1 Ubangiji ya ce,
“Ya mutanen Isra’ila, idan za ku
juyo ku komo wurina,
Idan kuka kawar da abubuwan
banƙyama daga gabana,
Kuka kuma bar yin shakka,
2 Idan kun yi rantsuwa kuka ce,
‘Har da ran Ubangiji kuwa,‘
Da gaskiya, da aminci, da adalci,
Sa’an nan sauran al’umma za su so
in sa musu albarka,
Za su kuma yabe ni.”
3 Ubangiji ya ce wa mutanen Yahuza da na Urushalima,
“Ku kafce saurukanku,
Kada ku yi shuka cikin ƙayayuwa.
4 Ya ku mutanen Yahuza da na
Urushalima,
Ku yi wa kanku kaciya domin
Ubangiji,
Ku kawar da loɓar zukatanku
Don kada fushina ya fito kamar
wuta,
Ya cinye, ba mai iya kashewa,
Saboda mugayen ayyukan da kuka
aikata.”
Yahuza tana cikin Barazanar Yaƙi
5 “Ku yi shela a cikin Yahuza,
Ku ta da murya a Urushalima, ku
ce,
‘Ku busa ƙaho a dukan ƙasar!’
Ku ta da murya da ƙarfi, ku ce,
‘Ku tattaru, mu shiga birane masu
garu.’
6 Ku ta da tuta wajen Sihiyona!
Ku sheƙa a guje neman mafaka,
kada ku tsaya!
Gama zan kawo masifa da babbar
halaka daga arewa.
7 Zaki ya hauro daga cikin
ruƙuƙinsa,
Mai hallaka al’ummai ya kama
hanya,
Ya fito daga wurin zamansa don ya
mai da ƙasarku kufai,
Ya lalatar da biranenku, su zama
kango, ba kowa.
8 Domin haka sai ku sa tufafin
makoki,
Ku yi makoki ku yi kuka,
Gama fushin Ubangiji bai rabu da
mu ba.”
9 Ubangiji ya ce, “A ranan nan, sarki da sarakuna, za su rasa ƙarfin hali, firistoci za su firgita, annabawa kuwa za su yi mamaki.”
10 Sai na ce, “Kaito, kaito, ya Ubangiji Allah, ka ruɗi jama’an nan da Urushalima, da ka ce musu, ‘Za ku zauna lafiya,’ amma ga shi, takobi zai sassare su.”
11 Lokaci yana zuwa da za a faɗa wa mutanen Urushalima cewa, “Iska mai zafi za ta huro daga tuddan hamada zuwa wajen jama’ata, ba domin a sheƙe ta ko a rairaye ta ba!
12 Wannan iska da za ta zo daga wurin Ubangiji, tana da mafificin ƙarfi. Yanzu fa zan yanke hukunci a kansu.”
Abokan Gāba sun Kewaye Yahuza da Yaƙi
13 Duba, ga abokin gāba yana zuwa
kamar gizagizai,
Karusan yaƙinsa suna kama da
guguwa,
Dawakansa sun fi gaggafa sauri.
Kaitonmu, mun shiga uku!
14 Ya Urushalima, ki wanke mugunta
daga zuciyarki,
Domin a cece ki,
Har yaushe mugayen tunaninki za su
yi ta zama a cikinki?
15 Gama wata murya daga Dan ta
faɗa,
Ta kuma yi shelar masifar da za ta
fito daga duwatsun Ifraimu.
16 “A faɗakar da al’ummai, yana zuwa,
A faɗa wa Urushalima cewa,
‘Masu kawo mata yaƙi suna zuwa
daga ƙasa mai nisa,
Suna yi wa biranen Yahuza ihu.
17 Za su kewaye Yahuza kamar masu
tsaron saura,
Saboda ta tayar wa Ubangiji.’ Ni
Ubangiji na faɗa.
18 “Al’amuranki da ayyukanki suka
jawo miki wannan halaka,
Tana da ɗaci kuwa,
Ta soki har can cikin zuciyarki.”
Irmiya ya yi Baƙin Ciki don Mutanensa
19 Azaba! Ba zan iya daurewa da azaba
ba!
Zuciyata! Gabana yana faɗuwa da
ƙarfi,
Ba zan iya yin shiru ba,
Gama na ji amon ƙaho da hargowar
yaƙi.
20 Bala’i a kan bala’i,
Ƙasa duka ta zama kufai,
An lalatar da alfarwaina, ba zato ba
tsammani,
Labulena kuwa farat ɗaya.
21 Har yaushe zan yi ta ganin tuta,
In yi ta jin amon ƙaho?
22 Ubangiji ya ce,
“Mutanena wawaye ne,
Ba su san ni ba,
Yara ne dakikai,
Ba su da ganewa.
Suna gwanance da aikin mugunta,
Amma ba su san yadda za su yi
nagarta ba.”
23 Da na duba duniya sai na ga kufai ce
kawai ba kome,
Na kuma dubi sammai sai na ga ba
haske.
24 Da na duba duwatsu, sai na ga suna
makyarkyata,
Dukan tuddai kuma suna rawar jiki,
su yi gaba su yi baya.
25 Na duba sai na ga ba ko mutum
ɗaya,
Dukan tsuntsaye kuma sun tsere.
26 Na duba, sai na ga ƙasa mai dausayi
ta zama hamada,
An mai da dukan biranenta
kangwaye
A gaban Ubangiji saboda zafin
fushinsa.
27 Gama Ubangiji ya ce, “Ƙasar duka za ta zama kufai, amma duk da haka, ba wannan ne zai zama ƙarshenta na har abada ba.
28 Duniya za ta yi makoki saboda
wannan,
Sammai za su duhunta,
Gama ni na faɗa, haka kuwa na nufa
in yi,
Ba zan ji tausayi ba,
Ba zan kuwa fāsa ba.”
29 Da jin motsin mahayan dawakai da
na maharba
Kowane gari zai fashe.
Waɗansu za su shiga kurama,
Waɗansu kuma su hau kan duwatsu.
Dukan birane za su fashe tas,
Ba wanda zai zauna a cikinsu.
30 Ya ke da kike kufai marar kowa,
Me kike nufi da kika ci ado da mulufi,
Kike caɓa ado da kayan zinariya,
Kika sa wa idanunki tozali ram?
Kin yi kwalliyarki a banza,
Abokan sha’anin karuwancinki sun
raina ki,
Ranki suke nema.
31 Na ji kuka kamar na mace wadda take
naƙuda,
Na ji nishi kamar na mace a lokacin
haihuwarta ta fari,
Na ji kukan ‘yar Sihiyona tana
kyakyari,
Tana miƙa hannuwanta tana cewa,
“Wayyo ni kaina, gama ina suma a
gaban masu kisankai!”