An Sa Irmiya a Kurkuku
1 Zadakiya ɗan Yosiya, wanda Nebukadnezzar, Sarkin Babila ya naɗa Sarkin Yahuza, ya yi mulki a maimakon Yekoniya ɗan Yehoyakim.
2 Amma shi da barorinsa, da mutanen ƙasar, ba wanda ya kasa kunne ga maganar Ubangiji wadda ya yi musu ta bakin annabi Irmiya.
3 Sai sarki Zadakiya ya aiki Yehukal ɗan Shelemiya, da Zafaniya firist, ɗan Ma’aseya, a wurin annabi Irmiya cewa, “Ka yi addu’a ga Ubangiji Allah dominmu.”
4 A lokacin nan Irmiya yana kai da kawowa a cikin mutane, gama ba a tsare shi a kurkuku ba tukuna.
5 Rundunar sojojin Fir’auna kuwa ta taho daga Masar, amma da Kaldiyawa waɗanda suka kewaye Urushalima da yaƙi suka ji labari, sai suka janye daga Urushalima.
6 Sai Ubangiji ya yi magana da annabi Irmiya, ya ce,
7 “Ni Ubangiji Allah na Isra’ila, na ce ka faɗa wa Sarkin Yahuza wanda ya aiko ka ka tambaye ni, ka faɗa masa cewa, ‘Rundunar sojojin Fir’auna, wadda ta kawo maka gudunmawa tana gab da juyawa zuwa ƙasarta a Masar.
8 Kaldiyawa kuwa za su komo su yi yaƙi da wannan birni. Za su ci birnin, su ƙone shi da wuta.
9 Ni Ubangiji, na ce kada ku ruɗi kanku da cewa Kaldiyawa ba za su dawo ba, gama ba shakka za su zo.
10 Ko da a ce za ku ci dukan rundunar sojojin Kaldiyawa wadda take yaƙi da ku, sauran waɗanda kuka yi wa rauni da suke kwance a alfarwai za su tashi su ƙone birnin da wuta.’ ”
11 Da rundunar sojojin Kaldiyawa ta janye daga Urushalima saboda zuwan rundunar sojojin Fir’auna,
12 sai Irmiya ya tashi daga Urushalima zai tafi can ƙasar Biliyaminu, don ya karɓi nasa rabo tare da dangi.
13 A sa’ad da ya isa Ƙofar Biliyaminu, shugaban matsara, Irija ɗan Shelemiya, ɗan Hananiya, ya kama annabi Irmiya ya ce, “Kai kana gudu zuwa wurin Kaldiyawa ne.”
14 Sai Irmiya ya ce, “Ƙarya ce, ni ba gudu zuwa wurin Kaldiyawa nake yi ba.” Amma Irija bai yarda ba, sai ya kai shi wurin shugabanni.
15 Shugabanni suka yi fushi da Irmiya, suka yi masa dūka, suka tsare shi a gidan Jonatan magatakarda, gama an mai da gidansa ya zama kurkuku.
16 Irmiya ya yi kwanaki da yawa can cikin kurkukun.
Zadakiya Ya Nemi Shawara ga Irmiya
17 Sarki Zadakiya ya aika a kawo masa Irmiya. Sarki kuwa ya shigar da shi gidansa, ya tambaye shi a asirce, ya ce, “Ko akwai wata magana daga wurin Ubangiji?”
Sai Irmiya ya ce, “Akwai kuwa!” Ya ci gaba ya ce, “Za a ba da kai a hannun Sarkin Babila.”
18 Sai kuma ya tambayi sarki Zadakiya ya ce, “Wane laifi na yi maka, ko barorinka, ko wannan jama’a da ka sa ni a kurkuku?
19 Ina annabawanku waɗanda suka yi maka annabci cewa, ‘Sarkin Babila ba zai kawo wa ƙasarku yaƙi ba?’
20 Yanzu ya maigirma sarki, ina roƙonka ka ji wannan roƙo da nake yi maka, kada ka mai da ni a gidan Jonatan magatakarda, domin kada in mutu a can.”
21 Sai sarki Zadakiya ya ba da umarni, suka sa Irmiya a gidan waƙafi. Aka riƙa ba shi malmalar abinci daga unguwar masu tuya kowace rana, har lokacin da abinci ya ƙare duka a birnin. Haka kuwa Irmiya ya zauna a gidan waƙafi.