Jawabin Ubangiji zuwa ga Yahudawan da suke Masar
1 Ubangiji ya yi magana da Irmiya a kan dukan Yahudawan da suke zaune a ƙasar Masar, a garin Migdol, da Tafanes, da Memfis, da dukan ƙasar Fatros, ya ce,
2 “Ni Ubangiji Mai Runduna Allah na Isra’ila, na ce, ku da kanku kun ga masifar da na aukar wa Urushalima, da dukan garuruwan Yahuza. Yanzu sun zama kufai, ba wanda yake zaune a cikinsu,
3 domin mutanen da suke cikinsu sun aikata mugayen abubuwa da suka tsokane ni. Sun miƙa wa gumaka hadayu, suka kuma bauta musu, ko da yake su, ko ku, ko kakanninku, ba ku san su ba.
4 Na yi ta aika muku da dukan bayina annabawa waɗanda suka faɗa muku kada ku aikata wannan mugun abin banƙyama.
5 Amma ba su kasa kunne ba, ba su kuwa ji ba, da za su juyo daga mugayen ayyukansu na miƙa wa gumaka hadayu.
6 Saboda haka fushina ya yi zafi a kan garuruwan Yahuza da titunan Urushalima, don haka a yanzu sun lalace, suka zama kufai.
7 “Yanzu, ni Ubangiji Allah Mai Runduna, Allah na Isra’ila, ina tambaya, me ya sa kuke jawo wa kanku wannan babbar masifa, kuna so ku hallakar da mata da maza, yara da jarirai daga cikin Yahuza, har a rasa wanda zai wanzu?
8 Me ya sa kuke tsokanata da ayyukan hannuwanku, kuna miƙa wa gumaka hadayu a ƙasar Masar inda kuka zo don ku zauna? Yin haka zai sa a hallaka ku, ku zama abin la’ana da zargi a cikin dukan ƙasashen duniya.
9 Ko kun manta da mugayen ayyukan kakanninku, da na sarakunan Yahuza da na matansu, da naku, da na matanku, waɗanda suka aikata a ƙasar Yahuza da kan titunan Urushalima?
10 Amma har wa yau ba ku ƙasƙantar da kanku ba, ba ku ji tsorona ba, ba ku kuwa kiyaye dokokina da umarnaina ba, waɗanda na ba ku ku da kakanninku.
11 “Domin haka, ni Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra’ila, zan aukar muku da masifa, in hallaka mutanen Yahuza duka.
12 Sauran mutanen Yahuza kuwa waɗanda suka ragu, waɗanda suke niyyar zuwa ƙasar Masar da zama, zan sa dukansu su halaka a can. Takobi da yunwa za su kashe dukansu a Masar, da yaro da babba. Za su zama abin la’antawa, da abin tausayi, da abin zargi, da abin kunya.
13 Zan hukunta dukan waɗanda suke zaune a Masar kamar yadda na hukunta wa Urushalima da takobi, da yunwa, da annoba.
14 Ba waɗansu daga cikin mutanen Yahuza da suka ragu, waɗanda suka zo Masar da zama, da za su tsere ko su rayu. Ba wani daga cikinsu da zai koma Yahuza inda suke marmarin komawa da zama, ba wanda zai koma, sai dai ‘yan gudun hijira.”
15 Sai dukan mazan da suka sani matansu sun miƙa wa gumaka hadayu, da dukan matan da suke tsaye a wurin, da dukan Yahudawan da suke zaune a Fatros, babban taron jama’a, suka ce wa Irmiya,
16 “Ba za mu kasa kunne ga jawabin da kake yi mana da sunan Ubangiji ba!
17 Za mu aikata dukan abin da muka faɗa. Za mu miƙa wa gunkiyan nan, wato sarauniyar sama, hadayu, da hadayu na sha kamar yadda kakanninmu, da shugabanninmu suka yi a garuruwan Yahuza, da kan titunan Urushalima. A lokacin kuwa muna da abinci a wadace, muka arzuta, ba wata wahala.
18 Amma tun da muka daina miƙa wa sarauniyar sama hadayu, da hadayu na sha, ba mu da kome, sai dai takobi da yunwa suke kashe mu.”
19 Mata kuma suka ce, “Sa’ad da muka toya waina ga siffar sarauniyar sama, muka miƙa mata hadayu, da hadayu na sha, ai, mazanmu sun goyi bayan abin da muka yi.”
20 Sa’an nan Irmiya ya ce wa dukan mutane, mata da maza, waɗanda suka ba shi irin amsan nan, ya ce,
21 “A kan turaren da ku da kakanninku, da sarakunanku, da shugabanninku, da mutanen ƙasar, kuka ƙona a garuruwan Yahuza da a titunan Urushalima, kuna tsammani Ubangiji bai san su ba, ko kuna tsammani ya manta?
22 Ubangiji ba zai yarda da mugayen ayyukanku ba, da ƙazantarku da kuka aikata, don haka ƙasarku a yau ta zama kufai ba mai zama a cikinta. Ta zama abin ƙyama da la’ana.
23 Saboda kun ƙona turare, kun yi wa Ubangiji zunubi, ba ku yi biyayya da muryarsa ba, ba ku kiyaye dokokinsa, da umarnansa, da sharuɗansa ba, shi ya sa wannan masifa ta auko muku a yau.”
24 Sai Irmiya ya ce wa dukan mutane duk da mata, “Ku ji maganar Ubangiji, dukanku mutanen Yahuza da suke a Masar.
25 Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra’ila, ya ce, ‘Ku da matanku kun faɗa da bakinku, kun kuma aikata da hannuwanku, cewa za ku aikata wa’adodin da kuka yi na ƙona turare, da miƙa hadayu na sha ga sarauniyar sama.’ To, sai ku tabbatar da wa’adodinku, ku cika su!
26 Domin haka ku ji maganar Ubangiji, dukanku mutanen Yahuza da yake zaune a ƙasar Masar. ‘Ni Ubangiji na rantse da sunana Maɗaukaki, cewa ba zan yarda kuma wani mutumin Yahuza da yake ƙasar Masar ya ambaci sunana da yin rantsuwa, cewa ya rantse da zatin Ubangiji ba.’
27 Ga shi, ina lura da su, ba domin alheri ba, amma domin in aukar musu da masifa. Takobi da yunwa za su hallaka dukan mutanen Yahuza waɗanda suke a ƙasar Masar.
28 ‘Yan kaɗan ne za su tsere wa takobi, za su kuwa koma daga ƙasar Masar zuwa ƙasar Yahuza. Sauran mutanen Yahuza da suka ragu, waɗanda suka zo Masar da zama, za su sani ko maganar wa za ta cika, tasu ko kuwa tawa.
29 Ni Ubangiji na ce, wannan zai zama muku alama, cewa zan hukunta ku a wannan wuri domin ku sani lalle maganata ta aukar muku da masifa za ta cika.
30 Zan kuma ba da Fir’auna Hofra, Sarkin Masar, a hannun abokan gabansa, da waɗanda suke neman ransa, kamar yadda na ba da Zadakiya, Sarkin Yahuza, a hannun Nebukadnezzar, Sarkin Babila wanda ya zama abokin gābansa, ya kuwa nemi ransa.’ ”