Ku Gyara Hanyoyinku da Ayyukanku
1 Ubangiji ya yi magana da Irmiya ya ce,
2 “Ka tafi ka tsaya a ƙofar Haikalin Ubangiji, ka yi shelar wannan magana, ka ce, su kasa kunne ga maganar Ubangiji, dukansu mutanen Yahuza, su da suke shiga ta ƙofofin nan don su yi wa Ubangiji sujada!
3 Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra’ila ya ce, ‘Ku gyara hanyoyinku da ayyukanku, ni kuwa zan ƙyale ku, ku zauna a wannan wuri.
4 Kada ku amince da maganganun nan na ruɗarwa, cewa wannan shi ne Haikalin Ubangiji. Wannan shi ne Haikalin Ubangiji, wannan shi ne Haikalin Ubangiji!
5 “ ‘Idan dai kun gyara hanyoyinku, da ayyukanku bisa kan gaskiya, idan da gaskiya kuke aikata adalci ga junanku,
6 idan ba ku tsananta wa baƙo, ko maraya, ko gwauruwa, wato matar da mijinta ya rasu, idan ba ku zubar da jinin marar laifi a wannan wuri ba, idan kuma ba ku bi abin da zai cuce ku ba, wato gumaka,
7 sa’an nan zan bar ku ku zauna a wannan wuri, a ƙasa wadda tuni na ba kakanninku har abada.
8 “ ‘Ga shi, kun amince da maganganu na ruɗami, marasa amfani.
9 Za ku yi ta yin sata, da kisankai, da zina, da rantsuwar ƙarya, da ƙona wa Ba’al turare, da bin waɗansu gumakan da ba ku sani ba?
10 Sa’an nan za ku zo ku tsaya a gabana a wannan Haikali, wanda ake kira da sunana, ku ce, “An cece mu,” don kawai ku ci gaba da yin dukan waɗannan abubuwan banƙyama?
11 Wannan Haikali wanda ake kira da sunana ya zama kogon mafasa a idanunku. Ga shi, ni da kaina na gani.’ ” in ji Ubangiji.
12 “ ‘Ku tafi Shilo wurin da na fara zaunar da sunana, ku ga abin da na yi mata saboda muguntar mutanena Isra’ila.
13 Yanzu kuwa saboda kun aikata waɗannan al’amura, sa’ad da na yi ta yi muku magana, amma ba ku kasa kunne ba, sa’ad da na kira ku, ba ku amsa ba,
14 domin haka zan yi wa Haikali wanda ake kira da sunana, wanda kuma kuka amince da shi, da kuma wurin da na ba ku, ku da kakanninku, kamar yadda na yi wa Shilo.
15 Zan kore ku daga gabana kamar yadda na yi wa dukan ‘yan’uwanku, dukan zuriyar Ifraimu.’ ”
Fushin Allah a kan Bin Gumaka
16 “Kai kuwa, Irmiya kada ka yi wa mutanen nan addu’a. Kada ka yi kuka ko addu’a dominsu, kada ka roƙe ni, gama ba zan ji ka ba.
17 Ba ka ga abin da suke yi a biranen Yahuza da titunan Urushalima ba?
18 Yara sukan tara itace, iyaye maza sukan haɗa wuta, iyaye mata sukan kwaɓa ƙullu don su yi wa gunkin nan wadda ake kira sarauniyar sama, waina. Sukan kuma miƙa wa gumaka hadayu na sha domin su tsokane ni.”
19 In ji Ubangiji, “Ni suke tsokana? Ashe, ba kansu ba ne don su ruɗar da kansu?”
20 Saboda haka ga abin da Ubangiji Allah ya ce, “Duba, zan kwarara fushina da hasalata a kan wannan wuri, a kan mutum duk da dabba, da akan itatuwan saura da amfanin gona. Zai yi ta cin wuta, ba kuwa za a kashe ba.”
Horon Yahuza saboda Tayarwa
21 Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra’ila, ya ce, “Ku ba da hadayunku na ƙonawa da na sadakarku, ku ci naman.
22 A ranar da na fito da kakanninku daga ƙasar Masar, ban yi magana da su, ko na umarce su, a kan hadayun ƙonawa da na sadaka ba.
23 Amma na umarce su su yi biyayya da maganata, zan zama Allahnsu, su kuma za su zama mutanena, su bi dukan al’amuran da na umarce su, domin lafiyarsu, don su zama lafiya.
24 Amma ba su yi biyayya ba, ba su kuma kula ba. Sai suka bi shawarar kansu da ta tattaurar muguwar zuciyarsu. Suka koma baya maimakon su yi gaba.
25 Tun daga ran da kakanninku suka fito ƙasar Masar, har zuwa yau na yi ta aika musu da dukan bayina annabawa kowace rana.
26 Duk da haka ba su saurare ni ba, ba su kula su ji ba, sai suka taurare zukatansu suka aikata mugun abu fiye da na kakanninsu.
27 “Saboda haka za ka faɗa musu waɗannan abubuwa duka, amma ba za su ji ka ba. Za ka kira su, amma ba za su amsa ba.
28 Za ka faɗa musu ka ce, wannan ita ce al’ummar da ba ta yi biyayya da maganar Ubangiji Allahnta ba, ba ta karɓi horo ba. Gaskiya kuma ta ƙare sam, ba ta a bakinsu.
29 “Ku aske gashin kanku, ku zubar da shi. Ku yi makoki a filayen tuddai, gama Ubangiji ya ƙi ‘yan zamanin nan, ya rabu da su saboda fushinsa.
30 Ni Ubangiji, na faɗa, cewa mutanen Yahuza sun yi mugun abu a gabana. Suna ajiye gumakansu a Haikalina, sun ƙazantar da shi.
31 A cikin kwarin ɗan Hinnon sun gina bagade, mai suna Tofet, don su miƙa ‘ya’yansu mata da maza hadayar ƙonawa. Ni ban umarce su su yi haka ba, irin wannan abu ba shi a zuciyata.
32 Domin haka, ni Ubangiji na ce, kwanaki suna zuwa lokacin da ba za a ƙara faɗar Tofet, ko kwarin ɗan Hinnom ba, amma za a kira shi Kwarin Kisa, gama za a binne mutane a Tofet domin ba sauran wuri a ko’ina.
33 Gawawwakin mutanen nan za su zama abincin tsuntsaye da na namomin jeji, ba wanda zai kore su.
34 Zan sa muryar murna da ta farin ciki, da muryar ango da ta amarya su ƙare a biranen Yahuza da titunan Urushalima, gama ƙasar za ta zama kufai.”