Faɗuwar Urushalima
1 A watan goma a na shekara ta tara ta sarautar sarki Zadikiya, Sarkin Yahuza, sai Nebukadnezzar Sarkin Babila, da dukan sojojinsa suka zo, suka kewaye Urushalima da yaƙi.
2 A rana ta tara ga watan huɗu, a shekara ta goma sha ɗaya ta sarautar Zadakiya, sai aka huda garun birnin.
3 Sa’an nan da aka ci Urushalima, sai dukan sarakunan Sarkin Babila suka shiga, suka zauna a Ƙofar Tsakiya. Sarakuna, su ne Nergal-sharezer, da Samgar-nebo, da Sarsekim, wato Rabsaris, da Nergal-sharezer, wato Rabmag, da dukan sauran shugabannin Sarkin Babila.
4 Sa’ad da Zadakiya, Sarkin Yahuza, da dukan sojoji suka gan su, sai suka gudu, suka fita daga birnin da dare, ta hanyar gonar sarki a ƙofar da take a tsakanin garu biyu. Suka nufi zuwa wajen Araba.
5 Amma sojojin Kaldiyawa suka bi su, suka ci wa Zadakiya a filayen Yariko. Suka kama shi, suka kawo shi gaban Sarkin Babila a Ribla a ƙasar Hamat, a can Nebukadnezzar ya yanka masa hukunci.
6 Sarkin Babila ya kashe ‘ya’yan Zadakiya, maza, a Ribla a kan idon Zadakiya. Ya kashe dukan shugabannin Yahuza.
7 Ya kuma ƙwaƙule idanun Zadakiya, ya buga masa ƙuƙumi, ya kai shi Babila.
8 Sai Kaldiyawa suka ƙone gidan sarki, da gidajen jama’a. Suka kuma rushe garun Urushalima.
9 Sa’an nan Nebuzaradan shugaban matsara ya kwashi sauran mutane da suka ragu a birnin zuwa babila, wato mutanen da suka gudu zuwa wurinsa.
10 Amma ya bar matalauta waɗanda ba su da kome a ƙasar. Ya ba su gonakin inabi da waɗansu gonaki a ran nan.
Nebukadnezzar Ya Lura da Irmiya
11 Sai Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya yi wa Nebuzaradan shugaban matsara umarni a kan Irmiya ya ce,
12 “Ka ɗauke shi ka lura da shi da kyau, kada ka yi masa wani mugun abu, amma ka yi masa dukan abin da yake so.”
13 Sai Nebuzaradan shugaban matsara, da Nebushazban, wato Rabsaris, da Nergal-sharezer, wato Rabmag, da dukan shugabannin Sarkin Babila,
14 suka aika aka kawo Irmiya daga gidan waƙafi, suka ba da Irmiya amana ga Gedaliya, ɗan Ahikam ɗan Shafan, don ya kai shi gida. Da haka Irmiya ya zauna tare da mutane.
Ebed-melek yana Sa Zuciya ga Kuɓuta
15 Ubangiji ya yi magana da Irmiya a lokacin da aka kulle shi a gidan waƙafi, ya ce,
16 “Ka tafi ka faɗa wa Ebedmelek mutumin Habasha, cewa Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra’ila ya ce, ‘Zan sa masifa, ba alheri ba, ta auko wa wannan birni. Wannan kuwa zai faru a kan idanunka a wannan rana.
17 Amma a ranan nan, ni Ubangiji zan cece ka, ba za a ba da kai a hannun mutanen da kake jin tsoronsu ba.
18 Gama hakika zan cece ka, ba za ka mutu ta takobi ba. Za ka sami ranka kamar ganimar yaƙi, domin ka dogara gare ni, ni Ubangiji na faɗa.’ ”