1 Da ma kaina ruwa ne kundum,
Idanuna kuma maɓuɓɓuga ne,
Da sai in yi ta kuka dare da rana,
Saboda an kashe jama’ata!
2 Da ma ina da wurin da zan fake a
hamada,
Da sai in rabu da mutanena, in tafi
can!
Gama dukansu mazinata ne,
Ƙungiyar mutane maciya amana.
3 Ubangiji ya ce,
“Sun tanƙwasa harshensu kamar
baka,
Ƙarya ce take rinjayar gaskiya a
ƙasar.
Suna ta cin gaba da aikata mugunta,
Ba su kuwa san ni ba.
4 “Bari kowane mutum ya yi hankali
da maƙwabcinsa,
Kada kuma ya amince da kowane
irin ɗan’uwa,
Gama kowane ɗan’uwa munafuki
ne,
Kowane maƙwabci kuma mai kushe
ne.
5 Kowane mutum yana ruɗin
maƙwabcinsa da abokinsa,
Ba mai faɗar gaskiya,
Sun koya wa harshensu faɗar
ƙarya.
Suna aikata laifi,
Sun rafke, sun kasa tuba.
6 Suna ƙara zalunci a kan zalunci,
Yaudara a kan yaudara,
Sun ƙi sanina,” in ji Ubangiji.
7 Saboda haka, Ubangiji Mai
Runduna, ya faɗa cewa,
“Zan tsabtace su, in gwada su,
Gama me zan yi kuma saboda
jama’ata?
8 Harshensu kibiya ce mai dafi, yana
faɗar ƙarya,
Kowa yana maganar alheri da
maƙwabcinsa
Amma a zuciyarsa yana shirya masa
maƙarƙashiya.
9 Ba zan hukunta su saboda waɗannan
al’amura ba?
Ba zan sāka wa al’umma irin
wannan ba?”
10 Zan yi kuka in yi kururuwa saboda
tsaunuka,
Zan yi kuka saboda wuraren kiwo,
Domin sun bushe sun zama marasa
amfani.
Ba wanda yake bi ta cikinsu.
Ba a kuma jin kukan shanu,
Tsuntsaye da namomin jeji, sun gudu
sun tafi.
11 “Ni Ubangiji na ce, zan mai da
Urushalima tsibin kufai,
Wurin zaman diloli,
Zan kuma mai da biranen Yahuza
kufai, inda ba kowa.”
Za a Rushe Birni a Kai su Zaman Talala
12 Wa yake da isasshiyar hikimar da zai fahimci wannan? Wa Ubangiji ya faɗa masa don ya sanar? Me ya sa ƙasar ta lalace ta zama kufai, har ba wanda yake iya ratsa ta, kamar hamada?
13 Sai Ubangiji ya ce, “Saboda sun bar dokata wadda na sa a gabansu, ba su yi biyayya da maganata ko su yi aiki da ita ba.
14 Amma suka taurare, suka biye wa zuciyarsu, suka bi Ba’al, kamar yadda kakanninsu suka koya musu.
15 Domin haka, ni Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra’ila, zan ciyar da mutanen nan da abinci mai ɗaci, in shayar da su da ruwan dafi.
16 Zan watsa su cikin sauran al’umma waɗanda su da kakanninsu ba su san su ba, zan sa takobi ya bi su don in hallaka su.
17 “Haka ni Ubangiji Mai Runduna na
ce,
Ku yi tunani, ku kirawo mata masu
makoki su zo,
Ku aika wa gwanaye fa.”
18 Jama’a suka ce,
“Su gaggauta, su ta da murya,
Su yi mana kuka da ƙarfi,
Har idanunmu su cika da hawaye,
Giranmu kuma su jiƙe sharaf.
19 “Gama ana jin muryar kuka daga
Sihiyona cewa,
‘Ga yadda muka lalace! Aka kunyatar
da mu ɗungum!
Don mun bar ƙasar, domin sun
rurrushe wuraren zamanmu.’ ”
20 Irmiya ya ce,
“Ya ku mata, ku ji maganar
Ubangiji,
Ku kasa kunne ga maganar da ya
faɗa,
Ku koya wa ‘ya’yanku mata kukan
makoki,
Kowacce ta koya wa maƙwabciyarta
waƙar makoki,
21 Gama mutuwa ta shiga tagoginmu,
Ta shiga cikin fādodinmu,
Ta karkashe yara a tituna,
Ta kuma karkashe samari a dandali.
22 Ubangiji ya ce mini,
‘Ka yi magana, cewa gawawwakin
mutane za su fāɗi tuli
Kamar juji a saura,
Kamar dammunan da masu girbi
suka ɗaura,
Ba wanda zai tattara su.’ ”
23 Ubangiji ya ce, “Kada mai hikima ya yi fariya da hikimarsa, kada mai ƙarfi ya yi fariya da ƙarfinsa, kada kuma mawadaci ya yi fariya da wadatarsa.
24 Amma bari wanda zai yi fariya, ya yi fariya a kan cewa ya fahimce ni, ya kuma san ni. Ni ne Ubangiji mai yin alheri, da gaskiya, da adalci a duniya, gama ina murna da waɗannan abubuwa, ni Ubangiji na faɗa.”
25 Ubangiji ya ce, “Kwanaki suna zuwa sa’ad da zan hukunta dukan waɗanda aka yi musu kaciya,
26 da Masar, da Yahuza, da Edom, da ‘ya’yan Ammon, maza, da na Mowab, da dukan waɗanda suke zaune a hamada, da waɗanda suke yi wa kansu sanƙo, gama dukan al’umman nan marasa kaciya ne, dukan jama’ar Isra’ila kuma marasa kaciya ne a zuci.”