama abincin tsuntsayen sararin sama da na namomin jeji.”

5 Ubangiji kuma ya ce, “Kada ka shiga gidan da ake makoki, ko ka tafi inda ake baƙin ciki, kada ka yi baƙin ciki saboda su, gama na ɗauke salamata, da ƙaunata, da jinƙaina daga wurin jama’an nan.

6 Yaro da babba za su mutu a wannan ƙasa, ba za a binne su ba, ba kuwa za a yi baƙin ciki dominsu ba. Ba kuwa wanda zai tsaga jikinsa ko ya aske kansa ƙwal dominsu.

7 Ba wanda zai ba mai makoki abinci don ya ta’azantar da shi saboda mamacin, ba kuma wanda zai ba shi abin sha don ya ta’azantar da shi saboda mahaifinsa ko mahaifiyarsa.

8 “Kada kuma ka shiga gidan da ake biki, ka zauna ka ci ka sha tare da su.

9 Gama ni Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra’ila, zan sa muryar murna, da ta farin ciki, da ta ango, da ta amarya, su ƙare a wurin nan a idonka da zamaninka.

10 “Sa’ad da ka faɗa wa mutanen nan wannan magana duka, za su kuwa ce maka, ‘Me ya sa Ubangiji ya hurta wannan babbar masifa a kanmu? Mene ne laifinmu? Wane irin zunubi muka yi wa Ubangiji Allahnmu?’

11 Sai ka faɗa musu cewa, Ubangiji ya ce, ‘Domin kakanninku sun rabu da ni, sun bi gumaka, sun bauta musu, sun yi musu sujada. Sun rabu da ni, sun ƙi kiyaye dokokina.

12 Ku kuma kun yi laifi fiye da na kakanninku. Kowannenku kuwa ya bi tattauran mugun nufin zuciyarsa, yana ƙin kasa kunne gare ni.

13 Don haka zan fitar da ku daga wannan ƙasa zuwa wata ƙasa wadda ku ko kakanninku ba ku sani ba. A can za ku bauta wa gumaka dare da rana, gama ba zan nuna muku ƙauna ba.’

14 “Saboda haka, ga shi, kwanaki suna zuwa,” in ji Ubangiji, “da ba za a ƙara cewa, ‘Na rantse da ran Ubangiji wanda ya fito da jama’ar Isra’ila daga ƙasar Masar ba.’

15 Amma za a ce, ‘Na rantse da Ubangiji wanda ya fito da jama’ar Isra’ila daga ƙasar arewa, da kuma daga dukan ƙasashe da ya kora su,’ gama zan komo da su zuwa ƙasar da na ba kakanninsu.

16 “Ga shi, ina aiko da masunta da yawa,” in ji Ubangiji, “za su kuwa kama su, daga baya kuma zan aika da mafarauta da yawa, za su farauce su daga kowane tsauni, da tudu, da kogwannin duwatsu.

17 Gama ina ganin dukan ayyukansu, ba a ɓoye suke a gare ni ba, muguntarsu kuma ba a ɓoye take a gare ni ba.

18 Zan riɓaɓɓanya sakayyar da zan yi musu saboda muguntarsu da zunubinsu, domin sun ƙazantar da ƙasata da ƙazantattun gumakansu marasa rai, abin gādona kuma sun cika shi da abubuwansu na banƙyama.”

Addu’ar Irmiya ta Dogara ga Allah

19 “Ya Ubangiji, ƙarfina da kagarata,

Mafakata a ranar wahala,

A gare ka al’ummai za su zo,

Daga ƙurewar duniya, su ce,

‘Kakanninmu ba su gāji kome ba, sai

ƙarya,

Da abubuwan banza marasa

amfani.’

20 Mutum zai iya yi wa kansa alloli?

Ai, waɗannan ba alloli ba ne!”

21 Ubangiji ya ce,

“Saboda haka, ga shi, zan sa su sani,

Sau ɗayan nan kaɗai zan sa su su san

ikona da ƙarfina,

Za su kuma sani sunana Ubangiji

ne.”