IRM 50

Jawabin Ubangiji a kan Babila

1 Jawabin da Ubangiji ya yi wa annabi Irmiya a kan

Babila da ƙasar Kaldiyawa ke nan,

2 “Ku ba da labari ga sauran

al’umma, ku yi shela,

Ku ta da tuta, ku yi shela,

Kada ku ɓuya, amma ku ce,

‘An ci Babila da yaƙi,

An kunyatar da Bel,

An kunyatar da siffofinta,

Merodak ya rushe,

Gumakanta kuma sun ragargaje!’

3 “Wata al’umma za ta taso daga arewa gāba da ita, za ta mai da ƙasar abar ƙyama, ba wanda zai zauna ciki. Mutum da dabba duk sun watse, kowa ya bar ta.”

4 Ubangiji ya ce, “Sa’ad da lokacin nan ya yi, mutanen Isra’ila da na Yahuza za su zo tare, suna kuka, suna nemana, ni Ubangiji Allahnsu.

5 Za su tambayi hanyar Sihiyona, sa’an nan su bi ta, suna cewa, ‘Bari mu haɗa kanmu don mu yi madawwamin alkawari da Ubangiji, alkawari wanda ba za a manta da shi ba.’

6 “Mutanena sun zama kamar ɓatattun

tumaki,

Waɗanda makiyayansu suka bauɗar

da su,

Suka ɓata a cikin tsaunuka,

Suna kai da kawowa daga wannan

dutse zuwa wancan.

Sun manta da shingensu.

7 Duk waɗanda suka same su, sun

cinye su.

Maƙiyansu suka ce, ‘Ba mu yi laifi

ba,’

Gama sun yi wa Ubangiji laifi,

wanda yake tushen gaskiya,

Ubangiji wanda kakanninsu suka

dogara gare shi.

8 “Ku gudu daga cikin Babila,

Ku fita kuma daga cikin ƙasar

Kaldiyawa,

Ku zama kamar bunsurai waɗanda

suke ja gaban garke.

9 Ga shi, zan kuta manyan ƙasashe

daga arewa

Su faɗa wa Babila da yaƙi.

Za su ja dāgar yaƙi gāba da ita, su

cinye ta.

Kibansu kamar na gwanayen

mayaƙa ne

Waɗanda ba su komowa banza.

10 Za a washe Kaldiyawa,

Waɗanda suka washe su kuwa za su

ƙoshi,

Ni Ubangiji na faɗa.

11 “Saboda kuna murna, kuna farin

ciki,

Ku da kuka washe gādona,

Saboda kuma kuna tsalle kamar

karsana a cikin ciyawa,

Kuna haniniya kamar ingarmu,

12 Domin haka za a kunyatar da Babila

sosai, inda kuka fito.

Za ta zama ta baya duka a cikin

sauran al’umma,

Za ta zama hamada, busasshiyar

ƙasa.

13 Saboda fushin Ubangiji, ba wanda

zai zauna a cikinta,

Za ta zama kufai,

Duk wanda ya bi ta wajen Babila, zai

ji tsoro,

Zai kuma yi tsaki saboda

lalacewarta.

14 “Dukanku ‘yan baka, ku ja dāga, ku

kewaye Babila,

Ku harbe ta, kada ku rage kibanku,

Gama ta yi wa Ubangiji zunubi.

15 Ku kewaye ta da kuwwar yaƙi!

Ta ba da gari,

Ginshiƙanta sun fāɗi.

An rushe garunta,

Gama wannan sakayya ce ta

Ubangiji.

Ku sāka mata, ku yi mata kamar

yadda ta yi.

16 Ku datse wa Babila mai shuka,

Da mai yanka da lauje a lokacin

girbi.

Saboda takobin azzalumi,

Kowa zai koma wurin mutanensa,

Kowa kuma zai gudu zuwa

ƙasarsa.”

17 “Isra’ilawa kamar tumaki ne waɗanda zakuna suka bi su suna kora. Da farko dai Sarkin Assuriya ne ya cinye su. Yanzu kuwa Sarkin Babila, wato Nebukadnezzar, shi ne yake gaigayi ƙasusuwansu.

18 Saboda haka ni Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra’ila na ce, zan yi wa Sarkin Babila da ƙasarsa hukunci, kamar yadda na hukunta Sarkin Assuriya.

19 Zan komar da Isra’ila a makiyayarsa, zai yi kiwo a Karmel da Bashan. Zai sami biyan bukatarsa a tsaunukan Ifraimu da na Gileyad.

20 Ni Ubangiji na ce sa’ad da lokacin nan ya yi za a nemi laifi da zunubi a cikin Isra’ila da Yahuza, amma ba za a samu ba, gama zan gafarta wa sauran da suka ragu.

21 “Ku haura ku fāɗa wa ƙasar

Meratayim da mazaunan Fekod.

Ku kashe, ku hallaka su sarai,

Ku aikata dukan abin da na umarce

ku,

Ni Ubangiji na faɗa.

22 Hargowar yaƙi tana cikin ƙasar,

Da kuma babbar hallakarwa!

23 Ga yadda aka karya gudumar dukan

duniya!

Ga yadda Babila ta zama abar

ƙyama ga sauran al’umma!

24 Na kafa miki tarko, ya kuwa kama

ki, ya Babila,

Ke kuwa ba ki sani ba.

An same ki, an kama,

Domin kin yi gāba da ni.”

25 Ubangiji ya buɗe taskar

makamansa,

Ya fito da makaman hasalarsa,

Gama Ubangiji Allah Mai Runduna

yana da aikin da zai yi a ƙasar

Kaldiyawa.

26 Ku zo, ku fāɗa mata daga kowane

sashi.

Ku buɗe rumbunanta,

Ku tsittsiba ta kamar tsibin hatsi,

Ku hallakar da ita ɗungum,

Kada wani abu nata ya ragu.

27 Ku kashe dukan bijimanta, a kai su

mayanka!

Kaitonsu, gama kwanansu ya ƙare,

Lokacin hukuncinsu ya yi.

28 Ku ji, sun gudu sun tsere daga ƙasar

Babila,

Don su faɗa cikin Sihiyona,

Sakayyar Ubangiji Allahnmu domin

Haikalinsa.

29 “Ku kirawo ‘yan baka, dukan

waɗanda sukan ja baka, su faɗa

wa Babila.

Ku kafa sansani kewaye da ita, kada

ku bar kowa ya tsira.

Ku sāka mata bisa ga dukan

ayyukanta, gama ta raina Ubangiji

Mai Tsarki na Isra’ila.

30 Domin haka samarinta za su fāɗi a

tituna.

Za a hallaka sojojinta duka a wannan

rana,

Ni Ubangiji na faɗa.

31 “Ga shi, ina gāba da ke, ke Babila,

mai girmankai.

Gama ranar da zan hukunta ki, ta zo,

Ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.

32 Mai girmankai za ta yi tuntuɓe ta

fāɗi,

Ba kuwa wanda zai tashe ta,

Zan ƙone garuruwanta da wuta,

Zan kuma hallaka dukan abin da yake

kewaye da ita.

33 “Ni Ubangiji Mai Runduna na ce,

An danne mutanen Isra’ila da na

Yahuza,

Duk waɗanda suka kama su bayi sun

riƙe su da ƙarfi.

Sun ƙi su sake su.

34 Mai fansarsu mai ƙarfi ne,

Ubangiji Mai Runduna ne sunansa.

Hakika zai tsaya musu don ya kawo

wa duniya salama,

Amma zai kawo wa mazaunan Babila

fitina.

35 Ni Ubangiji na ce,

Akwai takobi a kan Kaldiyawa,

Da a kan mazaunan Babila,

Da a kan ma’aikatanta da masu

hikimarta,

36 Akwai takobi a kan masu sihiri

Don su zama wawaye.

Akwai takobi a kan jarumawanta

Don a hallaka su.

37 Akwai takobi a kan mahayan

dawakanta, da a kan karusanta,

Da a kan sojojin da ta yi ijara da su

Don su zama kamar mata,

Akwai takobi a kan dukan dukiyarta

domin a washe ta.

38 Fari zai sa ruwanta ya ƙafe,

Gama ƙasa tana cike da gumaka

waɗanda suka ɗauke hankalin

mutane.

39 “Domin haka namomin jeji da diloli

za su zauna a Babila,

Haka kuma jiminai.

Ba za a ƙara samun mazauna a

cikinta ba har dukan zamanai.

40 Abin da ya faru da Saduma da

Gwamrata,

Da biranen da suke kewaye da su,

Shi ne zai faru da Babila.

Ba mutumin da zai zauna cikinta.

41 “Ga mutane suna zuwa daga arewa,

Babbar al’umma da sarakuna

Suna tahowa daga wurare masu nisa

na duniya.

42 Suna riƙe da baka da māshi,

Mugaye ne marasa tausayi.

Amonsu yana kama da rurin teku,

Suna shirya don yin yaƙi da ke, ya

Babila.

43 Sarkin Babila ya ji labarinsu,

Hannuwansa suka yi suwu.

Wahala da azaba sun kama shi

kamar mace mai naƙuda.

44 “Ni Ubangiji ina zuwa kamar zakin da yake fitowa daga kurmin Urdun zuwa makiyaya. Nan da nan zan sa su gudu daga gare ta. Sa’an nan zan naɗa mata wanda na zaɓa. Wa yake kama da ni? Wa zai yi ƙarata? Wane shugaba zai yi gāba da ni?

45 Saboda haka ku ji shirin da Ubangiji ya yi gāba da Babila, da nufin ya yi gaba da ƙasar Kaldiyawa. Hakika za a tafi da ƙananansu, garke zai zama kango.

46 Duniya za ta girgiza sa’ad da ta ji an ci Babila da yaƙi. Za a ji kukanta cikin sauran al’umma.”