1 Abin da yake rubuce a littafin nan, jawabi ne a kan Yahuza da Urushalima, wanda Allah ya bayyana wa Ishaya ɗan Amoz a zamanin da Azariya, da Yotam, da Ahaz, da Hezekiya, suka yi sarautar Yahuza.
Allah Ya Tsauta wa Al’umma Mai Zunubi
2 Ubangiji ya ce, “Duniya da sararin sama, ku kasa kunne ga abin da ni, Ubangiji, nake cewa! ‘Ya’yan da na goya sun tayar mini.
3 Shanu sun san ubangijinsu, jakai sun san wurin da ubangijinsu yake ba su abinci. Amma wannan ya fi abin da jama’ata Isra’ila suka sani. Ba su gane ba ko kaɗan.”
4 An hallaka ki, ke al’umma mai zunubi, ku lalatattun mutane! Zunubinku ya ja ku ƙasa! Kun ƙi Ubangiji, Allah Mai Tsarki na Isra’ila, kun juya masa baya.
5 Me ya sa kuke ta tayarwa? Kuna so a ƙara muku hukunci ne? Ya Isra’ila, kanki duka rauni ne, zuciyarki da kwanyarki suna ciwo.
6 Daga kanki har zuwa ƙafafunki, ba inda yake da lafiya a jikinki. Raunuka da ƙujewa da manyan gyambuna sun rufe jikinki, ba a tsabtace raunukanki an ɗaure ba. Ba a yi musu magani ba.
7 An lalatar da ƙasarku, an ƙone biranenku ƙurmus. Kuna gani, baƙi suka ƙwace ƙasarku, suka mai da ko’ina kufai.
8 Urushalima kaɗai ta ragu, birnin da aka kewaye da yaƙi, ba wata kariya kamar rumfar mai ƙumu a gonar inabi, ko ta mai ƙumu a gonar kankana.
9 Da a ce Ubangiji Mai Runduna bai rage sauran jama’a ba, da an hallakar da Urushalima gaba ɗaya, kamar yadda aka yi wa Saduma da Gwamrata.
An Kira Su Tuba
10 Ya Urushalima sarakunanki da jama’arki sun zama kamar Saduma da Gwamrata. Ku kasa kunne ga abin da Ubangiji yake faɗa muku. Ku mai da hankali ga abin da Allahnmu yake koya muku.
11 Ya ce, “Kuna tsammani ina jin daɗin dukan hadayun nan da kuke ta miƙa mini? Tumakin da kuke miƙawa hadaya ta ƙonawa, da kitsen kyawawan dabbobinku ya ishe ni. Na gaji da jinin bijimai, da na tumaki, da na awaki.
12 Wa ya roƙe ku ku kawo mini dukan wannan sa’ad da kuka zo yi mini sujada? Wa kuma ya roƙe ku ku yi ta kai da kawowa a kewaye da Haikalina?
13 Ko kusa ba na bukatar hadayunku marasa amfani. Ina jin ƙyamar ƙanshin turaren da kuke miƙawa. Ba zan jure da bukukuwanku na amaryar wata, da na ranakun Asabar, da taronku na addini ba, duka sun ɓaci saboda zunubanku.
14 Ina ƙin bukukuwanku na amaryar wata, da na tsarkakan ranaku. Sun zama nawaya wadda na gaji da ita.
15 “Sa’ad da kuke ɗaga hannuwanku wajen yin addu’a, ba zan dube ku ba. Kome yawan addu’ar da kuka yi, ba zan kasa kunne ba domin zunubi ya ɓata hannuwanku.
16 Ku yi wanka sarai. Ku daina aikata dukan wannan mugun abu da na ga kuna aikatawa. I, ku daina aikata mugunta.
17 Ku koyi yin abin da yake daidai. Ku ga an aikata adalci, ku taimaki waɗanda ake zalunta, ku ba marayu hakkinsu, ku kāre gwauraye, wato matan da mazansu suka mutu.”
18 Ubangiji ya ce, “Yanzu fa, bari mu daidaita al’amarinmu. Duk kun yi ja wur da zunubi, amma zan wanke ku, ku yi fari fat kamar auduga. Zai yiwu zunubinku ya sa ku zama ja wur, amma za ku yi fari fat kamar farin ulu.
19 Idan za ku yi mini biyayya kaɗai za ku ci kyawawan abubuwan da ƙasa take bayarwa.
20 Amma idan kuka ƙi, kuka raina ni, mutuwa ce ƙaddararku. Ni Ubangiji na faɗi wannan.”
Hukuncin Urushalima da Tubanta
21 Birnin da yake dā mai aminci ne, yanzu ya zama kamar karuwa! Dā adalai a can suke zaune, amma yanzu sai masu kisankai kaɗai.
22 Ya Urushalima, dā kamar azurfa kike, amma yanzu ba ki da amfani, dā kamar kyakkyawan ruwan inabi kike, amma yanzu baƙin ruwa ne kaɗai.
23 Shugabanninku ‘yan tawaye ne, abokan ɓarayi, a koyaushe sai karɓar kyautai suke yi, da rashawa. Amma ba su taɓa kare marayu a ɗakin shari’a, ko su kasa kunne ga ƙarar da gwauraye suka kawo ba, wato matan da mazansu suka mutu.
24 Domin haka fa yanzu, sai ku kasa kunne ga abin da Ubangiji Mai Runduna, Allah mai iko na Isra’ila, yake cewa, “Zan ɗauki fansa a kanku ku maƙiyana, ba za ku ƙara wahalshe ni ba.
25 Zan hukunta ku. Zan tace ku kamar yadda ake tace ƙarfe, in kawar da dukan ƙazantarku.
26 Zan ba ku shugabanni da mashawarta kamar waɗanda kuke da su dā can. Sa’an nan za a ce da Urushalima adala, amintaccen birni.”
27 Gama Ubangiji mai adalci ne, zai ceci Urushalima da dukan wanda ya tuba a can.
28 Amma zai ragargaza dukan wanda ya yi zunubi, ya tayar gāba da shi, zai kashe duk wanda ya rabu da shi.
29 Za ku yi da na sani, ku da kuka taɓa yin sujada ga itatuwa da dashe-dashen masujada.
30 Za ku bushe kamar busasshen itacen oak, kamar lambun da ba wanda yake ba shi ruwa.
31 Daidai kamar yadda busasshen itacen da tartsatsin wuta ya fāɗa wa, haka mutane masu iko za su hallaka ta wurin mugayen ayyukansu, ba wanda zai iya hana a hallaka su.