Jawabin Irmiya ga Baruk
1 A shekara ta huɗu ta sarautar Yehoyakim, ɗan Yosiya, Sarkin Yahuza, Baruk ɗan Neriya ya rubuta abin da Irmiya ya faɗa masa.
2 “Ubangiji Allah na Isra’ila ya ce maka, kai Baruk,
3 kai ka ce, ‘Kaitona, gama Ubangiji ya ƙara baƙin ciki a kan wahalaina, na gaji da nishina, ba ni da hutu!’
4 “Sai ka faɗa wa Baruk cewa, ‘Ni Ubangiji na ce, ga shi, abin da na gina zan rushe shi, abin da kuma na dasa zan tumɓuke shi, wato ƙasar ɗungum.
5 Kana nemar wa kanka manyan abubuwa? Kada ka neme su, gama zan kawo masifa a kan dukan ‘yan adam, amma zan kuɓutar da ranka kamar ganima, a dukan wuraren da za ka tafi.’ ”