IRM 21

An Yi Faɗi a kan Faɗuwar Urushalima

1 Wannan ita ce maganar Ubangiji wadda ya faɗa wa Irmiya sa’ad da sarki Zadakiya ya aiki Fashur ɗan Malkiya, da Zafaniya firist, ɗan Ma’aseya, wurin Irmiya cewa,

2 “Ka tambayar mana Ubangiji, gama Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya kawo mana yaƙi. Ko Ubangiji zai yi mana al’amuran nan nasa masu ban al’ajabi kamar yadda ya saba, ya sa Sarkin Babila ya janye, ya rabu da mu?”

3 Sai Irmiya ya ce musu,

4 “Ku faɗa wa Zadakiya, Ubangiji Allah na Isra’ila ya ce, ‘Ga shi, zan juyo kayan yaƙin da suke hannunka waɗanda kake yaƙi da su gāba da Sarkin Babila, da sojojinsa, waɗanda suka kewaye garun birnin, zan kuwa tsiba kayan yaƙinka a tsakiyar birnin nan.

5 Ni kaina zan yi yaƙi da kai da dukan ƙarfina, da hasalata, da dukan zafin fushina.

6 Zan kuwa kashe mazaunan birnin nan, mutum da dabba, da babbar annoba.

7 Bayan wannan zan ceci Zadakiya Sarkin Yahuza, shi da bayinsa, da mutanen birnin nan waɗanda suka tsira daga annoba, da takobi, da yunwa, zan bashe su a hannun Nebukadnezzar Sarkin Babila, da hannun abokan gābansu, da waɗanda suke neman rayukansu. Zai kashe su da takobi, ba zai ji tausayinsu, ko ya rage waɗansunsu, ko ya ji juyayinsu ba.’

8 “Sai ka faɗa wa wannan jama’a, ka ce, ‘Ni Ubangiji na ce, ga shi, na sa tafarkin rai da na mutuwa a gabanku.

9 Shi wanda ya zauna a birnin nan zai mutu da takobi, da yunwa, da annoba, amma shi wanda ya fita ya ba da kansa ga Kaldiyawa waɗanda suke kewaye da ku zai rayu ya tserar da ransa.

10 Gama na ƙudura zan kawo wa wannan birni masifa, ba alheri ba. Zan bashe shi a hannun Sarkin Babila, shi kuwa zai ƙone shi da wuta.’ ”

Annabci a kan Sarakunan Yahuza

11 “Sai ka faɗa wa gidan sarautar Yahuza cewa, ‘Ku ji maganar Ubangiji,

12 Ya gidan Dawuda, ni Ubangiji na ce,

Ku aikata adalci kowace safiya.

Ku ceci wanda aka yi masa ƙwace

daga hannun mai matsa masa,

Don kada hasalata ta tashi kamar

wuta,

Ta yi ƙuna, har ba mai iya kashe

ta,

Saboda mugayen ayyukanku.

13 Ga shi, ina gāba da ku, ya ku

mazaunan kwarin,

Ya dutsen da yake a fili,’ in ji

Ubangiji.

‘Ku da kuke cewa, wa zai iya

gangarowa wurinku,

Ko kuwa wa zai shiga wurin

zamanku?

14 Zan hukunta ku bisa ga ayyukanku,’

in ji Ubangiji,

‘Zan sa wa jejin ƙasar wuta.

Za ta cinye duk abin da yake kewaye da

ita.’ ”