Assuriya Za Ta Ci Masar da Habasha
1 Bisa ga umarnin Sargon, Sarkin Assuriya, sai sarkin yaƙin Assuriya ya fāɗa wa Ashdod, birnin Filistiyawa, da yaƙi.
2 A wannan lokaci Ubangiji ya riga ya faɗa wa Ishaya ɗan Amoz, cewa ya tuɓe tsummokin da yake saye da su, ya kuma tuɓe takalmansa. Shi kuwa ya yi biyayya ya yi ta yawo tsirara, ba kuma takalmi a ƙafarsa.
3 Sa’ad da aka ci Ashdod, sai Ubangiji ya ce, “Bawana Ishaya ya yi ta yawo tsira, ba kuma takalmi a ƙafarsa har shekara uku. Wannan ita ce alamar abin da zai faru a ƙasa Masar da Habasha.
4 Sarkin Assuriya zai kwashe kamammun yaƙi waɗanda ya kama a ƙasashen nan biyu, ya tafi da su tsirara. Matasa da manya kuma ba takalmi a ƙafafunsu, asirinsu a tsiraice, don a kunyata Masar.
5 Waɗanda suke dogara ga Habasha, suna kuwa fāriya da Masar, za su ruɗe, sa zuciyarsu zai wargaje.
6 A wannan rana mutanen da suke zaune a gaɓar Filistiyawa za su ce, ‘Dubi abin da ya faru ga jama’ar da muka dogara da su don su tsare mu daga Sarkin Assuriya! Ƙaƙa za mu yi mu tsira?’ ”