1 “Ni Ubangiji na faɗa, cewa a wancan lokaci, za a fitar da ƙasusuwa daga kaburburan sarakunan Yahuza, da na sarakansu, da na firistoci, da na annabawa, da na mazaunan Urushalima.
2 Za a shimfiɗa su a rana, da a farin wata, da a gaban dukan rundunan sama, waɗanda suka ƙaunata, suka bauta wa, waɗanda suka nemi shawararsu, suka yi musu sujada. Ba za a tattara su a binne ba, amma za su zama juji a bisa ƙasa.
3 Sauran mutanen muguwar tsaran nan waɗanda suke a wuraren da na warwatsa su, za su fi son mutuwa fiye da rayuwa. Ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.”
Zunubi da Hukunci
4 “Ka faɗa musu, ka ce, ni Ubangiji na
ce,
‘Wanda ya fāɗi ba zai sāke tashi ba?
Idan wani ya kauce ba zai komo kan
hanya ba?
5 Me ya sa, mutanen nan na
Urushalima suke ratsewa, suke
komawa baya kullayaumin?
Sun riƙe ƙarya kan-kan
Sun ƙi komowa.
6 Na kula sosai, na saurara,
Amma ba wanda ya faɗi wata
maganar kirki,
Ba wanda ya taɓa barin muguntarsa,
Kowa cewa yake, “Me na yi?”
Kamar dokin da ya kutsa kai cikin
fagen fama.
7 Ko shamuwa ta sararin sama ma, ta
san lokatanta,
Tattabara da tsattsewa, da gauraka
suna kiyaye lokacin komowarsu.
Amma mutanena ba su san dokokina
ba.
8 Ƙaƙa za ku ce, “Muna da hikima,
Dokar Ubangiji tana tare da mu”?
Ga shi kuwa, alkalamin ƙarya na
magatakarda, ya yi ƙarya.
9 Za a kunyatar da masu hikima.
Za su tsorata, za a kuma tafi da su.
Ga shi, sun ƙi maganar Ubangiji.
Wace hikima suke da ita?
10 Saboda haka zan ba da matansu ga
waɗansu,
Gonakinsu kuma ga waɗanda suke
cinsu da yaƙi,
Saboda tun daga ƙarami har zuwa
babba
Kowannensu yana haɗamar cin
muguwar riba,
Tun daga annabawa zuwa firistoci
Kowannensu aikata ha’inci yake yi.
11 Sun warkar da raunin mutanena
sama sama,
Suna cewa, “Lafiya, lafiya,” alhali
kuwa ba lafiya.
12 Ko sun ji kunya
Sa’ad da suka aikata ayyuka masu
banƙyama?
A’a, ba su ji kunya ba ko kaɗan,
Fuskarsu ko gezau ba ta yi ba.
Domin haka za su faɗi tare da
fāɗaɗɗu,
Sa’ad da na hukunta su, za a ci su da
yaƙi.
Ni Ubangiji na faɗa.’
13 “Ni Ubangiji na ce,
‘Sa’ad da zan tattara su kamar
amfanin gona,
Sai na tarar ba ‘ya’ya a kurangar
inabi,
Ba ‘ya’ya kuma a itacen ɓaure,
Har ganyayen ma sun bushe.
Abin da na ba su kuma ya kuɓuce
musu.
Ni Ubangiji na faɗa.’ ”
14 Mutanen Urushalima sun ce,
“Don me muke zaune kawai?
Bari mu tattaru, mu tafi cikin
garuruwa masu garu,
Mu mutu a can,
Gama Ubangiji Allahnmu ya
ƙaddara mana mutuwa,
Ya ba mu ruwan dafi,
Domin mun yi masa laifi.
15 Mun sa zuciya ga salama, amma ba
lafiya,
Mun sa zuciya ga lokacin samun
warkewa,
Amma sai ga razana!
16 Daga Dan, an ji firjin dawakai.
Dakan ƙasar ta girgiza saboda
haniniyar ingarmunsu.
Sun zo su cinye ƙasar duk da abin
da suke cikinta,
Wato da birnin da mazauna
cikinsa.”
17 “Ni Ubangiji na ce, ‘Zan aiko muku
da macizai, da kāsā,
Waɗanda ba su da makari,
Za su sassare ku.’ ”
18 Baƙin cikina ya fi ƙarfin warkewa,
Zuciyata ta ɓaci ƙwarai!
19 Ku ji kukan jama’ata ko’ina a
ƙasar,
“Ubangiji, ba shi a Sihiyona
ne?
Sarkinta ba ya a cikinta ne?”
Ubangiji ya ce,
“Me ya sa suka tsokane ni da
sassaƙaƙƙun gumakansu,
Da baƙin gumakansu?”
20 Mutane suna ta cewa,
“Damuna ta ƙare, kaka kuma ta
wuce,
Amma ba a cece mu ba.”
21 Raunin da aka yi wa jama’ata,
Ya yi wa zuciyata rauni.
Ina makoki, tsoro kuma ya kama ni
ƙwarai.
22 Ba abin sanyayawa a Gileyad ne?
Ba mai magani a can ne?
Me ya sa ba a warkar da jama’ata
ba?