Biyayyar Rekabawa
1 A lokacin da Yehoyakim, ɗan Yosiya yake mulkin Yahuza, sai Ubangiji ya ce wa Irmiya,
2 “Ka tafi gidan Rekabawa, ka yi magana da su, ka kawo su a Haikalin Ubangiji, cikin ɗayan ɗakunan, sa’an nan ka ba su ruwan inabi su sha.”
3 Sai na ɗauki Yazaniya ɗan Irmiya, ɗan Habazziniya, da ‘yan’uwansa, da dukan ‘ya’yansa maza da dukan iyalin gidan Rekabawa.
4 Na kawo su cikin Haikalin Ubangiji, a ɗakin ‘ya’yan Hanan da Igdaliya, mutumin Allah. Ɗakin yana kusa da na shugabanni, a kan ɗakin Ma’aseya ɗan Shallum mai tsaron bakin ƙofa.
5 Sa’an nan na sa tuluna cike da ruwan inabi, da ƙoƙuna a gaban Rekabawa, sai na ce musu, “Ku sha ruwan inabi!”
6 Sai suka amsa, suka ce, “Ba za mu sha ruwan inabi ba, gama Yonadab ɗan Rekab, kakanmu, ya umarce mu cewa, ‘Ko ku, ko ‘ya’yanku, ba za ku sha ruwan inabi ba har abada,
7 ba kuma za ku gina ɗaki ba, ba kuwa za ku yi shuka ba, ba za ku yi dashe ba, ba za ku yi gonar inabi ba. Za ku zaune cikin alfarwai dukan kwanakin ranku, domin ku yi tsawon rai a ƙasar baƙuncinku.’
8 Mu kuma muka yi biyayya da umarnin da Yonadab ɗan Rekab, kakanmu, ya yi mana, cewa kada mu sha ruwan inabi, mu da matanmu, da ‘ya’yanmu mata da maza,
9 kada kuma mu gina wa kanmu gidajen zama. Ba mu da gonar inabi, ko gona ko iri.
10 Amma a alfarwai muke zamanmu. Mun yi biyayya da dukan abin da Yonadab kakanmu ya umarce mu.
11 Amma sa’ad da Nebukadnezzar Sarkin Babila ya kawo yaƙi a ƙasar, sai muka ce, ‘Bari mu tafi Urushalima domin muna jin tsoron sojojin Kaldiyawa da Suriyawa.’ Shi ya sa muke zaune a Urushalima.”
12 Sa’an nan Ubangiji ya yi magana da Irmiya ya ce,
13 “Haka ni Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra’ila, na faɗa, ka tafi ka faɗa wa mutanen Yahuza da mazaunan Urushalima cewa, ‘Ba za ku karɓi umarnina, ku kasa kunne ga maganata ba?’
14 Umarnin da Yonadab ɗan Rekab ya yi wa ‘ya’yansa, kada su sha ruwan inabi, sun kuwa kiyaye shi. Ba su taɓa shan ruwan inabi ba har wa yau, domin suna biyayya da umarnin kakansu. Ni kuwa na yi ta yi muku magana, amma ba ku kasa kunne gare ni ba.
15 Na yi ta aiko muku da bayina annabawa, ina cewa, kowa ya bar muguwar hanyarsa, ya gyara ayyukansa, kada ya bauta wa gumaka. Ta haka za ku zauna a ƙasa wadda na ba ku, ku da kakanninku, amma ba ku kasa kunne, ku ji ni ba.
16 ‘Ya’yan Yonadab ɗan Rekab sun kiyaye umarnin da kakansu ya yi musu. Amma jama’an nan ba su yi mini biyayya ba.
17 Domin haka, ni Ubangiji Allah Mai Runduna, Allah na Isra’ila, na ce zan kawo wa mutanen Yahuza da mazaunan Urushalima masifar da na ce zan kawo musu, domin na yi musu magana, ba su ji ba, na kira su, ba su amsa ba.”
18 Sai Irmiya ya ce wa Rekabawa, “Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra’ila ya ce, ‘Tun da yake kun kiyaye dukan abin da Yonadab kakanku ya umarce ku,
19 saboda haka Yonadab ɗan Rekab ba zai taɓa rasa magaji wanda zai tsaya a gabana ba.’ ”