Ajalin Urushalima da Yahuza
1 “Ya ku mutanen Biliyaminu, ku
gudu neman mafaka,
Daga cikin Urushalima!
Ku busa ƙaho a Tekowa,
Ku ba da alama a Bet-akkerem,
Gama masifa da babbar halaka sun
fito daga arewa.
2 Ya Sihiyona, ke kyakkyawar
makiyaya ce, zan hallaka abin da
kika hahhaifa.
3 Makiyaya da garkunansu za su zo
wurinki,
Za su kafa alfarwansu kewaye da ke,
Kowa zai yi kiwo a makiyayarki.
4 Za su ce, ‘Mu yi shiri mu fāɗa mata
da yaƙi!
Ku tashi, mu fāɗa musu da tsakar
rana!’
Sai kuma suka ce, ‘Kaitonmu, ga
rana tana faɗuwa, ta yi ruɗa-
kuyangi.
5 Mu tashi mu fāɗa mata da dare,
Mu lalatar da fādodinta.’ ”
6 Ubangiji Mai Runduna ya ce,
“Ku sassare itatuwanta,
Ku tula ƙasa kewaye da
Urushalima,
Dole in hukunta wannan birni
saboda ba kome cikinsa sai
zalunci,
7 Kamar yadda rijiya take da ruwa
garau,
Haka Urushalima take da
muguntarta,
Ana jin labarin kama-karya da na
hallakarwa a cikinta,
Kullum akwai cuce-cuce, da raunuka
a gabana,
8 Ku ji faɗaka, ya ku mutanen
Urushalima,
Don kada a raba ni da ku,
Don kada in maishe ku kufai,
Ƙasar da ba mazauna ciki.”
9 Ubangiji Mai Runduna ya ce,
“Za a kalace ringin Isra’ila sarai,
kamar yadda ake wa inabi,
Ka miƙa hannunka a kan rassanta
kamar mai tsinkar ‘ya’yan
inabi.”
10 Da wa zan yi magana don in faɗakar
da shi, don su ji?
Ga shi, kunnuwansu a toshe suke, su
ji,
Ga shi, maganar Ubangiji kuwa ta
zama abin ba’a a gare su,
Ba su marmarinta.
11-12 Don haka ina cike da fushin
Ubangiji
Na gaji da kannewa.
Ubangiji ya ce,
“Zan kwararo fushi kan yara da suke a
titi.
Da kuma kan tattaruwar samari.
Za a ɗauke mata da miji duka biyu,
Da tsofaffi, da waɗanda suka tsufa
tukub-tukub.
Za a ba waɗansu gidajensu, da
gonakinsu, da matansu,
Gama zan nuna ikona in hukunta
mazaunan ƙasar.
13 Gama daga ƙaraminsu zuwa babba,
Kowannensu yana haɗama ya ci
ƙazamar riba,
Har annabawa da firistoci,
Kowannensu ya shiga aikata rashin
gaskiya.
14 Sun warkar da raunin mutanena
sama sama,
Suna cewa, ‘Lafiya, Lafiya,’ alhali
kuwa ba lafiya.
15 Sun ji kunya sa’ad da suka aikata
abubuwan banƙyama?
Ba su ji kunya ba ko kaɗan.
Ko gezau ba su yi ba,
Don haka za su fāɗi tare da
fāɗaɗɗu,
Sa’ad da na hukunta su, za a
hamɓarar da su.
Ni Ubangiji na faɗa.”
16 Haka Ubangiji ya ce,
“Ku tsaya kan hanyoyi, ku duba,
Ku nemi hanyoyin dā, inda hanya
mai kyau take,
Ku bi ta, don ku hutar da
rayukanku.
Amma suka ce, ‘Ai, ba za mu bi ta ba.’
17 Na sa muku matsara cewa, in kun ji
an busa ƙaho ku kula!
Amma suka ce, ‘Ba za mu kula ba.’
18 “Don haka, ku ji, ya ku al’ummai,
Ku sani, ku taron jama’a,
Don ku san abin da zai same ku.
19 Ki ji, ya ke duniya,
Ga shi, ina kawo masifa a kan
wannan jama’a,
Sakayyar ƙulle-ƙullensu,
Don ba su kula da maganata ba,
Sun ƙi dokokina.
20 Da wane nufi kuke kawo mini turare
daga Sheba,
Ko raken da kuke kawowa daga
ƙasa mai nisa?
Ba zan karɓi hadayunku na ƙonawa
ba,
Ba kuwa zan ji daɗin sadakokinku
ba.
21 Don haka, ni Ubangiji na ce,
Zan sa abin tuntuɓe a gaban wannan
jama’a,
Za su kuwa yi tuntuɓe, su fāɗi.
Iyaye tare da ‘ya’yansu, da
maƙwabci,
Do abokansu za su lalace.”
22 Haka Ubangiji ya ce,
“Ga shi, jama’a tana fitowa daga
ƙasar arewa.
Babbar al’umma ce,
Ta yunƙuro tun daga manisantan
wurare na duniya.
23 Suna riƙe da baka da māshi,
Mugaye ne marasa tausayi,
Motsinsu kamar ƙugin teku ne.
Suna haye a kan dawakai,
A jere kamar wanda ya yi shirin
yaƙi
Gāba da ke, ya ‘yar Sihiyona.”
24 Mutanen Urushalima sun ce,
“Mun ji labarin yaƙin,
Hannuwanmu suka yi rauni.
Azaba ta kama mu,
Ciwo irin na mai naƙuda.
25 Kada ku fita zuwa gona,
Kada kuma ku yi yawo a kan
hanya,
Gama abokin gāba yana da takobi,
Razana a kowane sashi.”
26 “Ya mutanena, ku sa tufafin makoki,
Ku yi birgima cikin toka,
Ku yi makoki mai zafi irin wanda
akan yi wa ɗa tilo,
Gama mai hallakarwa zai auko mana
nan da nan.”
27 Ubangiji ya ce wa Irmiya,
“Na maishe ka mai aunawa da mai
jarraba mutanena
Domin ka sani, ka auna
al’amuransu,
28 Su duka masu taurinkai ne, ‘yan
tawaye,
Suna yawo suna baza jita-jita.
Su tagulla ne da baƙin ƙarfe,
Dukansu lalatattu ne.
29 Ana zuga da ƙarfi,
Dalma ta ƙone,
Tacewar aikin banza ne,
Gama ba a fitar da mugaye ba.
30 Ana ce da su ƙwan maƙerar azurfa
ne,
Gama ni na ƙi su.”